shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 20 November 2015

KAUNA CE SILA 1--2--3

kauna-ce-sila.jpg

[10/11, 2:39 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 1





**********NA************



MUHD-ABBA~GANA








garin ya kasan ce mai dadi saboda yanayin damuna da muke ciki garin ya yi luf-luf da alamar hadari ga wata iska mai sanyi da take kaduwa ranar laraba ne shida ga watan goma shekara ta dubu biyu da sha biyar wannan ranar ta kasance ranar farin ciki ga daliban mkaaran tar kwana ta kimiyya wato garko don a ranar ne suka kammala karatunsu na secondry wato candy idan ka duba harabar makarantar dalibai ne ko ina sanye da fararen uniform mai ratsin kore suna ta musayar adireshkn gidajensu ne wasu kuma suna tsattsaye yayin da suke jiran a zo a dauke su don zuwa gidajensu a gefe wasu aminnan juna ne a zaune a gindin bishiya darbejiya wato mama da kawarta maryam maryam ta kalli mama tace mamaa nace mata na'amm tace tunda har yanxu mama bata karaso ba rakani shagon hanyar hostel na siyo bread yunwa nake ji nace mata to tare da mikewa mun tashi kenna tana zaro kudi a jakarta na hango motar mama nace mata maryam ga mama nna sai ta juyo da sauri ai kuwa mama ce nna muka karasa cikin sauri da murmushi dauke a fuskarta ta tare mu tace a'a yan mata yan garko to congratulations muka hada baki muka ce mata thank you sanan muka gaishe ta mama ta bude mana boat muka fara zuba kayan mu sanan muka bita ta karbo mana pass a ofisin shugabn makaranta bayan mun fito muka dauki hanyar fita maryam ta shiga gaba nikuma na zauna a baya fitowar mu kennan mun dan hau titi mama ta dan rage tafiya ta fara magana kamar haka:








MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
[10/11, 2:57 PM] Ábbä~Gåña: KAUNA CE SILA 2










MUHD-ABBA~GANA



To alhamdullilahi yau kun gama makaranta Allah ya gani mun baku tarbiya daidai gwargwado ina kara jan hankalin ku da ku nutsu ku sanya tsoron Allah a ranku domin yanzu ne zaku fara rayuwa kuma zaku fuskanci kalubale iri iri sannan zaku hadu da kawaye daban daban masu kuma tarbiya daban daban ku kula sosai dan irin mutanen da zakuyi mu'amala Allah ya yi muku albarka mukace ameen a tare nida maryam mama tana kai aya ta karo sautin radio ta mike hanyar kano.tafiya muke tayi cikin nutsuwa da kwarewa amma a hakikanin gaskiya hankalina baya tare dasu ina ta tunanin gaskiyar hankalina baya tare dasu ina ta tunanin maganganun mamaa suna ta min kuwwa a kunne in ta jujjuya su to wani iri kalubale mama take nufi zamu fuskanta kalubale hum a hakan ne ta lura da maryam har bacci ya dauketa mun iso kano misali 1pm daidai mun isa tarauni layin uba yan katsere daura da gidan shakatawa na tarauni wato garden a kofar gidan mama ta ajiye ni yayin da suka wuce gidan su wanda yake a kano bus stop ina shiga gida na tarar da ummanmu ta fito daga bandaki ita da buta a hannunta zatayi alwala sai kawai ta ajiye butar ta taro nida fara arta tace oyoyo yan garko yau dai kukan komawa ya kare sai nayi dariya na bude baki da zummar gaisheta sai kawai naji hawaye wanda bansan dalilin zubowar suba ta kalle ni tace ikon Allah to meye haka? shi kenan to shiga ki cire kayan kizo kici abinci dana shiga daki saina saka daya daga cikin kayan da muka dinka na fitar mu doguwar rigar shadda mai ruwan jinin kare na fito don yin alwala ina idar da sallah na zauna kenan zan fara cin abinci nace wa umma wai ina baba ban kuma ga sadiq ba.






MUHD-ABBA~GANA

09039016969





www.abbagana.pun.bz
[10/13, 7:58 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 3












MUHD-ABBA~GANA





TAce min bababku yayi tafiya muna sa ran shi jibi shi kuwa sadiq yana makaranta an jima kadan zaki ganshi ina cin abinci amma ina hammma don baccine a idanu na saboda gajiya da muka sha ga hayaniya da koke koke kowa dai yasan yanda yan makarantar kwana suke yi a lkkacin da ake ce musu zasu fita ina gama cim abinci na fara bacci ban tashi farkawa ba sai hudu da mintina kamar goma shima umma ce ta tasheni da kyar dai nayi sallar la a sar ina tashi naga safiq kanina yana cin abinci ya kalleni da murmushi yacemin yyaa mamaa congrats! nace masa tnx you bayan na idar da sallar la'asar ne nayi azkar na shiga bandaki na watso ruwa na canja kaya nazo na zauna a tsakiyar su muka fara hira nna na dinga jin labaran abubuwa da suka faru da bana nan wani nayi dariya wani naji tausayi har da labaran wa'yanda suka riga mu gidan gaskiya duk nace Allah ya jikansu ya kyauta namu karshe haka muka kai har dare muna shan hira dan sallah ce kawai take tashar damu har lokaci kwanciyar bacci yayi muka kwanta tun asuba muka tashi abinka da gidan da kowa aiki yake tafiya umma ta riga mu karyawa da misalin bkawai ta tafi aiki don tana koyarwa ne a makaranatar primary ta gwammaja dake kano atare da sadiq muka karya shima muna gamawa ya tafi mkaranta sai suka barni ni kadai a gida bayan na gama sauran aiyukan gida da suka rage sai nayi wanka na saka wani dinki riga da wando kamar fakistan amma da material aka dinka mai launin shudi mai duhu da misalin karfe daya saura na rana umma tashigo tare da sallama nayi mata sannu d zuwa ta shiga dan rage kayan jikinta












MUHD-ABBA~GANA
09039016969





www.abbagana.pun.bz
Share:

3 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive