shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 5 August 2015

sireenah**********4

muhd.jpg

Sireenah 4
*********by*********

muhd-Abba~Gana

{sharifin~Zamani}Marubuci abba gana
Kulawar Sireenah gabaki daya yakoma gun
Fateema tana kula da ita yadda yakamata don
tasamu soyayyar Alhaji Sadam kafin ta kashe shi
aiko tasamu abinda take so kunsan hausa sunce
mai da wawane but Alhaji Sadam bai furta mata
son da wuri ba gajarcen hakuri irin nata wanda
yayi sanadin komawarta gurin boka Adeku
nagarin Kogi bayan ta'isa ne tasoma bayanin
abinda yakawota boka Adeku yadakatar da ita ta
hanyar daga MAta hannu Kafin yasheka wani
muguwar daria kace tusar jaki, Muna sane da
abinda ke tafe dake kudin aikin ki 50k ne nan
Fateema ta zube masa abinda yabukata daman
tasane aikin nasa yanaci amma ga tsada Kunji
batatta Allah yashirya , kizuba masa cikin abin
shansa muddin yasha zai soki tamkar ransa zai
fita sati bazai zagayo ba za ayi auren Nan
tashiga yimasa godia da kirari irin wanda ake wa
boka shi ko sai aikin daria yake yi wadda bata da
babbanci da tusar jaki.
Bayan dawowar Fateema gida ta tarar da Alhaji
bayanan sun fita da Sireenah daman muddin zai
fita tare suke fita da tilon "yarsa wadda bai
hadata da kowa ba gabaki daya ya mayar da
komai na dukiarsa zuwa na Sireenah don yasan
bashida wani magada bayan ita amma duk
wannan abu batareda sanin Fateema, aikin
Fateema daman shine tayiwa Sireenah wanka
tashiryata sai abincin da take bata bacci kuma
wurin Alhaji takeyinsa. Rashin Alhaji Sadam a
gida yabawaFateema daman shirye shiryenta inda
tashiga kitchen dakanta ta dafa masa best food
dinsa bayan akwai Ma aikata masu dafa abinci
saboda irin gidan nanne wanda kowane aiki da
mai yinsa masu dafa abinci sunyi ta Mamakin
hakan but ba halin magana don sun san yar
gaban goshin Alhaji ce shiyasa suka zuramata na
mujiya. Tayi masa special drink wanda ta juye
gabaki daya maganin da ta amsa wurin boka
gamawar ta Keda wuya tafara jera su kan dinning
table daman ba mai shiga sashen Alhaji sai ita
don haka a sashensa tashirya komai tafeshe ko
ina da turare tasaki A.C kamshi kadai ketashi
gakuma sanyin dadin daya gauraye dakin tawuce
dakinta don tashirya ta dade a bayi tana gurza
murdadden jikinta mai Kama da kirar maza badon
da tanada duwawu ba da tuni an dade dakaita
bola tashirya cikin tufafi masu daukar hankali
tafeshe jikinta da turarukka masu karfin gaske
wanda har hawa kai sukeyi turaren babu babbanci
dana yan bori ta hamkince kan Kujerar dake
babban falon kamar gidan ubanta tana jiran Alhaji
ba afi minti biyar ba Alhaji yadawo da Sallamarsa
yashigo cikin fallon daman dabi arsa ce ko ba
mutum sai yayi sallama, Wa alaikummu salam
maraba da Alhaji magana take a yangance ta
mika hannu don amsar Sireenah tareda yimata
wasa babita Fulani nayi missing dinki Kun fita
batareda kungayya ceni ba(Fateema ce tafara
kiran Sireenah da Fulani don haka yan aikin gidan
suma suka dauka ) Sireenah daria kawai takeyi
don batada wayon fahimtar metake fada! Alhaji
ma dariar yakeyi yana fadin ayi hakuri mommyn
Fulani koda muka fita Kina barci shiyasa bamu
tada ke ba gashi bana son na katse maki jin
dadin barcin murmushi Fateema tayi tareda cewa
toh na hakura Alhaji ,muje YanZu kuci abinci
wanda nice na girka maka yau na mussaman
Alhaji yaji dadi sosai amma sai baiyi magana ba
sun dai Kama hanyar dinning bayan sun isa ne
tayi serving dinsa itakuma ta fake da bawa
Sireenah abincinta wanda Shima yana kan dinning
din a aje Alhaji nafara ci tadinga dariar mugunta
cikin zuciarta don tasan daga yasha drink din
Shikenan yazama nata yana Kafa bakinsa da kofin
bai dauke ba har sai da ya shanye drink din tas
saboda drink din yayi masa daidai yadda yake
sonsa! Mommyn Fulani Nagode sosai dawannan
dawainiya dakike damu Allah yasaka maki da
aljanna Haba Alhaji bakomai ai yiwa kaine
wannan dawainiya dakike damu yasa na yanke
hukunci kizamto mata a gareni yadda zaki samu
riba biyu biyu, Fatima kin kasance Kina da
halaiya masu kyau wanda duk wani namiji zaiyi
Kwadayin kin zamo mata a garesa samun macce
irinki sai an tona kuma a ganina Kedai ce zaki iya
rika mani amanar marainiyar "ya ta kwara daya
dana mallaka a dunia ko bayan raina ko bahaka
bane? Kinyi shiru Fateema ko baki amince dani
bane? Haba Alhaji wazaiki amincewa wannan
babban tayin naka kawai dai farin cikine yasa
nakasa furta komai (Lallai tsafi gaskiar mai shi
gasu Fateema ansamu dunia yadda akeso don
kam magani yafara aiki ) Nagode sosai da
amincewarki YanZu sai muyi maganAr auren mu
ko tunda dukkan mu munyi rashi dama tun farko
Fateema ta taba aure but sai dai itace takashe
mijinta dalilin yaka mata da kwarto saman
gadonsu na sunna wa'iyazubillah! Ta cakawa
mijinta wuka a ciki sanadiyar kokuwar dasuke
bayan kwarton yasani inda dare yayi masa nan
rai yayi halinsa itako ta tattara nata da nata
tabar kauyen aka zo garin Abuja yawon bariki
tana cikin wannan sana'ar NE taji ana cigiyar yar
aiki gidan Alhaji nan tagarzaya tabaya sai da aka
dauketa aiki ko don cika mugun burrinta don tana
sane da irin tarin dukiyar da Alhaji Sadam Keda
kuma tana Kwadayin dukiyar!
**
Bayan sun sasanta kansu inda aka daura auren
garin Abuja wanda mutane da dama sun hallarci
daurin auren!
Limamin unguwar shi ya wakilci amarya yayin da
ango kuma babban abokinsa ne ya wakilce shi...
Bayan daurin aure amarya da Ango sun sha
amarci sosai har sunje kasashe da dama yawon
honeymoon har makka yakaita sai dai wani abin
mamaki kamar maganin da yasha yafara sakinsa
don yanzu yafi bawa Sireenah attention fiyeda
matarsa Hajjaju Fateema don tun lokacin da
maganin yafara aiki baya kula da Sireenah kamar
da bata wani samun kulawa yadda yakamata sai
dai idan yan aiki suka dauketa toh wannan
kulawar da yafara bawa yarsa yana yiwa Hajia
Fateema ciwo sosai har yakai tafara shawarwarin
komawa gurin bokantq Adeku Mai hali baya fasa
halinsa don hajia Fateema ta komawa gurin
bokanta don ta mallake mijinta wanda sai abinda
tace zaiyi sai dai kamar taje a rashin sa a saboda
boka yace wannan karon muddin tanason biyan
bukata dole sai ya sadu da ita har taki amincewa
daga baya komai ta tuna Oho nan dai ta amince
da bukAtarsa bayan sun kammala yabata
maganin tana isa gida ta sawa Alhaji nan tashiga
juya Alhaji yadda take so wani abu da hajia
Fateema bata sani ba shine kwanciyar da sukayi
da boka yayi mata ciki!
Ku gafarceni anan zan dakata zan cigaba Insha
Allah Ina muku fatan alkhair

muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).