shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 6 November 2015

Hukuncin Tsuntuwa

sabo.jpg

NA TSINCI NAIRA ₦500 KOZAN IYA AMFANI DA ITA
BATARE DA CIGIYA BA ???
Tambaya ?
Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya
tsinci Naira 500, kuma baiga wadanda zai yiwa
cikiya ba...
Yaya kamata yayi da wannan kudin tsintuwar ?
Suna ajiye yanzu haka kusan wata daya kenan.
(Daga Ibraheem Ishaq Rano).
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa idan mutum yayi tsintuwa ya wajaba a
gareshi yayi cigiya har tsawon shekara guda, idan
bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da
ita, amma idan mai ita yazo daga baya zai biya
shi.
Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisinsa mai
lamba ta: 5761.
Amma idan abin daya tsinta dan kadan ne bashida
yawa, to ya halatta yayi amfani dashi koda baiyi
cigiya ba.
Saboda abin da aka rawaito cewa:
Annabi (s.a.w) yaga wani dabino akan hanya, sai
yace:
In banda ına tsoron kona sadaka ne da naci.
Muslim ya rawaito a hadith mai lamba ta:2527.
Sai hadişin ya nuna dan karamin abu baya bukatar
cigiya.
Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da
bata bukatar cigiya.
Wasu sun ce za'a koma al'adar mutane, duk abin
da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to
idan an tsince shi baya bukatar cigiya, Ibnu
Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa:
Bai wajaba mutum yayi cigiyar abin da bai Kai a
yanke hannu saboda shiba, wato daya bisa hudun
dinare.
Haka nan sayyadina Aliyu (R.A) ya tsinci dinare
daya yayi amfani da ita batare da yayi cigiya ba.
Abin daya gabata yana nuna cewa:
mutukar baka sami mai Naira (500) din da ka
tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta kayi amfani da
ita batare da cigiya ba, tunda ba kudine mai yawa
ba, kuma mai ita bazai kwallafa rai Akantaba.
Domin neman karin bayani aduba: Al-mugni
6/351.
Allah shine mafi Sani.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive