shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 7 August 2015

sireenah**********---11

samp906c78071de1d454.jpg

Sireenaah 11


********by**********

muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz


! Munafukar tsiya mekika tsaya kallo, yi sauri
kigama aikin dana sakaki kifece daganan kafin na
makeki mayyar banza idanuwa kamar na mujiya,
cikin rawar jiki tagama aikin datakeyi tabar
sashen mommyn!by muhd Abba Gana Allah sarki sireenah kada ki
damu" What surely goes up most surely comes
down " Ko ba haka bane masu karatu?...by muhd abba gana Haka
dai mommy tee da yan biyunta suka cigaba da
mugaye plans dinsu basu san wacce sukeyi domin
ita tana jinsu kuma tasha alwashin bazata yarda
su san Itace suke nema domin tsira da rauywarta
ko kunga laifinta. ********* Azeema kwantar da
hankalinki babu wanda ya'isa ya wulakanta mani
ke muddin ina numfashi a doron kasa, akan wata
talakar banza zai mareki har yace kun rabu yayi
kadan wallahi shidin nawa yake? Nayi maki
alkwali karshema sai ya aureki kin juyashi son
ranki kamar masa(waina) naga karshen
wulakantaki! Daddy idan hakan takasance zanyi
farin ciki sosai dakaga mani komai dunia. Kada ki
damu azeema share hawayenki kinji,Toh daddy!
Zamu ci riba biyu idan akayi aurenki dashi, hada
iri da mai martaba Yahya ribane sosai hanyar
karin samuwar arzikina ne, bana kaunar hada da
iri datalakawa, meye amfanin kabayar ba'a maida
maka? Gaskiane daddy daman ni inason aurensa
ne don nunawa dunia gwarzon namiji one in town,
zancen arziki ba'a magana ko banza shi kadaine
namiji wurin mahaifansa nasan idan mai martaba
yarasu shine za'a sakawar ragamar dukiyar! Kunji
jahila kamar tasan wanda zai riga wani mutuwa!
Haba Daddyn azeema kazauna kana biye ma
shirmen azeema nasan suhail bazai sa hannu ya
mareta muddin balaifi tayi masa ba, Kerufe mani
baki daman nasan bakya son yata kin haifeta
kawai ne amma baki kaunarta, haba daddyn
azeema wazaiki dan cikinsa naga rashin dacewar
halin nata ne tadaina wulakanta talaKawa da son
abin dunia wannan rashin gode wa Allah ne, haka
kaima naji kabawa suhail kyautAr motar naira
million 50 Wanda nasan badon Allah kayi kyautar
ba kayine idan birtday azeema yatashi a linka
maka fiyeda hakan wallahi kuji tsoron haduwa da
ubangijinku ku yawaita gode masa kudaina
hangen abin wani. Yayi malama uwar addini idan
kingama yi mana wa'azin sai kibace mani
daganan, nasha gaya maki idan bazakiyi
supporting kan abinda nakeyi da" yata ba kidinga
samana idanu! Zulfa'u ki guji randa zaki kaini
bango! Yi hakuri daddyn azeema Allah yahuci
zuciarka nadaina saka kaina cikin issue dinku sai
dai fatana gareku Allah yashiryeku yasa kugano
gaskia! Ke tashi kifice kafin ki kara tunzurani,
Haka zulfa'u ta fice jiki sanyaye. Shi Kuma yaci
gaba da bawa "yarsa hakuri da muguyen
shawarwari. Ashe azeema wurin mahaifinta duk
tayi gadon rashin son talakawa (like father like
daughter) Allah yakyauta. Daddyn azeema(Alhaji
Bello) yakasance irin marassa godewa Allah ne
abin dunia yarufe masa idanu shi kullum burinsa
yaga yafi natare dashi duk yakasance cikin jerin
manyan attajiran garin Abuja amma a banza.
Baya sadaka,zakka don yaza masa dole yake
fitarwa muddin yayi kyauta toh zaici ribane
matarsa batada irin halinsa tana son talakawa
haka tana kyautata musu itace silar arzikin
mijinta, ya aureta a lokacin da baya da wani aiki
mai tsoka, kudin gadon da aka rabane lokacin da
mahaifinta yarasu tadauki nata kason tabashi
don yaja jari Allah yasa masa hannu har yayi
wannan arzikin amma don batulci irin nasa shine
ke kyamar talaka a kullum bayada magana banda
yace talaka bayin sune(attajirai) don su bauta
(aiki) mana akayosu, Allah yasaita daddyn
azeema kozai gano gaskia "Matsayin talaka da
mai arzikin duk dayake a wurin Allah" Wanda yafi
wani wurin Allah shine Wanda yafi tsoronsa" Allah
yayi masu arzikin da talakawa don su bauta
masa" Yana sane da halin da bawansa yake ciki.
Zulfa'u bata isa tacewa "yarta ga abinda yadace
kiyi ba saboda "yarta axeema tasamu grantee
daga mahaifinta what ever she wish to do zatayi
babu wanda ya,isa yahanata. Yadauka ko sone
baisan lalaci bane, zamu gani idan zai haifa musu
da mai ido....mu hadu a kashi na gaba ************


muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive