shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 16 December 2015

KAUNA CE SILA***2***36 & 37

kauna-ce-sila.jpg

[11/30, 11:46 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 36


MUHD-ABBA~GANA

sai nayi sauri nace a,a ai layin wata kawata ne da muna waya da ita sai yace to ga wayarki nace masa na gode wannan abu da ban mamaki yake dama yaya ne kwanaki ya dinga min haka lallai to meye hikimar shi tayi min haka nace kai ban yarda zai iya min haka ba amma bara nayi binciken da zan iya ko zan gane ina hanyar gida na kira layin rabi,u direban yaya nace masa dan Allah kana da layin yaya wani glo sai ya ce eh nace dan Allah turo min yanzu fah sai yace to abinda ya rikitar dani shine layin ba abin daya bambanta su lallai yaya to meye nayi min haka bayan ya san duk duniya ban taba san wata halitta kamar shi ba sai na fara sake sake to yanxu na nuna masa na gane kona share kawai sai wata zuciyar ta ce kawai ki share tunda kema haka yayi miki kuma baki san dalilinsa nayin haka ba da haka kawai na bar zancen yau tun da safe dana fito aiki nake tayi kuma a gurin su yaya ahmad dan wakokin biki zanyi guda biyu na gama dayar sai nace wa mai dauka na bara muyi salla tunda lokaci yayi ina idarwa na dan fito waje sai muka hadu da marwan bayan mun gaisa da fara'a ta nace masa ina yaya nane ni yau tunda na fito ban ganshi ba sai yace nima rabona dashi tun jiya da daddare na raka shi zance kafin ya karasa tuni fara'a da take fuskata ta gushe nace shikenan sai yace ai nasan kinsan a gidan alhaji ado an bashi yarinya wai kyauta kuma abin haushi bai yi musu ba ban san me nake ji ba ba zan iya gane irin yanayin dana tsinci kaina ba hawaye ne ya fara biyo fuskata na juya dan kar ya gane nace ina zuwa,

www.abbagana.pun.bz
[12/1, 12:46 PM] Ábbä~Gåñāl: KAUNA CE SILA 37

MUHD-ABBA~GANA


da gudu na shiga bandaki da muke alwala ina shiga wani kuka ya zo min mai karfi nayi kamar minti biyar na fito bayan na wanke fuskata da kyar na iya karasa wannan wakar ta biyu ni dai kawai yi nake duk da nasan me nake fada amma muryata kamar mara lafiya haka na gama lokacin da na fito ina fitowa muka ci karo da yaya da ma bamu cika gaisawa ba amma nasan zai yi mamakin irin yanda yaga fuskata kamar ban taba fara,a ba waje naje na tsaya sai ga asma u tace me kike yi anan nace bbu komai tafiya ma nake son yi nace da wuri haka nace mata E tace to jakata na koma na dauko a ciki yana zaune ko kallon inda yake ban yi ba ina hanya ina hawaye sai kawai na fara rubuta masa text BAMU DA BBAN GIDA DA ZAMU GAYYACE KA HAR ACE MAKA AN BAKA NI IYAYENA BASU DA SAN ZUIYAR DA ZASU SIYE MIN SOYAYYARKA KA DAN DA MA NI KADAI NA SANKA
yana gani ya rubuto min amsa wai ina ina ne? nace masa ina hanyar gida sai yace shi kenan wani takaici ne ya tsaya min wato ba abin da zaice kenan haka dai har na karasa gida ina ta tunanin abin da ya dace dani bayan an idar da sallar magariba sai ga sakon yaya yana tambayata me nake nufi da sakon dana turo masa sai nace masa ashe ya aka baka a gidani su hajiya shi yasa baka sona ce komai akan su ba komai muma Allah yana sonmu ni gwara ma ni nafi jin tausayin zakiyya ita da aka dade da ita sai ya min wani sako cewa ya isa haka ina karantawa naji kamar ma zugani yake nan kuwa nayi ta tura masa sakonni kuma duk na bakaken magana ne saboda ranar raina ya baci matuka can sai ya turo min.

www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

  1. muhseen aka. Pr¡nc€~ch@rm¡ng16 December 2015 at 09:22

    yar uwa akodayaushe kadakirika tsayawa kollon ruwa sai kwado yaimaki kafa baki masan lokacin ba.anawa tunanin kinema saurayi ki aure don kare mutuncin kanki .domin gadukkan alamu wannan yayan naki bata naki yakeyi ba.09037644916

    ReplyDelete
  2. muhseen aka. Pr¡nc€~ch@rm¡ng16 December 2015 at 09:25

    yar uwa akodayaushe kadakirika tsayawa kollon ruwa sai kwado yaimaki kafa baki masan lokacin ba.anawa tunanin kinema saurayi ki aure don kare mutuncin kanki .domin gadukkan alamu wannan yayan naki bata naki yakeyi ba.09037644916

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive