KAUNA CE SILA**2**26-27-28-29 & 30
[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: [11/24, 7:58 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 28
MUHD-ABBA~GANA
WATA rana ina titi a tsaye zan siyi katin waya sai naga kiran yaya ina dauka naji yana fada ke yanzu haka kike naki aikin nace masa meya faru yace shine ake baki aikin wakar biki a gidan Alhaji ado kikayi musu a farashi mafi kankanta kuma har da cd din nace wallahi ba haka bane waye ya fada maka sai naji kawai ya kashe wayarshi na fara nema amma kememe yaki dagawa kawai sai na kira hajiya aina domin dama ita tq bani dan bikin yarta za a yi tana dagawa nace mata waye ya fadawa ahmad ninayi muku waka sai ta ce wallahi mamaa ban taba wata mu'amala da shi ba don ban sanshi a fuska ba ma amma bari na shiga gida na tambaya ban san abin da ya faru ba sai ta kirani tace min wallahi bata san me yake faruwa ba amma ance mata yana kofar gidan ya kawo wa yayarta wakar bikin da yayi mata itama bayan ta fita na kira ta sai naji shi a gurin yana ce mata kyale ta kawai inaji ta karbi numbarsa nima na kashe wayata gani nayi yana kirana ban daga ba dan naji haushin sosai karin haushin ma hajiya na karbar lambarsa to meye hadin su bayan tana da aure ina ta surutai na har wayata ta yanke har na tashi zan cire kayan jikina dan shirin kwanciya sai wata zuciyar tace gaskiya ko mai yaya yayi miki bai cancanci haka ba ya kira kin ki dagawa bai kamata ba nab na dauki wayata na kira shi yana dagawa sai yace yau ni nake kiranki kina katsewa kuma har da turo min sakon cewa kin yi din tunda na yarda koh? to meye na kirana kuma kawai kiyi yanda kike so ba damuwa na gode sai naji ya kashe wayar sa na tashi kawai na hakura nima dare ya fara yi don goma tayi sai naga hajiya tana kirana sai na ki dagawa sai na kuma jin kira na zata itace ina dubawa naga yaya ne ina dagawa yace ta kira ki kin ki dauka koh?
www.abbagana.pun.bz
[11/25, 7:57 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA29
MUHD-ABBA~GANA
NACE MASA to ya zanyi saiyace ki daga wayar ta idan kuma ban isa ba kiyi san ranki kawai sai na kira layin ta tana dagawa ta fara min bayani ni dai nayi shiru ina saurarenta ashe kiran shi tayi tace ya hada mu gashi naki daga waya ta abin da ya faru shine ita hajiya aina ta sanni tun da dadewa muna mutunci da ita sosai kamar uwardakina nake kallanta tunda ba sa'a ta ba ce bikin yarta ya tashi sai ta ce nayi mata wakar biki kamar uku amma abubuwa sun mata yawa dan Allah nayi mata ragi nace mata to ta biya ni kudin aikina dan ragin da nayi mata ma wallahi dan kadanne bayan ta bani aikin sai yayar ta ta bawa ya ahmad itama yayi mata wakar bikin kenan duk amarya daya zamu yiwa aiki ba tare da kowa ya san an bawa kowa ba na riga shi basu tawa kuma ni uwar amarya ce ta bani aiki kuma ita na kaiwa shi kuma yaya sai ranar da ya kira ni ya kai tashi lokacin da yaje gurin matar sai take ce masa haba ahmad yanzu kai sai yau ita kuwa mamaa vocal tun wancan satin ta kawo kuma tayi mana bata san muna mutunci ba shi kuma yana jin haka shine ya fara min araha waya yana min fada ni kuma abin daya bani haushi nasan bata san a nawa nayi aiki ba dan nasan ita hajiya aina ba zata taba fada ba ni bama wannan ba da ace da gaske a haka nayi ba zan damu ba na gane ta fada masa haka ne dan ta bata masa rai ai kuwa ransa ya baci washegari ban dade da tashi ba sai ga kiran ta bayan mun gaisa sai ta ce min da fatan dai kin huce yanzu ko sai kawai nayi dariya sai tace ai jiya naga ikon Allah amma mamma ahmad saurayinki ne ko nace a'a me kika gani tace naga kin ji haushin dan an fada masa kuma har da kuka shima ba ki ga yanda ransa ya baci ba nan da nan idonsa yayi ja.
www.abbagana.pun.bz
[11/26, 8:58 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 30
MUHD-ABBA~GANA
NACE a"a to Allah ya kyauta nace mata amin mukayi sallama kawai da ita mun dan yi kamar kwana biyu ni da yaya ba wanda ya kula wani amma daga baya muka ci gaba da abin da mukeyi wata rana sai hajiya aina ta kira ni bayan mun gaisa tace min ina ahmad? by abba gana,nace ban san inda yake ba sai tace mamaa ahmad saurayiki ne amma kar ki damu idan ma baya sonki ni zan baki miji nace mata to kawai nayo dariya ban fada masa abin da muka yi ba amma nace masa wai me yasa matar nan ta damu da al"amarina sai yace ai yar uwarmu ce ina kuma ganin mutuncinta sai nace masa to naji bayan kamar wata daya komai ya wuce sai na kira ta ina son ta bani number wayar uwani sai bayan mun gaisa sai tace min ina ahmad sai nace wai me yasa kike tunanin shi saurayina ne ko kuma kike so na soshi sai tace yana da qualities din da duk mace zata so ya zama mijinta nace lallai kam sai tace Allah dai ya zaba abin da yafi alkairi nace ameen tun daga wannan ranar zargi ya darsu a zuciyat kuma na fara tunanin yanke duk wata mu'amala da ita watarana muna yin text dinda muka saba sai ya fara min maganar ta sai nace ai ns tsaneta sai yace naji tsoron Allah me tayi min da zan tsaneta haka to wallahi bara ya fada min idan kaunarsa dole naso ta ita da zuri'ar ta nan take naji wani bakin ciki tare da tsanarta a lokaci guda tace masa lallai kam abin da bai sani ba wata tsana ya ja mata dan a lokacin na goge lanbarta a waya ta amma bai sani ba
www.abbagana.pun.bz
[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: [11/23, 9:16 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 26
MUH'D-ABBA~GANA
KAMAR jira yake ai yana gani ya kuma turo min GASKIYA KE ME WAKA CE KUMA BAKI DA AURE KUMA INA GANINKI A MAKARANTAR MU IN DAI BA ZALUNTATA ZAKIYI BA KI SAURARE NI KI GIRMAMA KALMAR SO KAMAR YADDA KUKE FADA A WAKA,nayi mamakin jin wannan bayanin kenan ya sanni to amma ai bai ce mim ga sunan shi ba wata zuciyar tace kila ma irin mazan nan ne masu cankar abu nayi tsaki ai kuwa sai ga shigowar wani DAN ALLAH KIYI MIN MAGANA,shima dai sharewa nayi sai kuma ga wani sakon yana shigowa ASHE KE AZZALUMA CE MARA TAUSAYI MARA IMANI,ganin wannan yayi matukar bata min rai sai kawai na fara neman kiran nashi sai ya daga nace hello!! hello!! kamar so hudu naji anyi shiru an ki a yi magana sai na kashe na kuma kira wannan ma bai daga ba abin daya bata min rai na share kawai naci gaba da shirin fita gurin aikina bayan sallar azahar dukkanmu mu uku muna zaune a vocal sai nace wa hauwa ara min wayarki na kira wani layi kinga text aka ta min da layin idan na kira ba a magana ta miko min ina kira aka daga sai aka yi shiru da naga haka sai na fara magana na ce dan ALLAH waye ne? meye haka sai kawai na kashe dan rainin hankali kuma wani text din aka kara turo min ALLAH YANA GANI abin ma abin dariya da haushi sai kawai nayi masa wani nace DAN ALLAH KAR KA KARA MIN TEXT DAI BANA SO DAN ALLAH ki sani duk abin da kai shi za'a yi maka ni dai ina sonki dole kema Allah ya jarabace ki da wani watarana ina gamawa ba tura masa E naji na gode amma fa sakon shi na karshe ya dan tsorata ni na dai daure dana samu bai kara turo min ba.
www.abbagana.pun.bz
[11/23, 9:34 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 27
MUH'D-ABBA~GANA
KAMAR kullum yau ma na gama ina shirin tafiya na cewa asma'u bazaki rakani bane tace ni na isa muje muna zuwa inda muke rabuwa sai tace kin san me ya faru nace sai kin fada tace jiya mun sha hirar ki a gidan hajiya nace dake dawa tace da ahmad da abokinsa Dd nace ke amsa'u me kuka ce ai kuwa nan ta fara bani labari ahmad ne yace wai ke dashi kaunar ku daga Allah ne yace ke masoyiyarsa ce ta gaske dan yana ji dake da DD ya tambaye shi yace a haka kamar ba kwa mutunci sai yace haka zaku gani idan ka ganmu zaka ga kamar bamu damu da juna ba to wannan yarinyar kanwata ce ta hakika sai muka ce lallai kam ikon Allah haka dai asma'u tayi ta bani labarin abin daya faru ai kuwa naji dadi tun daga wannan ranar asma'u ta zama kawata sosai dan kusan kullum idan muka hadu sai ta bani labarin wani abu da ya faru akan yaya wani lokacin tayi ta min hirar abin da yake fada idan suna hira koda kuwa bata da alaka da ni idan muna hira na kan ji dadi amma kuma ban taba nunawa asma'u muna yawan text ba don ta sha tambaya ta wayar da nake sakawa a jaka wane layi ne nace mata wani layi ne na wani ta kanyi dariya ta kalleni kawai haka rayuwa tayi ta tafiya komai yana tafiya yanda ya kamata tare kuma daci gsba mai amfani a bangarena da yaya kuwa muna tayi abin da muka saba a kullum kuwa sabuwar shakuwace ke shiga tsakaninmu da fahimtar juna dan ko fada bama yi a wannan lokacin junior da gidan yaya ya cika shekara daya yace nayi masa wakar birthday nace to mutane da yawa sun masa waka amma tawa ma ba laifi tana cikin masu dadi.
www.abbagana.pun.bz
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.