BANA KAUNARKA!!! 26
BANA KAUNAR KA!!! 26 MUHD-ABBA~GANA gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba -------------------------------------------- ina tunanin daga masallaci suka fito shida shahid ne yai gun anti nai saurin cewa ya shahid kar ka tashe ta ta samu bacci cak ya tsaya ya zuba min kwala kwalan idanunsa masu tsananin kyau na lumshe idanuna ina jin wani sanyi na ratsa min duk ilahirin jikina toko shine so? no! ni nasan ko kadan bana som bom boy kome yasa oho ma muryar shahid din ita ta dawo dani hayyacina yace anty tayi sallah ne? a,a gani nai ta samu bacci shi yasa na kyale ta da sauri ya karasa ya kama hannunta jin sa yai kamar kankara yai saurin yaye bargon da wahida ta rufa mata tare da taba jikinta inalillahi wa inna ilaihi raji'un ya dago a firgice yana karkada hannu yana fadin abba anty bbu,anty bbu ya sulale tare da dafa kai da sauri abba ya karasa mikewa da gudu na karasa ina girgiza anty,anty ki tashi don Allah kar ki tafi ki bar mu anty kuka nake sosai a daidai lokacin likitoci suka shigo tun daga lokacin ban kara sanin meke faruwa ba sakamakon suman da nai.shahid bai taba shiga tashin hankali irin na wannan rana ba,don ma karfin addu'a da taimakon ubangiji ya samu nutsuwa. Bayan sati biyu wahida zaune ta hada uban tagumi wasu irin hawaye ke shatata akan kumatunta ya faruq ya shigo ya zauna wahida ya kira sunan cikin sanyin murya na dago na kalle shi sai dai sam na kaaa tsayar da hawayen,wahida ya kamata kiyi hakuri addu'a zakiyi wa anty,tashi kiyi wanka kinji Allah ya ji kanta "amin" na mike na nufi bedroom dinmu nai wanka na fito cikin atamfa gold star ba wata kwalliya nai ba nasa hijabina dakin mom na shiga nace mom zani gidansu bom boy mom ta kalle ni wahida kin ga kuwa yadda kika rame na rausayar da kai ta ci gaba,din Allah wahida ki kwantar da hankalinki ko kina so kema mu rasa ki? na girgiza kai tace to kar ki dade wai ma me zaki yi a gidansu bom boy din? mom kayana zan kwaso sannan ina son ganin bom boy domin na san..... shigowar ya faruq ce ta katse min maganar na mike kawai na fice, na zauna a motar ina shirin tayar da motar hassan me bawa filawa ruwa ya rugo da gudu yana daga min hannu, hassan dattijo ne domin a kalla zai yi shekera hamsin muna mutunci sosai domin akwai shi da ban dariya yana zuwa ya tsungunna,an gaishe ki sarauniyar kyau na tabbata duk nigeria bbu mai kyanki wahida ta mahida hajiya wahida ta alhaji al'amin family dinku na kaunarku muma muna kaunarku,domin kuna fita hakkinmu ya dan sassauta yana washe baki na harare shi ta kasan mutuwa akai min ba sorry ya hakuri? nace mun gode Allah to Allah ya jikan musulmi Allah yai musu rahama, amin nace sannan na dauko dubu biyar na bashi ya zube yana kwara godiya ya bani tausayi ainun a sallibe naja motar. nai sallama falon kakarmu da haidar suna zaune suka amsa sallamar na zauna ina gaishe su,kakarmu tace yanzu nake cewa zanje duba ki ashe kina tafe na sunkuyar da kai nace shahid na nan kuwa tace eh dakinsa na shiga nai sallama, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.