shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 6 November 2015

AL'AMARIN~ZUCI***56--------60

al-a-marin-zuci.jpg

[11:49AM, 10/22/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
56Koda Mimi ta tashi daga bacci, sai kamshin turaren faruk ta ke ji a jikinta,
Dakin momy taje,da sallamarta tasamu ta sallame sallah kenan,"momy yaya ya shigo ne?ya shigo domin kuyi sallama,ya samu kina bacci ya tafi abinsa.....zuwa ina? ina kika san zai je?wai da gaske yake ba zai je dani ba,ta karasa maganar ne cikin kuka.
Daga gani wannan kukan har da yunwa a cikinsa tashi kije kisamu abinda kika ci,tunda kikayi sallar asuba kina nan sai faman bacci kike har 11am, Momy Allah yaya bai kyautamin ba...Mimi jeki inaso inyi lazimi.
Tashi tayi ta bar dakin,tana mai cewa a cikin ranta "lallai yaya har ni zai yima haka,wato da gaske yakeyi kenan,ba komai zan rama ne.
Sai da tayi wanka sannan tayi lokacin kari,fresh milk ta dauko tana sha har sai da taji tayi makil,sannan ta tashi taje bagaren su kaka,ko zata rage jin zafin abinda faruk ya mata.
Sallama dai masu gida,wa Alaikissalam,...to fa kinzo ba sauran hutu...karki damu ni bacci ma zanyi, amma dai tukuna ina mijina?ya fita,amma kike a dakinsa kina kyro magana,gyaran dakin nake....haba kaka bari na gyara mana tunda nazo,a'a yi baccinki ai har na kammala,don Allah kaka sai anyi sallah zaki tasheni... to naji 'yar iya yi, murmushi kawai mimi tayi batare da tace komai ba.

Written by Bilkeesu giro
[12:45PM, 10/22/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
57Yau sati Biyu kenan da taffiyar faruk, kullum yana kiran Mimi amma bata daga waya, da yaga haka ne sai ya kira Momy yace aba Mimi, ansar wayar kawai take bata tare da ta aza a kunnen taba, sai taje daki ta aje, har sai ya gaji ya kashe,sannan ta mayar ma Momy da wayar, ba tare da tasan abinda ake ciki ba.
Zaune suke a falo suna kallo Mimi ke cewa"Allah momy yunwa nake ji,a'ah to waya hanaki cin abinci?tashi tayi taje ta bude frij amma ba fresh milk, Momy babu fresh milkai da gangan na kyautar da ita sbd na fahimci ba kya cin abincin in akwai ta, Allah Momy bazan iya cin komai ba sai Ita,shiyasa.
Ashe ko aiki ya same ki,pls Momy.....ba wani in zakici abinci kici.

Tashi tayi taje bangaren su faruk,tana tunanin baza'a rasata ta ba.Da sallamarta ta shiga,sai dai waya umma take amma, hakan bai hanata amsa sallamar ba, tare da tambayarta me yake damnta, sbd fuskar ta nuna akwai dmw.

Umma fresh milk nake so in za'a samu pls, sosai makuwa Mimi,....gashi wai zaku gaisa ta mika mata wayar ta fice,batare da gaya mata waye ba.

My Mimi wannan horo haka, ai yayi yawa, pls am so sorry,wani irin hausin sa taji.
Hmmmm me kuma kake so kace dani yanzu, bayan bana da, wani amfani a gareka.....dai dai umma ta fito gashi bata so taji, mika mata wayar kawai tayi,har kun gaisa? eh umma,to ga fresh milk,ta amsa tayi gdy ta fita.

Written by Bilkeesu
[5:16PM, 10/22/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
58Tana dawowa kawai sai ta fada jkn Momy, tana magana a tsorace,"wayyo Momy motsi nake ji a cikin cikina,ke Mimi kodai yunwa ce... hannun Momy ta jawo ta aza a cikinta, mamaki qarara a fuskar Momy, tana cewa,

"Mimi dama cikin ki bai zube ba ne,domin wannan cikin daganinsa yayi wata biyar,tashi muje asibiti.

Haka kuwa akayi domin doctor ya gaya musu wannan cikin kadan ya rage ya cike wata biyar, sai dai da alama cikin ya zuba,ha kan yasa ya kwanta,amma yanzu komai zai zo normal inshaAllah,cike da farin ciki suka dawo gida.

Nan take family kowa ya sani sai murna ake, akasin faruk da aka kira wayarsa, a kashe take,amma tuni abban Mimi ya sani,domin har ya kira ta yana taya ta murna.

Zaune take tana shafar cikin ta wani irin farin ciki, ke ziyararta,tana cewa"Allah na godema, dakasa cikin nan bai zube ba, naso ace yaya, na nan, da yake ganin banida wani amfani,naga ya zaiyi,ya zaiji,me zai ce mun.

Written by Bilkeesu giro
[9:05PM, 10/22/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
59Bayan sati daya da faruwar haka.
Mimi ce kwance abisa 3 seater,bangare su faruk tana bacci,umma ko tana yanka kankana,sallamar faruk taji,ta amsa sallamar ne cike da mamaki,umma sannu da aiki yauwa sannu....amma meyasa baka kira zaka dawo ba,Allah umma wayata ta fadi,yau sati daya kenan,ganin aiki yayi min yawa shiyasa ban yi lokacin sayen wata ba.

Umma me za'ayi da wannan kankanar haka da yawa?kasan yau ne meeting.... eh shiyasa ma na dawo da wuri domin ina son in halar ci meeting din.

My Mimi..... bacci take fa karka tashe ta, me yake damun Mimina wai duk ta rame...... har ka tambaya bayan kasan ciki ne da Ita,ciki Umma?dama bai zube ba?dan guntun tsaki umma tayi,sannan,tace "zafin zuciyar ka ai bazai bari ka fahimci ya zube ko bai zube ba,tunda ko duba ta bakayi ba,Allah umma a lisafina cikin bai wuce 3 month ba,Sam na manta yakai 4month har da sati koda muka zo amma don Allah umma ayi hkr,da kuskuren da nayi na rashin duba ta,mu dai fatan mu Allah ya sauke da lafiya, sassanyar ajiyar zuciya yayi,kafin yake cewa "Ameen umma.
Kallon mimi yake cike da sha'awa taqara,haske,smooth, kyau,ga qirjinta da yaqara cika,sai wani irin abu yakeji.......umma ce ta katse shi,tana mai cewa,"ko kana bukatar abinci akawo ma?a qoshe nake umma' sai dai ko zuwa anjima.

Written by Bilkeesu
[10:06PM, 10/22/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
60Kowa ya hallara a gurin meeting Alhaji ya bude da addu'a, bayan haka suka fara tattauna wa akan lamurran family,ciki harda magana akan asa ranar auren Hafiz da Ali rana daya.
Duk abin nan da ake faruk hankalinsa na kan Mimi, ya matsu a qare ya gana da Ita,domin ya fahimci,har yanzu fishi take dashi.

Aiko ana gamawa ya riko hannuta da sauri,"Mimi pls kiyi hakuri da abinda nace miki ranar,wlh wasa nakey miki,asalima bako London naje ba....ok yanzu tunda kaji cewa cikin yana nan, shine zaka cemin wasa kake,bana son wani kwantar min hankali da zakayi,na riga da nasan cewa baka sona,sha'wa...no Mimi kar ki fadi haka,wallahi tuni na dawo gareki Mimi inasonki so na har abada,ai nasaba jin wannan yaya, sai ka zanxa wani salon.

Mimi ba lallai bane ki iya ganin yadda nake sonki, ba lallai bane kisan yadda na dauke ki ba, ba lallai bane kiji yadda nake kewar ki ba,domin ta zuciyata ne Kadai zaki iya gani,pls Mimi ki duba min fa,tunda naje nake kiranki a waya, amma ba kya daga wayar,kinaso kicemin wannan duk don cikin ne?...... sai kawai kuka yaci karfinsa,saurin dago kanta tayi domin bata zaci abin zai ga kuka ba,sai taji gabaki daya ya bata tsusayi,"yaya ka daina kuka please,indai nice na hkr,rungume juna sukayi suna kuka,Mimi I love u,love u too,yayana,

Tafi raf raf family ya dauka, har da su shewa,gaba ki daya sun manta a gaban family suke maganar,domin faruk bai ko bari aka fita ba ya riqo hannun Mimi.

Ahaa muje zuwa

Written by Bilkeesu giro
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive