shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 5 August 2015

sireenah**********--6

ni.jpg

Sireeenah 6


********by**********

muhd-Abba~Gana




Mai martaba yahya Yusuf ne zaune
da uwargidarsa/amaryarsa Hajia Amina suna
tattaunawa kan maganar rashin son auren dansu
Alhaji ni aganina tunda yaki fidda mata
mezaihana munema masa koda cikin yan uwa da
abokan arziki ne kaga ita azeemar yace kawarsa
ce a a Hajia banki taki ba but kinsan yanzu an
daina auren dole balle shi namiji ne ba ayi masa
dole duk da dan mu maibiyya ne why not muhada
masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa yadda
za a gayyaci yan uwa da abokan arziki kinga idan
shi da kansa yaga wacce yake so Alhamdullah
idan bai ganiba kinga sai na nema masa daya
daga cikin "ya "yan sarakuna a taron sarkuna din
da akeyi duk karshen shekara gaskia Alhaaji
shawarka yayi dama sauran sati daya birthday
dinsa don haka a yau zamu fara shirin. An buga
katin gayyata na mussamman suhail sunyi rabon
kati a school daga student har zuwa mallammai
haka mai martaba da uwargidarsa ba'a barsu a
baya suma sun gayyaci mutane da dama tun
daga talakawansu zuwa attajiran garin harda na
makwabta ma sun gayyata kowa yana jiran
lokacin... Mommy tee don Allah kisa ayi mana
order tufafi daga Dubai mana kinfa san ran jumua
ne birthday party yarima suhail kinga bikin na
masu arzikine dole duk abinda zamuyi amfani
dasu a gurin birthday din su kasance masu zafi
yadda kada a barmu a baya Haba yan biyuna
meku keci nabaka nazuba tufafinKu is already on
the way komai naku complete ne hatta Wayar
daza kuyi amfani dasu kudai yanzu sai kun gansu
don so nake koda daya daga cikinku ne ta auri
suhail shiyasa nake bukatar kuyi kwalliyar kece
raini Mommy Tee gaskia mungode yau ma zamu
fara zuwa ana mana gyaran jiki dasauransu.
Shiyasa nake sonku my twins ......... Oyoyo
muneera Muhammad yau kece a Nigeria kuma a
gidan mu? Sireenah bahaka bane tun tafiyana
London ban shigo 9ja ba sai this week koshima
birthday partyn din cousin dina yazo dani sannan
kema na kawo maki naki invitation card and you
must attend it insha Allah on Friday za ayi kada
ma kice mani mommy tee bazata barki ba
dakaina zanzo na dauke ki, naso muyi hirar bayan
rabuwa but am busy right now sai dai nazo OK
muneera bye... Muneera kawar sireenah ce tun a
primary up to secondary school sun san sirrin
junansu sosai duk abinda akeyiwa sireenah a gida
muneera nasane dalilin haka ne ma komai za a
sayawa muneera agidansu biyu ake saye saboda
halarci irin na uwayen muneera, sun rabu ne
lokacin da muneera tasamu addmssion a Oxford
university dake kasar London taso suje da
sireenah mommy tee ce tahana ko Nile university
din ma dakyar tabari saboda zalunci irin NATA,
tun randa muneera tabar Nigeria basu kara
haduwa ba sai yanzu datazo mata da invitation
card daman birthday partyn cousin dinta ne ya
mayar da ita. Anya kuna ganin mommy tee zata
barta taje? koma za a barta din wanne tufafi zata
saka? ************** Azeema anya kina ganin
suhail yana sonki Kuwa? haba friend yakike
magana hakane badon da ke besty nace ba da
nace kina hassada ne duk irin kulawar dayake
mani ai ya isa kisan yana sona jira kawai nake
mugama karatu nasanar da daddy batun aurena
da suhail, Azeema kalli can ga mutuniyarki nan
tafe black monkey (sireenah) Friend kin san Allah
bana kaunar ganinta sanadiyar suhail nake
wannan school da tuni nabar school din kanta
haba azeemda mai yayi zafi haka Allah ni
tausayinta nakeji, yayi uwar tausayi yi mana shiru
gata nan ta iso gab damu ... Ke black monkey
albishirinki nasamo maki aiki gidansu suhail dina
a partyn daza a gudanar ranar Friday a
matsayinki na mai serving din mutanen dazasu
halarci taron don naga kina bukatar taimako.
Hmm nagode amma bakiga nayi maki kama da
wacce take neman taimako ba kije kinemi
mabukata sanadiyar wannan furucin da sireenah
tayi azeema tadau hannunta ta wanke sireenah
da mari Lallai black monkey har kinyi bakin
dazanyi Magana kirama wannan Marin kadan
daga cikin matakin da zan dauka..... azeema bata
gama rufe baki ba taji saukar mari a kuncinta duk
sun razana sosai bama kamar azeema wacce aka
mara wadda duk tafisu razanar tunda take dunia
ba a taba marinta ba sai yau bakowa bane
yamareta face suhail ashe yana ganin duk abinda
ke faruwa daman yana sane dacin kashin datake
wa talakawa more especially sireenah Wanda
agaban idonsa takeyi mata wasu cin mutunci
yasha hanata tadaina wulakanta mutane bata
bari shine yau dai yadau mataki don yagaji da
hali irin NATA ... zan cigabaa insha Allah


muhd-Abba~Gana


More @
www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive