CIKIN BAYANI AKAN HASSADA.
CIKIN BAYANI AKAN HASSADA.
Malam yace:
ﻭﺍﻟﺤﺴﺪ .
WAL HASADU
««fassara»»
Dayin hassada
SHARHI
-------
Abin da ake cewa hassada shine:
Mutum yayi burin ku6ucewar wata ni'ima da Allah
yayiwa wani mutum babu gaira babu dalili saidan
kawai yanayi masa baqin ciki.
To wannan kai tsaye haramunne.
Saboda fadin ubangiji madaukakin sarki acikin
SURATUN NISA'I ayata 54.
KO KUMA SUNA YIWA MUTANE HASSADA NE
AKAN ABIN DA ALLAH YABASU NA FALALA ?
Sannan kuma cikin SURATUL FALAQ ayata 5
INA NEMAN TSARINKA (ALLAH) DAGA SHARRIN
MAI HASSADA IDAN YAYI HASSADAR.
Amma babu laifi idan kaga mutum Allah yabashi
ilimi ko dukiya, yana taimakon Addinin Allah dasu,
kace:
INAMA DAI ACE NIMA INADA ABU KAZA IRIN NA
WANE ?
DA NA TAIMAKI ADDININ ALLAH DASHI KAMAR
YADDA YAKEYI.
Amma shima din idan kaso ni'imar ta kubce daga
wajensa tadawo wajenka to wannan tazama
hassada kai tsaye, kuma baka da lada akan
wannan tunani.
Akwai abubuwa da dama acikin hassada, idan
nasami lokaci zanyi sharhi akanta.
Insha Allah.
Muna rokon Allah ya rabamu da HASSADA.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.