shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 29 December 2015

NA DAINA SO!! 6 & 7

na-daina-so.jpg NA DAINA SO!! 6 Muhd-Abba~Gana Akwai sinadarin sonki a cikin jinin jikina to ina mai kara tabbatar miki da cewa ba zan iya rayuwa idan babu ke ba ki tuna irin halacin da ki kayi min kin so ni a lokacin da kusa kowa ya ki ni kin hasance tare dani bayan da kowa ya guje ni" idan ka tafi yaushe zaka dawo? sai da ya dan yi jim kafin ya bata amsa cikin sassanyar muryarsa kin san yanayin neman aiki akwai wahala ban san takamaimai yadda al'amura za su kasance ba amma ina sa ran yanayin yadda kike yi min addu'a ba dare ba rana Allah zai taimake ni na samu aiki da wuri da yardar Allah ka samu ka gama to Allah ya sa ameen shiru suka dan yi na tsirarin sakanni yanxu tafiya zaka yi ka barni? ta tambaye shi tana mai marairaicewa kamar zata fashe da kuka kafin yayi magana taci gaba da cewa daga yau ni kadai zan ke zuwa rafi na debo ruwa? ni kadai zan ke cin abinci? daga yau ba mai side min hannu idan na gama cin abinci? daga yau bani da abokin wasa? bani da mai yi min tatsuniya? bani da mai yin...... haba mairamu abu da ba jimawa zan yi ba na san a na dade baifi nayi wata daya ba har wata daya! yanzu zaka iya shafe tsawon wata guda ba tare da ka ganni ba? Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/15, 12:22 PM] Âbbã Gäñà: NA DAINA SO 7 Muhd-Abba~Gana ko minti daya ba zan iya yi ba tare da na sa ki a kwayar idona ba amma abin da nake son kara tunasar da ke akwai hoton fuskarki a kowanne shafi na kundin adana hotunan dake cikin tarin shafikan dake binne a kwakwalwata zazzakar muryar ki a ko da yaushe na amsa kuwwa a dodon kunnena domin jikin ki ya jima da narkewa a cikin nawa jikin don haka tafiyar da zan yi zuwa birni zan tafi da kene amma a cikin ruhina yanayin yadda mijin nata ya iya tsara kalamai masu sanyaya zuciya yasa a lokuta da dama tafi tunanin cewa zai iya zama mawaki don ta sha fada masa to amma a can cikin zuciyarta bata fatan mijin nata ya zama mawaki saboda ta san yadda ake ce yan matan birni ke rububin mawaka ina so na tuna maka wani abu tace dashi bayan sun yi sallama mene ne kada ka manta kake shan magungunan ka kamar yadda ka saba nayi miki alkawarin ba zan manta ba kuma ba zan manta da irin yadda a kowanne lokaci kike nuna kulawarki a gareni ba kafin su rabu sai da suka zubar da hawaye har bayan da mota daya shiga ta bar tasha da kusan mintina ashirin mairamu bata bar wajen ba, www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive