BAYANI AKAN WASA
Malam yace:
ﻭﺍﻟﻌﺒﺚ
WAL ABATHU
««fassara»»
Dayin wasa
SHARHI
-------
Asalin wasa haramunne, don haka bai halatta ga
duk wani balagagge musulmi mai hankali yariqi
wasa abin yiba.
Domin UBANGIJI (S.W.T) yafada acikin
SURATUL MU'UMINUN
SHIN KUNA ZATON CEWA MUN HALICCE KUNE
DOMIN WASA ???
KO KUMA KUNA ZATON CEWA BAZAKU DAWO
IZUWA WAJEN MUBA ???
TO KUSANI ALLAH (S.W.T) SARKIN GASKIYA
YAFI KARFIN YA RIQEKU ABABEN WASA, DOMIN
SHI ALLAH NE NA GASKIYA WANDA BABU WANI
ALLAH SAIDAI SHI KADAI, SHINE KUMA
UBANGIJIN AL'ARSHI MAI GIRMA.
Saidai duk da haka malamai sunce shi wasa
yakasu kashi biyu:
Kamar yadda aka rawaito hadisi daga KHALID BN
ZAID (R.A) yadda yake cewa:
Babu wani wasa daya halatta sai wasanni guda
uku sune kamar haka:
1- Wasan da mutum zaiyi da iyalinsa.
2- Wasan da mutum zaiyi domin ya horar da
dokinsa.
3- Harbe-harbe ko guje-guje (tsere) domin koyar
yaqi.
Imam Ahmad da tirmizy da Nasa'I da Hakim suka
rawaito.
Darasi mai zuwa zanci gaba.
Insha Allah.
Allah yabamu ikon yin aiki da abinda muke
karantawa.
gud job gana
ReplyDelete