shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 3 February 2016

BANA KAUNARKA!! 13

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!13MUHD-ABBA~GANA


muna zuwa gida da gudu na fada jikin mom ina murna mom ta ture ni ni daga ni kai mom baki gane ni ba autar ki ce fa wahida me nai miki mom? kin fi kowa sani to yi hakuri mom na daina mahida ta fito tana hararata kai anti mahida me nai miki ta dungure ni ni ce ai zan ce miki anty ta kamo hannuna taso muje dakinmu na bita gaba daya dakin ta zagaye shi da manyan hotunan haidar da bom boy wani muduka sai wanda tasa aka hada mu nida bomboy ina sanye da wani material me tsananin kyau domin hoton ya dauku domin nayi kyau ainun mun dauki hotanne lokacin da mukai partin candy dinmu shima yayi kyau dama tare muka dauka amma lokacin bai nuna manufarsa a kaima ba yadda mu kai hoton in kin gani sai ki rantse muna son juna don gannin yadda na shisshige masa munyi kyau sosai ni kaina ina son hoton na kalle ta sai naga tana faman dariya na karaso yana da manyan idanu masu tsananin kyau da idanunsa ban tsoro domin in ya zare min ido sai nayi fitsari amma a yanxu suna birge ni inason kalar idanunsa masu zubin ruwan gol sam bana iya hada ido dashi domin wani shokin yake sakar min idanunsana hargitsa min lissafi sannan suna tsuma min zuciya toko shine so? kai ni na so ba son sa nake yi ba kauna ce ta yan uwantaka sannan yadda wannan dogon sajan dake kara fito da samartaka dogo ne shi domin bashi da kiba sai dai yana da faffafan kirji sannan yana da kirar karfafa jaruman maza fuskar nan kulum dauke da annuri kamala,kwarjini duk fa yadda naso fasalta muku bom boy ya wuce haka sai dai ince duk inda namiji ya kai da kyau iya diresin bom boy ya kai har ya wuce.
mahida kin san abin da yake hada ni dake kuwa? a,a kin gan ki wallahi za,ayi muguwar kazama saboda me kika ce haka? a farko kin ga dakin nan ina tunanin tunda na bar gidannan baki taba daukar tsinstiya da sunan zaki share dakin nan ba ko kin share? to ai bai yi dauda ba da kyau kinga kan kayan kallonnan kalli yadda sukai mugun kura mahida kalli zanin gado kalli tunin kayan dauda ke dai sai dai ki fidda goma ki tsoma biyar Allah kar ki ce na rana ki kece me son auro muddin kika ce kazanta zakiyi wallahi kinyi asara soyayyar kanta bata yiwuwa sai da tsafta ko ba komai da tsafta tafi inganci tsafta cikon addini ke kenan daga kallo sai karatun soyayya Allah ya kyauta nai shigewata (toilet) ina shiga na fito saboda wani zarni (toilet) keyi nace mahida kin banu toilet din ma ba kya wanke wa??


MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

  1. yayi Allah ya kara fasaha

    ReplyDelete
  2. Allah ya kara daukk muna murna

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).