Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta
adakin aure, awannan zamanin da muke
ciki,ta gode ma Allah. Ba don komai ba,
idan ta
duba zata ga wasu 'yan-mata irinta, sunfi
ta kyawun halitta da iya ado, amma har
yanzu basu samu mijin aure ba.Don haka
zai fi alkhairi agareki ki Qudurce
acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI
NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI.Ki
rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da
tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku.
Kuma ki
zama ko yaushe ashirye kike domin
biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.
Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE... Ba zasu
rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin
samu miji,su kuwa basu samu ba... Dole
suyi miki hassada.Ki kiyaye sirrin mijinki,
kar ki gaya ma kowa..
Musamman ma kawayenki zasu so suji
abinda yake faruwa.. Don haka kar ki
gaya musu.Idan kuna da 'ya'ya to ki kula
dasu, ki kula da
tsaftarsu. in ma 'ya'yan kishiyarki ne, to
ki kula dasu kamar yadda zaki kula da
'ya'yanki. Ki kiyaye dukkan amanonin
mijinki.
musamman ma iyayensa da 'yan uwansa
da dukiyarsa.
Allah Ya bamu ikon kiyaye Hakkin iyalan
mu.
Slm
ReplyDeleteWslm @Aisha.aminu,
ReplyDeleteslm
ReplyDelete