shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 11 August 2015

sireenah*********2**9

samp906c78071de1d454.jpg

Sireenah 2*9



********NA**********


muhd-Abba~Gana



www.abbagana.pun.bz


Suhail yasauka family house dinsu dake london
wanda nan ne muneerah take zama babban
gidane sosai. Koda Ya'isa garin bai tararda
muneerah a gida, don haka batasan da zuwansa.
Bayan yayi wankansa yaci abinci koda yaduba
agogo yaga dasauran lokaci before the meeting
yakwanta bacci cikin barcin yayi mafarkin sunyi
aure da sahibarsa with four kids suna shaqatawa.
Alarm dinda yayi setting shine yakatse masa da
daddan baccinsa. Baiso tashi ba but bayada
option dolensa yatashi saboda muhimmancin
meeting din so yasoma shiri cikin gaggawa, gama
shirinsa yayi daidai da isowar motar muneerah a
harabar gidan. Shigar suit yayi komai nasa farine
harda briefcase dinsa lifter yayi using wurin
saukowa while muneerah da steps tayi amfani so
basu samu damar haduwa. Madam you are highly
welcome, your brother just left, yar aikin gidansu
ce mai suna Linda take sanarwa muneerah fitar
yayanta, Linda which of my brother? Mr
handsome sunanda yan aikin gidan ke Kiran
suhail dashi. Okay koda ta'isa dakinta tagansa
tacikin securities camera so tayi farin ciki sosai
don haka tashiga hada masa favourite food dinsa
da juice tabata lokaci sosai wurin hada masa
girki Linda ce ta shirya abincin saman dinning
dake babban falo, muneerah taje tayi wanka
simple make-up tasa doguwar riga marar nauyi
kalar sky blue tana jiran yayanta, daman tanadaf
burri akansa sai gashi yazo mata cikin sauki don
haka baza tayi sakaci wurin gaya masa kada
lokaci yakure mata. Masu karatu menene wannan
burrin na muneerah?...........
**************
Salau har ka'iso? Eh hajia ina kwana, lafia lau
salau. Ke sireenah kina ina ga mijinki nan yazo
daukarki, ganinan Mommy tee, sireenah bata zata
an bada ita sadaqa dagaske sai da taga salau
yazo daukar ta gashi bata shirya komai koda take
bawani tufafin arziki ke gareta don haka school
bag dinta kadai tadauka, salau haushi yacika shi
daya ganta hannu sake yazata tunda sunce auren
sadaqa za'a hadota kayan gara, lefe etc but sai
yaga wayam, watakila kudine cikin jakarta haka
Malam salau yake tunanin haka. Shi yahana
yanuna bacin ransa a fili. Drivern mommy tee ne
yatuka su zuwa kasan layin ta wurin da shagon
salau yake Ado nasauke su yawuce abinshi. Ke
shiga ciki nan ne gidanah amma muga jikkarki
meye aciki bamusu ta mika masa yana budewa
yatarar da littafai nan yayi watsi dasu yana fadan
littafai zasu cine da ba'a kawo ta da komai ba,?
Bata kulasa ba ta shiga domin takarewa inda
zata zama kallo bata ankara ba taji an rufe
shagon da karfi hankalinta yatashi sosai don tayi
kokarin fitowa takasa sanadiyar shagon an rufesa
da makulli kuma aikin salau ne tana cikin haka
tatsinkayo muryar salau koda tasaurara taji yana
waya kamar haka:- Alhaji gatanan nazo da'ita
yanzu haka tana cikin shagon da aka dauki haya
na rufeta. Kada kadamu salau su iro suna cikin
unguwar yanzu haka kadan yarage su'iso daidai
wurin. Toh Alhaji yasauran balance dina? Tareda
balance din suke. Nagode sosai Alhaji. Sireenah
ta tsoratah dajin haka hawaye yasoma fita daga
idanuwanta amma bakinta bai goshe da addua
tasan Allah kadaine zai kubutar da ita daga
sharrin salau. Tafita hannu azzaluma tafada
hannun masu sayarda mutane, yaa ubangiji
kafidda ni daga wannan bala'i tayi kokarin
guduwa ba hanya. Ba'afi minti biyar dagama
wayar sai ga su ir0, babu alamun sassauci tare
dasu fuskarnan tasu a murtuke kamar basu taba
dariya, Salau tana INA? cikin shagon take, toh ga
sauran balance dinka katabbatar ka tattara
kayanka zuwa kauyenku. Ai daman kayana a
shirye suke, yauwa salau suna bude kofar
sireenah tayi yunkurin guduwa suka wasa mata
powder a fuskarta take tasome, suka dauketa sai
cikin mota dasaurinsu suka bar unguwar. Nan
salau yarufe shagon yasani inda dare yayi masa
yana mai mamakin me ALHAJI zaiyi da wannan
mumuna yasan muddin kudi za'ayi da ita tabbas
kudin zasu yi muni. Oh su salau kenan ko
inaruwansa bayan yasayarda yar mutane.. Wane
Alhajine aka sayarwa sireenah? Mezaiyi da ita?
Sai mun hadu ana gaba........

muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive