shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 6 November 2015

AL'AMARIN~ZUCI***46----------50

al-a-marin-zuci.jpg

[6:27PM, 10/20/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
46Bayan wata daya da faruwar hakan.
Mimi ce a bisa lilo sannu a hankali take yi,tana mai rera waka cikin natsuwa,karar budewar gate taji da alama faruk ne sbd lokacin dawowarsa ne,hakanne yasata tashi domin ta tarboshi kamar yadda ta saba,da Isar ta gun ya ware hannayensa,fadawa jikinsa tayi tana yi mai sannu da zuwa,tare da amsar jakar hannusa,suka karasa daga ciki,sai da yayi wanka sanna suka zauna cin abinci,budewar kula keda wuya taji wani irin amai ya tunkarota,aiko ba shiri ta haura sama domin zuwa toilet,faruk na biye da ita har toilet,sai sannu yake mata,ba iyaka,da ta gama,ya dauko ta ya aza abisa gado,yana mai yimata sannu,
Anan yakawo musu abinci domin suci,"yaya ni baxan iya cin wannan abincin ba,asali ma shi ne ysa ni amai,to me kike son ci?fresh milk,ai bazakiji kin koshi kamar abinci ba, eh nidai kawai abanni nasha,tashi yayi ya dauko,ya tsiyaya a cup ya mika mata,tana gama sha sai bacci abu ga mai ciki.

Haka yake fama da ita kullum, bata iya cin komai sai fresh milk, ga yawan bacci,amma hakan bai sa ta rage bashi kulawa kamar yadda ta saba ba.

Written by Bilkeesu giro
[6:27PM, 10/20/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
47Akwana a tashi yau cikin Mimi yakai wata uku.
Kwance take a bisa kirjnsa sai zuba shagwaba take,
"Yaya yaushe zamu je gida ne?not now,yayi maganar ne a takaice,meyasa yaya?Mimi inaso ne sai cikin nan ya fara kwari, sbd bai zaunu da kyau ba,irinshi yafi saurin kawo matsala,
yaya pls kayi hakr mutapi ,inshaAllh baza'a samu matsala ba,kibari nan da wata daya mugani, to Allah ya kaimu,Ameen.
Tashi ki dauko fresh milk kisha, domin daganin cikinki yunwa kike ji,tun dazu ma nake son tashi amma kasala ta hanani, ta karasa maganar ne tare da mikewa,garin dawowa ne tayi tntube da center capet ,da sauri yatashi ya tarbo ta, kar ta kai qasa,"sannu bakiji ciwo ba dai ko?girgiza kanta tayi alamar a'a.

gama shan fresh milk na aunaki inba matsala,tana gama sha ya duba, ba matsalar komai,wani irin ajiyar zuciya yayi,yana mai cewa "Alhmdllh.
Ita dai Mimi sai kallonsa take cike da mamaki,faruk ya lura da hakan,
Yadai kallonfa....hmm nidai yaya mamaki kake bani,kasa cikin nan a ranka sosai,ko ranar da kamin tsawa akan nayi gudu Allah sai da na firgita,aida da kinji yadda gabana ke uku uku sai kinfi mamaki,to ai yaya sa abu a rai da yawa yafi kawo Matsala,haka ne Mimi nima na tsinci kaina da son haifuwa,sai gashi kin samu ciki ba jimawa hakan yayi min matukar dadi,sai dai cikin yana da 'yar matsalar da ba'a cika son yawan motsa jiki ba,shiyasa kika ga na fiye damuwa akansa.

Written by Bilkeesu giro
[6:51PM, 10/20/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
48Yaya dama duk sabon ciki haka yake?a'a sbd bai shiga da kyau bane......karar wayarsa ta katse su,yana magana akan tafiyar su Nigeria nan da sati mai zuwa, wani irin dadi Mimi taji har ta matsu bai karasa wayar ba,yana ajiye wayar,take tambayarsa,yaya amma zamu dan dade ko?akan me?zamu daiyi sati, haba yaya kabari mu danyi ko wata daya mana,noo ina da anbinyi da yawa, sannan ai idan lokacin haifuwar ki yayi a gida zaki haifu inshaAllah kinga kenan zaki sha gida hadda style, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
Yau ne sati daya ta cika,su Mimi sai shirye,shiryen tafiya ake,"wannan zazzadin haka mimi sai kace wacce tayi shekara bata je gida ba,na fa yi kokari yaya sbd ban taba irin wadan nan watanin bana gida ba fa,to naji kiyi sauri kinsan fa karfe goma zamu daga, to yaya......Allah sarki yau zanga su kaka.

Karfe 10am cif su ka daga sai Nigeria.


NIGERIA

Koda suka sauko daga jirgi har sun samu su umma sunje tarbonsu, wani irin dadi Mimi taji kamar ta ruga da gudu, amma ba hali sbd rikon da yayi mata,yasan idan ba haka yayi mata ba zata iya gudu,suna isa ta fada jikin umma,shiko faruk ya dan rissina yana gai shesu.
Yauwa sannuku ya hanya Alhmdlh umma,har yanzu son jikin na nan kin wani lafe a jikin ta,sai kace mage,cewar momy,he Momy..... ba wani haka ne, cewar faruk,gabadaya suka dau dry suna masu shiga mota.

Written by Bilkeesu giro
[6:51PM, 10/20/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
49Bayan sun isa ne sukaje ko wane bangare ita da faruk,suka gaishe su,da suka je bangaren su kaka ne,kaka sai cewa take"wai dan kunjin nan naki bai fara fita bane?kai kaka.... wai dama yaya ya fadi,shi ne naga kowa sai kallona ake....wannan farin ciki Mimi bazan iya boye saba,amma yaya akwai kunya kowa sai kallona yake, tayi maganar ne a cikin shagwaba,
Yo ke har wata kunya ce da ke jifa yanda kuka wani makalewa juna,dagani haka kuka je kowa ne bangare, ai shi zaki gayawa haka kaka,yo shi namji ne fa,ba haka nake nufi ba,ta yaya mutum yace baya son auren, amma sai makale min yake baya ko jin kunyar kalmar da ya fada kafin ya bar gidan,tana magan ne a cikin zuciya,kuma da alama faruk ya fahimci me take nufi, domin ya janye jikinsa daga nata,ba tare da yace komai ba.

Zaune suke a falon su Mimi, suna fira,da alama abinci suka gama ci.......karar wayar mimi ce ta kaste musu fira, koda ta duba, Zainab ce, ta dagar wayar tana cewa"Zee......ba wani zee, kinzo gari ko ki gaya min saida yaya Hafiz ya fadamin, sorry pls so nayi nabaki surprise ki ganni kawai a gidanku,ai na riga ki domin ni yanzu haka ina bakin gate gidanku...da gaske? Allah kuwa,da gudu ta tashi tare yadda wayr a saman kushin, ta nufi hanyar fita.....Mimi!Mimi!! Mimi!!!yaya pls ina zuwa. Batare da tsaya ba,ta ci gaba da gudu ga gate din akwai dan jayawa.

Written by Bilkeesu giro
[6:52PM, 10/20/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCI Na Bilky giro
50Momy kin ganta ko,ta kuma san matsalar da kenan fa,yi hkr faruk bari ta dawo ai zata gane kurenta,
Ba a fi minti 3 ba sai gasu sun shigo Ita da Zainab,sai da zainab ta gama gaishe su, sannan momy ta fara da cewa "wai ke Mimi meyasa har yanxu kanki yana rawane,har da xa'a kira ki, kikaqi dakatawa,sai magana da kika jefowa mutane sbd rainin wayo!,Momy pls kiyi hkr....ai bani zaki bawa hakr ba,faruk zaki bawa hakr,shiko faruk tun shigowar ta, da yayi mata kallo daya bai sake ba,sbd yayi matukar hasala sai huci yake.
A tsorace Mimi taje gurinsa tana mai bashi hakr,daga kansa kawai yayi alamar yaji,batare da ya ko kalle ta ba.
Zainab muje daga ciki,bayan sun shiga ne Zainab ke tambayar ta,"me yake faruwa ne Mimi?kinsan ina dauke da junabiyu shi ne ya hanani gudu,sai akayi rashin sa'a na manta nayi,
ke kuwa gashi baki da abinyi in farin ciki ya sameki face gudu,wlh kuwa, ni abun yana damuna, inaso indaina amma abu ya faskara,kiroqi Allah sauki mana,haka zanyi,inshaAllah,nan dai suka cigaba da firar su,a cikin firar ne Mimi ta dan fara jin marar ta nayi mata ciwo amma bata so Zainab ta fahimci hakan,tun tana jurewa har abin ya faskara,anan Zainab ta fahimci halinda Mimi take ciki. "
yadai Mimi? marata zainab....na shiga uku, sannu ko,bari inje ingaya ma su momy......a'a kar ki fada don Allah bari mugani zuwa anjima ko zata daina,tun tana bisa gado har ta sauko kasa sbd ciwon ya tsananta,Mimi pls kibari na je.......oh no!Mimi jini fa ke zuba a jikinki...ba shiri zainab ta fita da gudu domin ta fada ma su faruk.
Muje zuwa domin jin yadda zata kaya.

Written by Bilkeesu giro
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive