shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 5 December 2015

KAUNA CE SILA*** 46__50

kauna-ce-sila.jpg

[11/29, 10:41 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA46
MUHD-ABBA~GANA
MUKAYI sallama na kashe wayata na koma studio muka cigaba da abin da muke yi har lokacin tafiya ta gida yayi wata rana ina zaune a vocal sai ga marwan bayan mun gaisa ya zauna yace min yayanki ya kirani sun sauka lafiya nace ina ya tafi yace yana saudiya nace Allah sarki ni ban sani ba yace to ki kira shi mana nace a'a ai in har bashi ya kirani ba to me zan kira nace masa yace haka ne nasan zai kira ki nace ehm ni dai mun cigaba da hira yayi dariya muka ci gaba da hira har dai ya gaji ya tafi ranar wata juma a da daddare ina waje muna hira da salisu bayan ya tafi na koma gida sai naga missed call har biyu da number mai dauke da + alamar number waje nan ko na hau kira ina tunanin waye wannan nasan dai akwai wata anty na da taje saudiya amma ita mun yi waya har nayi saving number ta to waye wannan har ta gama ringing ba a daga ba sai nima na share kawai nayi kwanciyata,bayan kamar kwanabiyu muna zaune muna hira da zainab a gidan mu ranar lahadi ne dama bama fita ranar lahadi sai dai idan kiranmu akayi sai ta fara yi min hirar ya ahmad a idan fa kika ga mutunmin nan kome kikeyi nutsuwa kike yi kuma komai yasa ki jikinki na rawa kike yi gaskiya kin damu da shi sosai sai nayi dariya nace ni kin tunamin ma naga an kira ni shekaran jiya daga makka bara na kira ko shine nan na fara kira ana dagawa sai naji ace waye ke magana? nan kuwa raina ya baci na fara magana da fada nace to ba kirana akayi da wannan number shekaranjiya.


MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[11/30, 8:50 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 47

MUHD-ABBA~GANA
sai naji yace ina nufin kin gane me magana sai a lokacin na dauki murmushi ai kuwa wani irin ihu na saka nace ya ahmad dama kaine yace nine ya gida nace lafiya nace masa zan kira ka da daddare yace to ya kashe zainab ta kalleni tana dariya tace zata tafi muka fito tare dan na rakata ta hau mota ta tafi gida tun daga wannan rana kullum sai na kira ya ahmad yawanci nafi kiranshi idan nazo kwanciya ba wata hira muke yi ba amma duk lokacin da muka yi magana da shi kwana nake cikin farin ciki har recording nake kawai dan in dinga jin maganarshi haka ne ya kasance tsakaninmu har ya dawo lafiya mun koma makaranta yayin da karatunmu ya kara daukan zafi don a lokacin ne muke shirin shiga zangon karshe a aji daya a wannan lokaci bana baro makaranta da wuri saboda yawan rext da assingment da muke yi ga practicals kusan ko yaushe.MUHD-ABBA~GANA
KAUNA CE SILA 48


MUHD-ABBA~GANA

Watarana na bar makaranta kamar uku da rabi ina zuwa na tarar da hauwa nace mata garin ma hadari kamar ruwa za a yi tace ai hadarin nan tun safe nace to Allah dai ya bamu wanda zamu iya ina zaune sai wani ya shigo yace wai nazo wani studio a kasa nayi masa amshi nace ina zuwa nacewa hauwa bara naje na dawo tace to ina zuwa sai na tarar da mai wakar ya fito ya gama nashi ina kokarin shiga sai na ajiye wayata a kusa da computer na shiga ina shiga salisu ya shigo yana ganin wayata ya dauka na dan zuro kaina nace dan Allah ban waya ta bai saurareni ba ya fara dubawa ban san ne yake dubawa ba nima kawai na ci gaba da yin aikina.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11/30, 8:56 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 49

MUHD-ABBA~GANA


ina fitowa bayan na gama sai naga salisu sai masifa yake yi wasu a gefenshi suna zifa shi nace masa ban wayata zan hau sama sai cewa yayi ba zan bayar ba nace to ai ba kai ka sai min ba kawai sai naga ya nuna min text da na yiwa ya ahmad amma wayar tana hannun shi SALAM YAYA YAU TUN DA SAFE NAJI INA SO NA GANKA KO NAJI WANI ABU DAGA GAREKA DUK INDA NAKE TUNANIN ZAN GANKA NAKE BAN GANKA BA KU SHA RUWA LAFIYA. lokacin dan a karanta abin da salisu ya nuna min kasa cewa komai nayi da nasan dai ni nayi na ma manta yana wayata amma to meye laifin abin da nayi ai yaya nane ina ta zancen zuci sai naji yace wallahi ba zan baki wayarnan ba duk abin da zaki iya kiyi ni tun da muke da ke kin taba cewa kina son ganina? nayi masa banza da naga da gaske yake kawai sai nayi tafiyata sama na bar shi anan yana ta masifanshi na samu hauwa na bata labari tace amma bai kyauta ba meye haka nace oho masa da wajen karfe biyar sai na leka ban ganshi ba na tambaya ake ce ya tafi na dawo nace hauwa dan Allah aramin wayarki na kira shi tace gashi dana kira sai yace min sai anjima zai dawo ina zaune ina jira har hauwa ta tafi ta barni abu kamar wasa har shida na yamma tayi ba salisu ba labarinshi na sauka neman shi ban ganshi ba ina tsaye sai ga ifan yace baki tafi ba na fada masa abinda yake faruwa sai naji ya kira salisu ta wayar shi ban san ya suka yi ba sai naji yace yana fa gida bana jin ma xai dawo zoo road yau nace dan Allah kai ni gidansu nasan kasan gidan su yace hau bayan mashin muje na kaiki.

MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[11/30, 9:12 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 50
MUHD-ABBA~GANA
Muna zuwa muka same shi a kofar gida ganinmu sai yayi kicin kicin kamar bai taba fara'a ba ganin haka yasa nima na sha kunu nace salisu waya ta nazo karba yace shine zaki biyo ni har gida? eh naga ai ba kai ka siya min ba yace bani na sai miki ba amma wallahi ba zan bayar ba ina jin ya rantse kawai na juya wani irin hawaye masu dumi naji suna bin fuskata ban iya tsaya gogewa ba ina bayan mashin ina kuka har naje gida raina ba dadi dan nayi kuka kamar raina zai fita kusan ana fitowa daga sallar magariba na karasa gida ina ganin shi yasa umma bata gane halin da nake ciki ba nima ban nuna mata ba da daddare da na dauki wayar umma na kira layin sai naji a kashe nan nayi tunanin kawai bara na kyaleshi da safe muna gama lecture din farko husna ta tambayeni lafiya nace rainane a bace nan na fara bata labari
[11/2, 9:45 AM] Abba~Gana: tace haba wai shi me yasa yake haka ne nace ina zan sani tace bara na kira shi nan dai ta kira shi ban san ya suka yi ba daga karshe dai naji tana cewa sai kazo bayan kamar awa daya yayi mata waya gashi ya shigo tace gamu nan zuwa a dab nesa da su na tsaya ina hango shi yana ta mata wasu bayanai a karshe dai ya bata wayar ta nufo gurina tun kafin mu karasa aji ta fara bani labarin yanda sukayi na farko ganin text din da na yiwa ya ahmad shi ya fara bata masa rai sannan wai yaji wata waka da ni na saka aka yiwa ya ahmad nayi saurin katseta na ce wallahi bani bace wanda yayi wakar ne yace naxo nayi masa amshi ya yiwa ya ahmad wakar ni kuma sai naki zuwa? ban ga laifi a ciki ba tunda dama aiki na ne sannan ya ahmad yayana ne dan na taya anyi masa abu ba komai.
www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive