shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 6 November 2015

AL'AMARIN~zuci 41----------45

al-a-marin-zuci.jpg

[8:28PM, 10/18/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
41Kwance take duk jikin ta ya mutu,shi ko faruk sai shirin tafiya yake.
"Mimi yau bazaki taya ni shiri ba,yaya Allah jikina ne ya mutu, ni bana son kayi tafiyannan, mimi kenan to ya aka iya,tasowa tayi domin ta taya shi tsarin kayan da zai sa, kwana nawa zaku yi?kallon ta yayi kafin ya bata amsa, sati daya, haba yaya shi ne baxa ka tafi dani ba,wai sau nawa zan gaya miki ba zai yiyuwa ba,sbd bani kadai zanyi tafiyar nan ba,meza ku jeyi a China din?zamu dauki lecture a gun wani shahararren doctor,to yaya.....to yaya me?so kike sai na bata miki raine kafin intafi ko?sadda kanta tayi kasa,cikin yanayi na son tayi kuka,tana mai ci gaba da tsara mai kayan.

Ta gama tsarin kayan amma ta kasa tashi a gun,faruk ya lura da haka,zowa yai ya tasheta daga durkushen da take,Mimi kiyi hakuri wani lokacin zamu yi tafiya tare kinji, daga kanta tayi alamar taji,nan ya fahimci kuka take sonyi, rungume ta yayi Mimi kar kiyi kuka mana,kinsan bake kadai zaki zauna a nan gidan ba,to ai Ita ba kai banecikin kuka take maganar, nasani amma ai hakuri zaki yi.....karar wayarsa ce ta katse su,kinga Mimi ni kadai ake jira.
Har bakin mota ta rakashi, yashiga yana mai yi mata bye bye hadi da jefo mata kiss,ita ma haka, tana kuma yimai addu'ar, zuwa da dawowa lfya da kuma samun nasara akan abinda suka jeyi,har sai da ya bace ma ganinta,ta koma daga ciki.

Written by Bilkeesu giro
[8:30PM, 10/18/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
42Zaune take a falo tana kallo,taji nocking tashi tayi ta bude kofar,wata yarinya tagani kyakkyawa da ita ba laifi, sai dai bata da fari sosai,kuma baza ta wuce tsaran mimi ba"zaki iya shigowa cewar Mimi tare da bata hanya,bayan sun zauna ne bakuwar ke cewa"suna na khaleesat,nice kanwar abokin mijinki,wato yaya Hashim, wow nice name,nikuma suna na mimi,
Sannuki, ya karatu?Alhmdlh, kiyi hkr na jima ban shigo ba,ba komai,ai ban ma zaci zaki shigo yanzu ba,tashi tayi ta kawo mata abinci,tana ci suna fira kamar dama sun san juna.

Bayan tagama cin abinci ne ta nuna mata masaukinta,tana mai cewa"sai dai banganki da kayan sawanki ba,suna a mota ta na bari,wai koda banan gidan bane,kinga yanxu zan dauko ba tantama,haka ne fah.

Washe grin ranar, Mimi ce a kicin tana hada musu abin karya warsu,sai ga khaleesat tazo ta sameta,tana mai cewa,ke kadai ke aiki ba gayyata,ba haka bane naga zaki je school ne...wace school? yau fa weekend,kinga sam na manta,iyye sbd hutawa,wane hutawa,kawai mantawa dai nayi,ko kuma dan ba kya zuwa school ba,ai idan bana zuwa,yayana yana zuwa aiki,eh kuma fa,tare suka kammala hadawa,dama sunyi wanka,sun gyara ko ina fes fes,sai suka zauna ma ci.

