shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 11 August 2015

SIRRIN KABEWA GA GYARAN JIKIN DAN ADAM

bana.jpg



Za mu dan tabo wasu daga cikin sirrukan
Kabewa. Ita dai Kabewa sinadari ce mai matukaar
muhimmanci da amfani a jikin bil Adama,
musamman ta fuskar Ibadar Aure. Masana a
wannan fagen a Duniya, sun tabbatar da a na da
nau’oi’n Kabewa guda goma sha takwas (18)
sannan A Afrika muna da guda takwas (8), bugu
da kari a nan Nijeriya muna da na’o’inta guda
hudu (4) kacal.
Kuma tana daga darajar miji a wajen matarsa
kuma abinci ce wanda idan ake sarrafata take
wanzar da abubuwa masu dumbin yawa na gyara
da inganci.
A nan ina so na yi amfani da wannan damar a
wannan jaridar tamu mai tarin farin jini in
bayyana amfanin Kabewan a takaice.
Abubuwan da za a tanada sun hada da abubuwa
hudu zan fitar da wasu sinadarai karfafa masu
kwarara da tsare mutuncin lafiya sannan su daga
kwarjininki da martabanki a wurin mijin ki. Ki
zauna abar ambato da yabo a wajen mijin ki,
kuma in kina da kishiyoyi, wato ba cuta ba
cutarwa, wanda ke ce da kan ki za ki sarrafa
babu batun ki je a ci kudinki a banza, babu gaira
ba dalili ba.
1. A markada Kabewa da Guaba da Ayaba, a tace
a dinga shan ruwan jifa-jifa, yana maganin gajiya
da saurin kosawa, sannan yana taimakawa
matuka yayin bukata ko sha’awa.
2. A cire hanzar nan ta Kabewa a zuba a ruwan
zafi, babban kofi daya a rufe, bayan hanzar ta jiku
sosai, sai a tace a zuba zuma cikin cokalin cin
abinci uku a kada har sai ya hadu shi ma a
shanye. Shi ma yana taimakawa matuka wajen
ni’ima da karin kuzari.
Hadin ‘Ya’yan Zogale
1. Ki samu farar shinkafarki, sai ki dan soyata
sama-sama, ma’ana kada ta soyu kwarai za ki
tafasa ruwa sai ki zuba gyada, ki yi sauri ki tace
ta, sai ki shanya idan kin yi daidai za ki ga
bawon gyadar yana cirewa da kansa kafin ta
bushe idan ta bushe sai ki murmushe ta ki
dakata in kin ki daka chukwi da dabino ki cire
‘ya’yan Zogale, ki cire fatar ki shanya a cikin
inuwa idan sun bushe ki hade su da dakakkiyar
soyayiyar shinkafarki da gyada da dabino, sai ki
rinka sha da madara ta ruwa, yana saukar da
ni’ima sosai.
Share:

3 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive