shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 23 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 27

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 27 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- nai sallama sama da goma da sauri na shiga yana zaune ya hada kai da gwiwa a salube na karasa na tsyngunna nasa hannu na dago fuskarsa wadda ta jike sharaf da hawaye idanun nan sun kada sunyi jajir ya shahid menene ba ka da lafiya ko anti ce?wayyo shahid ka bar yiwa anty kuka cikin kuka na furta kuka nake sosai na rike hannunsa gam yayi shiru wahida bbi abinda yake damuna da sauri muka zubawa juna ido har sai da muka gamsu dan kanmu na hango tsantsar kauna ta cikin kwayar idonsa ganin kallonsa na haifar min da kasala na sunkuyar da kai nace don Allah ka tashi kai wanka nan ma ba musu ya mike ya shiga toilet da hanzari na gyara masa dakin na feshe shi da airfresner sannan na fita. Shahid na fitowa sanyin ac da kamshin airfresner ya sanyaya masa zuciya hannu ya daga Allah ka bani wahida don hasken annabi da alkur'ani ya zauna gaban mirror yana kallon kansa tabbas ya rame rama ba yar kadan ba yai make up shadda yasa marun ya fesa turarensa me tsananin kamshi ya fito cikin kwalliya bakin takalmi yai amfani dashi yana fitowa wahida na mikewa inna ni zan tafi wahida ki kwana mana ayya inna ban ce zan kwana ba sai dai inna sake zuwa to ki gaida mom din.na shiga mota ina shirin tayar da motar ya bude ya shigo na kalle shi yai min kallo muje kawai na tada motar kai tsaye gidan baba rabiu ba nufa dake sabon titi ya kalle ni ina kuma zamu? na kalleshi nace yaya ina son bawa mamy sako ne bana so fa kina ce min yayan nan na kalleshi to me zan ce maka? kice min nawa ko kice min my darling uhum sai dai ince my brother ya harareni kasan sunan da nake tsananin jin dadinsa? ya girgiza kai ina son sa kai kuma baka so muce maka shine bom boy,daidai lokacin nai fakin da gudu mamy ta fito ta rungume ni ta kalli shahid dan uwa ku shigo daga ciki mana bayan mun gaisa da umminta muka wuce dakinta ta shiga hidima damu sai data cika sannan ta zauna shahid ina wuni kun wuni lafiya? ya muka ji da hakuri hakuri mun gode wa Allah Allah yai musu rahama "amin don albarkar annabi(S.A.W) n gaishe ta tace ina kika baro min mahida? tana gida.waya ta ta shiga kuka na dauka hello,naji ance daga can bangaran,salamu alaikum,aim wa alaikasalam,wahida "na'am wanene kai? wahida ba ki gane ni ba? amir ne ya hakuri? Alhamdullilahi to Allah ya jikan musulmi amin na gode,amir sai anjima na kashe tare da cilla wayar jaka don ganin yadda bom boy kole watsomin harara da wa kike magana oh yaya kenan na fuskanci tunda na soma magana hankalinka na kaina,to amir ne abokin yaya al'amin ya bugo yai min gaisuwa waya ba shi number ki ina tunanin ko gun ya amin ya amsa okey zamu haduda al'amin din taso mu tafi mamy ta ce oh bom boy ba dai kishi ba tun yanxu daku bari kuyi sallar magariba da sauri ya fice yace ba kya cewa mu kwana naiwa ummi sallama muka fita ya cemin bani key, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).