Written by Bilkeesu
[8:33PM, 10/18/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
43Haka suke rayuwar su abin sha'awa,kamar 'yan uwan juna.
Yau sati daya kenan da zuwan khaleesat wanda yayi dai dai,da yaune faruk zai dawo,sun shirya mishi lafiyayyen abinci.
Zaune suke a falo suna fira,firar da baza ta wuce ta salim ba wato saurayin khaleesat koyaushe bata da fira sai ita.
"ke khalee kodai zowa za'ayi a muku aure a huta, baki da aiki sai maganarsa,koyaushe kuna manne da juna ta waya......hmmm Mimi kenan, ke da kunyi aure amma ko yaushe cikin waya,sannan wannan uwar kwalliyar da kikaci duk fa don shi ne, khalee kenan, to ai ni mijina ne idan banyi masa ba wa zanyiwa,gsky kam,ni har birge ni kukeyi,da gaske?Allah kuwa.
Nan dai suka cigaba da firar su......... cikin firar ne suka ji ana nocking kofa,aiko ba shiri Mimi ta tashi ta bude kofar,jikinsa ta fada ta rungumeshi,yayana sannu da zuwa,shima rungumeta yayi tare da kaimata kiss a kumatu,suna masu karasowa cikin falon,amma ga alama Mimi ta manta da khalee na nan falon, domin sun soma fita hayyacin su ba tare da sun bar falon ba,ganin haka ne yasa khaleesat yin gyaran murya,faruk ne ya fara juyowa,yana mai cewa "a'ah, khaleesat ya kike, ya karatu?yana mai sosa keyar sa na alamar jin kunya yayi maganar.
Lafiya kalau, ya hanya? alhmdlh,Mimi duk kunya ta hanata juyawa sai kokarin take ta janye jikinta daga nashi,shiko yaki ya sake ta,sai da ya gama gaisawa da khalee sannan suka shige daga ciki.

Written by Bilkeesu giro
[8:34PM, 10/18/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
44Wanka zaka fara yi ko abinci zaka ci?abinci zan fara dashi domin yunwa nake ji,to yayi bari na kawoma,kunci abincin ne?a'a,to me zai hana inzo muci gabadaya,no kaidai bari in kawo ma naka,takarsa maganar ne tare da fita,sai da ta gama jera masa komai da tasan zai buqata,ta fita domin suci nasu,a daki ta sami khalee kwance,"har kin kwanta,to taso muje muci abinci ko,suna cikin cin abincin ne khalee ke cewa"yau fa zan koma school bazan qara ko kwana daya ba, me kike sonyi a school wannan sauri haka, gashi gobe weekend,kinsan mun kusa fara exam fa,hake ne,na manta.
Lallai kina futawa da yawa,hmm ke kullum baki da aiki sai cewa mutum yana hutawa, ai koni result kawai nake jira yafito na fara karatu,yaya faruk zai bari ne?eh akwai wani lokaci dana tambayesa ya kuma amince,anan ma yace zanyi karatu inshaAllah, to Allah ya taimaka,Ameen.......suna cikin magana ne sukaji faruk na qwalawa Mimi kira,ta amsa kiran ne tare mikewa cikin sauri.

Yaya gani,kun karasa cin abinci,eh munkare,to muje kitayani wanka,bayan sun fito ne,take fadamasa cewa yau khalee zata wuce,saurin me take haka?kasan sun kusa fara exam, ok yayi Allah ya taimaka.

Written by Bilkeesu
[8:34PM, 10/18/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
45Yaya please katashi muje muyi ball,Mimi me yasa kike son muyi ball?kullum sai munyi nida khalee,amma tunda ta tafi ban sake yi ba,sbd baka bari,Ita khalee har tana da lokacin ball,ksan morning lecture takeyi,sai muyi ball da maraice....yaya meyasa baka bari,sbd yanayin jikinki yanuna kina da ciki,kai yaya har naji kunya wlh,kunyar me Mimi?ai ni yarinya ce ban isa ba,Mimi kenan..... yau wata mu biyu da zuwa london fa,kinga kenan cikinki wata daya,amma bani da tabbacin ko ya kai wata daya sai na aunaki,yaya to muje shan ice cream,kinganki Mimi ba kya bari mutum ya huta......oya tashi ki shiryo muje.....yeeee! Yaya thank u,ganin yadda ta tashi da gudu ne, yasa ya dakatar da ita,cikin tsawa"Mimi!juyowa tayi ba tare da ta karaso ba,zo Mimi,cikin sanyi murya yake magana.
Mimi pls ki daina gudu kinji,sbd cikin nan bai yi kwari ba,zai iya zubewa ako wane lkc,idan kuma ya zube a dalilin ki zamu iya samun matsala,pls take care, yaya kayi hkr inshaAllah hakan bazai sake faruwa ba.

Written by Bilkeesu giro
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive