shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 16 December 2015

KAUNA CE SILA****2***18-19 & 20

kauna-ce-sila.jpg

[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: KAUNA CE SILA 2---18






MUHD-ABBA~GANA






SAI nayi dariya na kalleta haka dai na gyara shi da kaina akayi mana hoto da zamu tafi muka zube mata kayan tace kai mun gode sosai ai yaron ne yana da iyaye yanzu zan kira su nace vocal tazo ku gaida gida na gode muka fito muka nufi titi dama wani saurayin husna ne ya kaimu ni suka fara ajiyewa a gida sannan suka wuce da daddare ina idar da sallah isha'i na kiea kira shi nayi ta bashi labarin zuwan mu nace masa yana da kyau kamar ku daya yayi dariya kawai haka dai muka ci gaba da hirarmu har muka yi sallama a gaskiya a yan kwanakin nan mun kara shakuwa ta sirri da yaya dan kusan kullum sai mun yi waya da daddare ga text ba mu daina ba yawanci text din shina fadakarwa ne ko kuma muyi hira ta text din daga gausiwa sai mu ci gaba wani lokaci idan yayi min text kamar shidan yamma zan bashi amsa to daga nan zamu yi tayi har sai goman dare zamuyi sallama na kwanta cike da nishadi wata irin kaunarsa ce take kara ratsa ni kuma duk surutu irin nawa ba xaki taba ji na bawa wani labari ba wayata kuwa ba wanda ya isa ya gani amma hirarshi na kan yi idan naji anyi zancen shi zancen yaya nane idan kuwa muka hadu sai dai mu kalli juna idan ma baki sanmu ba za kice bama magana da shi haka dai abubuwa suka yi ta faruwa wasunna dadi wasu na kishiyarsa muna zaune mu uku da zainab da hauwa muna hira sai naji wayata tayi kara alamar shigowar text kwata kwata ban kawo komai ba ina budewa na fara karantawa a filu text din yayane kamar haka: BAYAN ALLAH DA ANNABINSA,IYAYENSA DA SAHABBANSA JIKOKI DA MATAYENSA DA FIYAYYEN BAYI WANE MUTUM NE CIKIN MAZAJE DA MATAYE MAFI SOYUWA A GAREKI,ina gama karantawa na kalli su hauwa nasan ban fada musu wanda yayi ba amma zasu yi tunanin shine da sun san shi kadai ne wanda zan iya ganin abinshi nayi farin ciki hgaka nan dai nayi shiru ina tunanin amsar bayarwa.






MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: [11/19, 12:45 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 19






MUHD-ABBA~GANA



A DUNIYA BANDA IYAYENA BANDA WANDA NAKE KAUNA SAMA DA KAI,bayan na tura masa shima ya turo min haka dai muka ci gaba da musayar text inda yawanci yana tambayata ne ina bashi amsa sai ya turo cewa yana so muyi magana idan ina da lokaci na ce masa ina hanyar zuwa gida sai dai bayan magariba yace Allah ya kaimu ina da sallar kuwa na fara neman layinshi da ban bari ya kirani ba bayan mun gaisa sai ya fara ce min to wai ke me yasa kike sona nace gaskiya da ban sani ba kawai naji ina kaunarka ne don Allah to daga baya kuma sai iliminka ya kara min kaunarka abin da na sani kenan nace to shi salisu kuma fa? nace ni fa yanzu bana sonshi yace dalili nace shi fa yana kula mata kuma yana sonsu sai naji yace to nice miki akai bana sonsu ne? nace E gaskiya nasan basu dameka ba" nace masa salisu fa har kawata ya taba so ni kuma idan har saurayi zai kula kawata me zanyi da shi yace a'a banda kowa dai yace wallahi ko waye yace lallai yau na tabbatar kina son salisu har da kishi haka nace ba haka bane haka dai muka yi sallama na kashe wayata yin text yanzu tsakanina da yaya abin ya girma domin kusan duk bayan kwana biyu sai yayi min idan baiyi yau ba ta zai yi gobe kuma ko wane lokaci ba shi da takamaiman lokacin yi ire iren text din yanzu sun canja yanzu yafi yi min kamar baitin wakar shi amma da alamun gaisuwa ko kuma ya dan tambaye ni wani abu da yake son ji daga nan sai mu ci gaba da hira mu kan yi kwaya goma a rana idan muka fara na tunatarwar ma bai daina yi ba yakan yi amma bai taba yi min na soyayya ba ganin irin yawan text din da muke yine ya sa na yanke shawarar ware masa wayarsa daban da layin shi daban don shi kadai sabuwar waya na siya kuma mai tsada da kyau ga layi na mtn shima mai kyau don har yafi ainahina layi ns kyau text nayi masa na layin na kuma ce idan zai min text yayi min ta wannan layin yace mai yasa nace shi na warewa layi ya ce to bayan nayi cajin wayar ban kaunan ta ba har washegari da na fita ina fita na kunan wani abin mamaki ashe har yayi min text a layin ina budewa naga shine wani dadi ya rafeni ME YASA JIYA DA KIKA GANNI KIKA GUDU ina karantawa na bashi amsa kamar haka: DA MA TAFIYA ZANYI sai ya kara turo min wani JIYA KIN YI KYAU SOSAI tab na karanta text din nan yafi sau biyar don mamaki nayi kyau yace kawai wani dadi ya rufeni har na rubuta masa NA GODE ASHE ZAKA SA NAYI TA SON KAYAN HAR MA NAJI NA KARA SONSU haka dai muka dan yi mukayi sallama a karshe wannan warewa yaya layin da na yi ya kara jawo shakuwa da wata sabuwar amana tsakaninmu dan yanzu yawan yin text din mu ya karu a yanzu na zama aminiyar yaya da kusan baya boye min komai da ya shafeshi baya shakkar sanar da ni masu kaunarsa haka masu kinsa wzni abin mamaki duk wanda na gane baya kaunarsa nima kuwa na tsaneshi ko waye baran ma idan shi ya fada min haka yan mata nasna masu sonshi na kuma san wa'yanda shine ke sonsu baya shakkan tambayarsa komai dan komai da nake sonji shi nake tambaya a take kuwa zai bani amsa wannan waya tawa babu wanda ya isa ya ganta don kullum tana jaka.





www.abbagana.pun.bz
[11/19, 1:13 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 2---20







MUHD-ABBA~GANA






MUN zana jarrabawar karshe cikin sa'a da taimakon ubangijinmu har mun gama yanzu bana zuwa ko ina sai studio daga nan kuma sai gida bamu dade ba sakamkon mu ya fito muka fara clearance ina yawan shiga makaranta yanzu nafi shiga ranar litini n domin ranar ne zan samu duk malaman da zasu saka min hannu yau ma shiga nayi tun safe na samu malaman bangarenmu amma duk da haka ban gama ba lokacin dan a fito daga bangaren su naga daya saura mintina kadan sai nayi tunanin bara naje gurin da muke cin abinci nayi sallah sai na wuce ina shiga muka gaisa da hajiya kafin nayi alwala hajiya ta zubo min abinci tace na bari na fara ci nace mata to na zauna ban dade da fara ci ba sai na dan kall gefena ashe wasu yan mata ne su uku a zaune a tare suke kallona nima kallesu muka yk musayar murmushi daya kawai na sani a cikinsu da ita muka gaisa suma mum gaisa din shiru ma naga kamar dayar na santa amma na rasa inda na santa kusa da su na kara matsawa dan ina son na tabbatar da tunanina na kalleta nace kin san wani bashir yana waka tayi dariya tace ban sanshi ba kafin na kara magana dayar wadda ita na sani kafin na bar makaranta sai tace dama dai ahmad kika ce mawakinmu a take gabana yayi wata muguwar faduwa domin tunanina ya tabbata zakiyya ce ta yaya sai naji wani gumi ya karyo min na tashi ba shiri dan yin alwala ina fara alwala naji muryar zakiya au dawo na ganeshi bayan na gama alwala sai na kalketa na yi dariya nace a'a kince baki sanshi ba tace A'a na ganeshi nace mata ba kina da kanwa ba sadiya?





www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive