Yadda Ake Hada Sabulu Soulp Asiyar A Samu Riba Mai Yawa
DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA
MAI JINKAI,DA SALATI GA
SHUGABAN HALITTAN ALLAH
ANNABI MUHAMMAD (SAW) DA
IYALANSA DA SAHABBANSA.
DALILIN YIN WANNAN POST DIN
Nayi wannan post dinne don
taimakon matasanmu maza da mata
game da abinda yashafi
SANA'A.Nayi tattaki zuwa wajen da
akeyin wannan aiki badan komaiba
sai don taimakawa al'ummata.
Da farko dolene ka tanaji
wadannan abubuwa....
1.Gishirin Soda
2.Alayyadi
3.Ruwa
4.Kumfa
5.Kala
6.Stati
7.Turare.
Bayan katanaji wadannan
abubuwan, kawai ka auna ruwa
kofi hudu,sai ka auna gishirin
sodannan kofi daya ka zuba
aciki,sai kabarshi ya kwana daya
idan kahadashi kamar da karfe
goma 10:00am to sai karfe 10:00Na
safiyar gobe yayi sannan ka cigaba
da hadashi
Idan ka dauko wannan ruwan daka
hadashi da gishirin soda saika auna
cikin kofi daya,sai ka auna alayyadi
cikin kofi hudu sai kasa sanda ko
muciya karinka juyawa idan kafara
juyawa ya dame to sai kuma kazuba
kumfa sai kaci gaba da juyawa sai
ka zuba kala da turare da statinnan
saika cigaba da juyawa sai ka dauko
container ka zuba idan yasha iska
zakasha mamaki da yardan Allah.
Idan kajika gishirin sodan nan
karkasa hannu dan zai konaka,Idan
kuma Allah ya aikoma ka kone
bakasaniba,kanajin zafi kawai sai
kashafa man Alayyadi a wajen da
ya kone to bazai tashiba da yardan
Allah,Idan kuma akai sakaci aka
sha to za'a fa mutu Allah yakare,mu
kuma sai mu kiyaye mu kaudashi a
inda yara bazasu ta6aba.
DA FATAN ALLAH YASA MUDACE
KUMA MU AMFANA DA ABINDA
MUKA KOYA.
Daga masana'antar muhd abba gana
gaskiya mungode daga jabir dan uwa www.jabir dan uwa
ReplyDeletenaji dadi na daina sayen sabulu kuma zan taimaki jama'a.na gode
ReplyDeleteAllah Yakara Basira
ReplyDeleteMungode allahsa nuyi aiki da abinda muka iya.
ReplyDeleteDan Allah ina tambaya, menene kala? Kuma a'ina ake samunsa shi da gishirin soda?
ReplyDeleteWanne kalar cup babba ko karami
ReplyDeleteDon Allah sabulun wanki ne ko kuwa ?
ReplyDeleteThank so much
ReplyDeletemuna godia.inada tambaya minene alayyadi
ReplyDeletemungode
ReplyDeleteTo ta kaka zan samu In saye wanan kayak hadin?
ReplyDeletezaka same su a kasuwa wajen da ake siyar da kayan chemicals nasu man shafawa
DeleteIna koyon yadda ake yin sabulu don Allah a taimaka mini
ReplyDeleteShin ka karanta gaba daya abinda mukayi jawabi akai?
DeleteMore power to ur elbow Mal Abbagana,Allah yayi albarka
ReplyDelete