shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 5 December 2015

KAUNA CE SILA***57

kauna-ce-sila.jpg

KAUNA CE SILA 57
MUHD-ABBA~GANA
WANI lokacin ma ya ce yanzu muka rabu da yayan naki a wannan lokacin kuma tsakanina da ahmad abin ya fara girma dan a yanzu kusan ko yaushe idan zaiyi aiki sai ya kirani na zo gurin kuma ba lallai da ni za a yi abin ba amma ana fara masa kida zai kira ni ni kuwa ina zuwa zan zauna nayi ta zuba masa surutu duk wanda ya fadi wani abu a kanshi ko yabi ko kishiyarsa sai nace masa kasan wane ko kaji abin da ya ce yakan ce min ba haka bane nan zai hau yi min bayani idan kuwa aka ce hangoshi nayi da gudu zan karasa ina haki, by muhd abba gana a wani lokacin ina zuwa zai dan rage murya yace yau da wa da waye suka yi gulmata ni kuma idan yayi haka kunywa yake bani sai kawai nayi dariya nace babu sai yace shikenan to a yanzu sunan ya ahmad ya tashi daga ya ahmad ya koma yaya dan ko a wayata na canja sunanshi shi sunan bana iya kiran sunan shi ko dana hada da yi din ne sai dai nace yaya a wannan lokacin kuwa mutane sun kara sani a gaba wai in dai ana so a ga bacin raina to a taba ya ahmad wasu kuwa suce sonshi take shi kuwa bai san tana yi ba mutane sun sha zuwa gabana naji ana zancen shi sai bayan na tsaya ina musu bayani sai naga sunyi dariya sunce da ma cewa mukayi bara mu tsokane ki gashi ta nasan mutane wasu tsokana ce kawai amma bana iya yin shuru ba zan taba bari a zageshi ba kuma ina bala'in son naji ana hirarshi a kusa dani.salisu yaci gaba da jinya yana samun sauki nima kuma naci gaba da zuwa dubashi lokaci zuwa lokaci sannan nakan kira shi a waya ina dubashi yau ma daga dubo shi muke muna kokarin hawa benen mu kenan na hango motar yaya sai na ga yana kokarin tsayawa hannunshi na hango yana kira na nan na karasa da sauri tun dana nufo shi naga yana ta kallona ta madubi ina zuwa nace masa ina wuni yace lafiya kinje kuwa kin dubo salisu"?
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
Share:

6 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive