shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 18 December 2015

KAUNA CE SILA**2**46-47-48-49 & 50

kauna-ce-sila.jpg

[12/5, 9:46 PM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA46


MUHD-ABBA~GANA

JIN haka sai nayi saurin barin gurin dan bana san ganinshi yau nayi tafiya ta sai da yamma naji ta kirani ina dagawa sai kuwa ta ce ke wallahi dariya kawai yake wai da gaske kinyi kuka nace eh sai yace Allah sarki kanwata kyale ta kawai karki damu nace mata umnm asma'u ba zaki gane ba nifa nasan da gaske yake amma shi kenan na gode mukayi sallama na kashe wayata wayar da muke tin text na kashe har washegari ina shirin fita sai wani ya kirani naxo na masa amshi amma a tukuntawa ina zuwa na fara kenan sai naji wayata tana kara ina dubawa sai naga lambar yaya naji gabana ya fadi kawai na daure nq daga ina dagawa naji yace kizo ki mana amshi ko ba zaki zo ba nace gani nan kawai na karasa na suri jakata na tafi ina zuwa na ganshi a waje suna magana da wasu ban masa magana ba nayi ciki sai na ciki yace bara na bude miki ki dan masa amshi ne da baiti biyu nace to bai shigo ba har na gama da yasan idan ya shigo ba lallai na iya ba ina gamawa sai asma'u tace bara na zo na baki labari nace ta taho ina jiranki tace ai dazu muna tare ya kiraki cewa yayi wai kina dagawa zai saka kuka yace mamaa niba zan iya rabuwa da ke ba nace to me yasa bai fada din ba sai tace to ba ke bace kina jin shi kawai kika kashe nace asma'u baza ki gane ba amma ba komai Allah ya zaba abinda yafi alkairi tace ameen nan dai muka yi ta yin hira har lokacin tafiyata gida yayi na tafi kawai sai na kunna wayar da muke yi sako to banga amfanin fushin da nake yi ba tunda bai ma san ina yi ba shi mara wayo ma ya maidani dan gashi ko a fuskarshi baya nuna komai gashi banji ana maganar bikin shi ba.

www.abbagana.pun.bz
[12/6, 8:51 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA47

MUHD-ABBA~GANA
RANAR alhamis ne tun a gurin aiki naji wani zazzabi haka dai na karasa na tafi ina zuwa gida kuwa ya rufeni da daddare asma,u ta kirani tace yau baki zo ba nace eh a gurinmu na zauna zazzabi ne ya rufeni yanzu haka ma a cikin bargo nake tace Allah sarki Allah ya baki lafiya nace amin sai da safe washegari sai na tashi jikina babu dadi babu zazzabi amma idan na tashi zanji kamar zan fadi sai ina dafa bango sai na ba zan iya fita ba da yamma har nayi wanka dan na fara jin karfin jikina sai fa kiran asma,u tace min ya jikin nace da sauki tace ga ibrahim nayi dariya nace bashi shima duk a gurin su asma,u yake nayi musu godiya mukayi sallana bayan anyi sallar magariba ina kan sallaya naji shigowar sako nayi murmushi dan nasan ko dai yaya na ne ko kamfani dan bani da wanda yasan layuin ina budewa ai kuwa yaya ne ;: SALAM NAJI ANCE BAKI DA LAFIYA IDAN AURE NANE ZAI KWANTAR DA KE HAR KIYI CUTA TO KI TASHI NA FASA , ina gama karantawa nayi dariya nace yaya kenan kawai sai na fara rubuta masa sako kamar haka: DAMA JIYA NE NAJI SOSAI YAU DA SAUKI AMMA BAN IYA FITA BA BUT YAUNZU ALHAMDULLILAH NAJI SAUKI SOSAI NA GODE, A AI kuwa yana gani ya kara turo min wani kamar haka: AU SHIKENAN DAMA NA ZATA NINE NAJA MIKI RASHIN LAFIYA TUNDA BANI BANE ALLAH YA BAKI LAFIYA YA TASHI KAFADU sai nayi murmushi nace hmmmm! kamar yaya so ne yace shine silar cutata ko to ko da gaske zai iya fasawa saboda ni kawai sai na hau rubuta masa wani sakon

www.abbagana.pun.bz
[12/6, 9:58 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 48


MUHD-ABBA~GANA

GASKIYA ba kai bane amma ka yi contributing sosai dan kusan abin daya kwantar dani kenan sai yace min ai na riga naji kince bani bane saboda haka Allah ya baki lafiya yasa kaffara ce na ce masa ameen bayan kwana biyu na dawo daidai na ci gaba da fita sana,a ta ina kuma yin nishadi na kamar yanda na saba amma fa ina tuno zancen yaya zanji wata mummunar faduwar gaba kuma ina jin tsoron yi masa sako ranar nan na bar gurin aiki ina gida sai ga sakon shi GA BIKI FA YANA TA KARATOWA AMMA BANGA GUDUNMAWARKI KI BA LOKACI YA KUSA banji ji dadi ganin sakon sa ba amma ban isa na nuna ba sai na bashi amsa yaya wai dan Allah da gaske kake auren nan zakayi to maman junior ta amince? sai yace min shi da gaske yake mana kuma matar shi ai ba ita ce mijin ba shine saboda haka zan yi nace masa to Allah ya sanya alkairi ya zabi duk abinda yake so zan masa sai yace waka ma ta isa nace to shikenan bayan mun yi sallama haka na karasa wannan daren dauke da tunane tunane, babu abin da yafi damuna sai yanda mutane zasu yi ta min dariya gashi dai ni ba cewa nake yi soyyaya muke yi ba amma mutane da yawa suna cewa ai ina bala'in sonsa wasu ma cewa suke yi ina sonshi amma bai san ina yi ba to yanzu idan suka ji yayi aure ai wasu a gabana zasu fada a zuci nake wannan zancen a fili nace innalillahi Allah ka yaya min son wannan bawan naka kaji tausayina washegari haka na fita na ganshi ai kuwa muna hada ido na dauke kai na shige ciki ban kuma fitowa ba har sai da lokacin tafiya ta yayi na tafi haka dai a kwanakin muka dinga yin wasan buya dan bana bari ya ganni saboda ina ganin shi zan ji wani sabon sanshi kuma ina ganinshi zan ji hawaye mun kai kamar sati daya a haka watarana sai ya yo min sakon cewa biki nan ya kusa nace masa Allah ya kaimu sai kuma nace bara dai na kira mutumin nan naji wai shin da gaske yake ko dai zolayata yake yine? ban san lokacin dana fara neman layinsa ba ai kuwa ya daga nace dan Allah da gaske kake aure zakayi?

www.abbagana.pun.bz
[12/7, 5:09 PM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 49


MUHD-ABBA~GANA


sai yace au kin dauka wasa ne? to da gaske nake ai ranan ma na hada su da asma,u ta waya sun gaisa hatana ce min wai asma'u tana da hankali nace dan dai waya ne daga nan ban kuma jin meye yake cewa ba dan duk na rikice nayi masa sallama na kashe wayata sai na kira asma'u na fara mata masifa wato har da gaisawa da amaryar yaya koni bance kinyi laifi ba da sai ki fada min ai tace wallahi bi ban san anyi ba wasa yake ni bai hada ni da kowa ta waya ba nace mata shi kenan sai mun hadu tace to nan mukayi sallama muka rabu ina hanya duk hakan ya faru har na karasa gida ina tunanin wannan abin mamakin da haushin ina gida har na kwanta duk da dai ban kwanta da shirin sai da safe ba amma na fara bacci sai naji shigowar sako waya ta na bude dan na karanta DA GASKE HAR YANZU KINA SO NA BAKI LAMBAR AMARYAR TAWA KO KIN FASA? ni ko ina karantawa nace masa ya turo min ina so nan take ya turo min naji wata muguwar fargaba nan nayi sauri na rubuta amarya sai ya ce min kuma wai na kira yanzu sai nace masa sai dai da safe dan har na fara bacci yanzu ma sakon sane ya tasheni ai kuwa sai yace to idan ba zan kira yanzu ba na barshi dan yace mata zan kira ta bance masa komai ba kawai sai na fara neman layin da ya turo min ban taba razana irin haka ba dan muryar mace naji kuma ban taba jin mai kama da muryar ba bare nace nasan mai muryar banji me ta fara cewa ba dan na tafi duniyar tunani sai naji tace ina gajiya ina jinki sai nace mata mamaa ce ban san me ya haddasa min rawar murya ba sai ji nayi tace a ina kika samu lambata.


www.abbagana.pun.bz
[12/7, 5:33 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA50
MUHD-ABBA~GANA


sai nace mata dazun ne a studio naji yaya ahmad yana cewa zai kara aure sai na ce ya bani lambar amaryar na gaida ta sai naji tayi dariya tace Allah sarki na gode kece mai waka mu koh nace mata Eh tace ai nima zaki mana koh dan an kusa wata shekara wata na uku nace mata Allah ya nuna mana nace mata a ina kike ne tace a abuja nake zone 6 nace to na gode tace nima haka muna gamawa wani kuka ya zo min mai karfi nace na shiga uku innallilahi wa inna ilahi rajiun a take na dinga ganin wani duhu kai ni dai ina tunanin kiran sunan Allah da nayi shine ya takaita min abin da nake ji haka ban daina tsiyayar da zazzafen hawaye ba waya ta tana hannuna na fara rubuta masa sako da a yanxu bana sha yin komai ina DAN ALLAH DAN ANNABI DAGA YAU KAR KA KARA SHIGA HARKATA DAN ALLAH ko minti biyu bai yi ba dan yana gani ya turo min sako cikin dimauta ME YA FARU? dan haushin dana karanta ce masa nayi bbu komai kawai bana so kuma da gaske nake ganin haka shi ma sai ya ce min:NAJI IN ALLAH YA YARDA BA ZAN KUMA BA YANZU ZAN GOGE KOMAI DAYA SHAFEKI SANNAN KEMA KAR KI KARA KIRA MIN MATAFA, wani kunci ne naji yaxo min ba bacin raina da yace shima ya rabu da ni ba haushin na kalmar daya fada ta karshe matarsa yace gashi har da bani umarni ko gargadi nayi tsaki kawai na kashe wayata gaba daya washegari na tashi da wata shawara kamar wanda aka bani ita ina cikin bacci dan ina tashi na yanke shawarar na canja layukana gaba daya sai kuma wata zuciyar tace saboda mutum daya zaki daina mu'amala da mutanan arziki wani cewa ta zaiyi a bashi lambar ki kuma kowa ai ita yake da ita nayi ajiyar zuciya nace nasan abin da zanyi shi layin da muke turawa juna sakonni shi zan rufe sannan na siyar da wayar dan ko ganinta bana son yi,


www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive