shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 30 December 2015

NA DAINA SO!!***8 & 9

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 8 muhd-Abba~Gana wata kakkafar ajiyar zuciya ta kuma yi bayan da ta kammala tunanin abun da ya faru tun shekaru da dama da suka shude mairamu ta tuna da irin halin kadaici data tsinci rayuwarta a ciki tun bayan da mijinta ya tafi birni ta tuna da irin zulumin da ta shiga bayan da aka shafe tsawon kwanaki siitin bai dawo ba babban abin daya fi tayar mata da hankali tunani data yi na cewar ko mijin nata ya hadu da wani mugun bala'ine toh amma surukarta ce ta yi ta kwamtar mata da hankali bayan shekara guda mahaifiyar mijin nata ta kira ta mairamu wata magana nake si muyi dake kin ga tun bayan tafiyar dan nan yau tsawon shekara guda kenan bai dawo ba bai kuma yi wani aike ba kin ga har wasu abokansa sai da suka je birni nemansa amma ba suji duniyarsa ba kin ga kuma ke yarinya ce bai dace rayuwarki ta ci gaba da da kasancewa cikin wannan yanayin ba kuma kina sane da surutan da jama a ke ta faman yi don haka ina ganin mai zai hana ki mika wuya bori ya hau? mai zai hana ki amincewa a raba auren ki samu wani mijin" bata tanka mata ba kuma bata amince da shawarar ba tsinin kibiyar sabon bakin ciki yayi dirar mikiya a zuciyar mairamu bayan da ta kuma tunawa da wani abu. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz NA DAINA SO 9 Muhd-Abba~Gana abin da ya fi tsaya mata a rai fiye da komai mijinta na sane da cewar lokacin da zai bar ta tana dauke da juna biyu har ta haifi da namiji bai zoba har dan ya kai shekara guda bai taba ganin mahaifinsa ba har yaron ya rasu mahaifinsa bai taba yin ko da aike ba shin mene ne dalilinsa daya sa mijinta zai yi mata haka? shin da gaske ya manta da ratuwarta kamar yadda aka sha fada mata tsanin so da take yi masa ne ya sa ba ta iya ganin laifin mijin natan ba bakon abu bane a kauye miji ya gudu birni ya bar iyalinsa cikin kunci da talauci,don ita kanta mairamu ta sha ganin haka to amma a iya saninta mazajen kan dawo bayan shekara daya ko biyu don haka ita mene ne dalilin da yasa mijinta ba zai dawo ba har sai bayan kusan shekara shida mai ya sa zai yi mata haka? da fada ya dace ta tareshi wata zuciyar ta bata shawarar idan yazo kada ki sakar masa fuska toh shin da wacce irin fuska zai dubeni,wadannan kalamai zai fada min daza su iya sa na manta da halin zulumi na rashin tabbas daya jefa ratuwata na tsawon shekaru wanne irin uzuri zai kawo min da zai gamsar dani? ban samu aiki da wuri ba aiki ne yayi min yawa,kauyen ne yayi min nisa nasan nayi laifi ki yafe min. www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive