YADDA ZAKAI AMFANI DA (FIYA) WAJEN GYARAN JIKI
YADDA ZAKIYI AMFANI DA FIYA WAJEN GYARAN
JIKI Amfani fiya ga jiki:
- Ana amfani da fiya ga busasshiyar fata don
kawo danshin fata. Tana dauke da sinadarai
masu yawa wadanda suka hada da bitamin K da
C da Copper da Iron da sauransu.
- Fiya tana dauke da sanadarin bitamin A da
kuma Glutamine wadanda suke taimakawa wajen
kawar da matattun kwayoyin halittar cikin fata.
- Laushin fata: fata takan tsotse man da yake
cikin fiya, wanda hakan yakan sanya man ya
ratsa kofofin fata, inda fata kuma takan tatse
sinadaran da suke dauke a cikin fiya, wannan sai
ya sanya fata ta yi laushi da kuma dadin gani
- Mayar da tsohuwa yarinya: Fiya tana dauke da
sinadaran da suke kone kwayoyin cututtukan da
suke kodar da fata, wanrda hakan sai ya sanya
fata ta rika sheki da kuma laushi, har a rika taken
ta mayar da ke yarinya.
- Hasken rana yana dauke da sinadaran da suke
kodar da fata ko kuma su sanya saurin tsufa,
amma sakamakon sinadarin da fiya take dauke
da shi, sai ya zamanto ta kare fata daga haske
rana.
Idan kika hada fiya da kuma man zaitun zaif
sanya fatarki laushi da damshi da kuma
sheki.Fiya da man zaitun na amfani ga
busasshiyar fata, musamman ma wajen karefata
daga bushewa ko zazzagewa.
Kayan hadi:
>Fiya
>Man zaitun
>Kukumba
Yadda aka hadawa:
* Ki samu fiya babba daya, sai ki cire bayon fiyar,
daga nan sai ki daka ta, bayan nan sai kizuba
man zaitun, sannan ki gauraya sosai,daga nan
sai ki shafa a fuskarki.
* Ki samu kukumba, sai ki daka ta, daga nan ki
shafa a fuskarki. Za ki bari har tsawon minti10.
Daga nan sai ki wanke fuskarki da ruwa mai
dumi, sannan ki yi amfani da tawulmai tsafta
wajen goge fuskarki. 2 Fiya da ayaba namatukar
taimakawa wajen gyara fatar jiki, sukan sanya
fata ta yi sheki da kuma laushi. Kayan hadi:
>Ayaba
>Fiya
>Yogot
>Man zaitun
Yadda za a hada:
1 Daga farko ki samu ayaba, sai ki bare, ki yasar
da bawon, daga nan sai ki samu fiya, ki bare ta,
sai ki zubar da bawon. Bayan nan sai ki hada
ayaba da fiya da kuma kwallon fiyar, sannan ki
daka.
2 Bayan kin gama dakawa, sai ki zuba yogot da
kuma man zaitun. Za ki ci gaba da cakudawa har
sai kin tabbata komai ya gaurayu.
3 Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki har
na tsawon minti 15.
4 Bayan nan, sai ki wanke fuskarki ko sauran
jikinki da ruwa mai dumi.
Ina zan samu fiya ko kuma de mai ake ce wa fiya da turanci?
ReplyDeleteMai fiya da turanci?
ReplyDeletewani bishiya ne mai fita wajen da ba koma yana fitar da yayanshi kamar gwanda amma cikin ba komai sai iska
ReplyDeleteAvocado pear sunanta
ReplyDeleteTO AMMA AKACE MAN ZAITUN NASA BAKI
ReplyDeleteMenene kukomba
ReplyDeleteSHIN FIYA ITACE AVOCADO?
ReplyDelete