shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 8 December 2015

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA (2)

kyau.jpg

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ
HAILA (2)
5. Azumi:
Bai halatta mai jinin Haila tayi azumi na farilla ko
na nafila, idan tayi kuma bai yiba, saboda haka
zata lissafa azumin da tasha bayan watan ya wuce
saita ramasu.
Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada
zatazo, amma dazarar tazo to ba azumi, dazarar
bata zoba to akwai azumi, koda kinji tafiyarjinin a
jikinki amma bai fitoba to biki fara al'adaba, sai ya
fitane za'a fara lissafi.
6. TABA ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Mai jinin Haila bata taba kasantuwarsa littafi mai
tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma
wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta
daukeshi ta gyara masa wuri.
7. Karatun Alkur'ani:
Mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duk dacewa
wadansu malamai suna ganin ya halatta ta
karantashi daka domin kada ta manta sabanin
dauka.
8. Saduwa:
Baya halatta saduwa da mace tana al'ada, idan
taqi yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana
Haila ba za'ace ta sabawa Allahba hasalima tayi
biyayyane gareshi.
Bai halatta a sadu da mace tana al'adaba harsai
al'adar ta dauke kuma tayi wankan tsarki, koda
al'adar ta dauke amma batayi wankaba to bai
halatta a sadu da itaba harsai tayi wanka.
Ya halatta miji ya taba duk inda yakeso a jikin
matarsa alokacin da take al'ada bayan tayi
kunzugu inbanda daga cikbiyarta zuwa gwiwarta
wannan kan bai halattaba harsai jinin yadauke
kuma tayi wanka.
Hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa
duk da tana al'ada.
9. Tabbatar Da Rashin Tsarki:
Al'ada tana tabbatar da wacce take da ita bata da
tsarki.
10. Wajabta Wanka:
Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar
datayi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan
tsarki ya wajaba akanta.
Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan
tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah yayi mana
jagora ya karba mana ayyukammu.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive