ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA (1)
Abubuwan Da Basu Halattaba Ga Mai jinin Haila (1)
Anan zan lissafa abubuwan da basu halatta mai
al'ada tayisu ba ko ayi mata.
Wadannan abubuwa ne guda goma zan kawo guda
5 darasi mai zuwa zan kawo ragowar:
1. Sallah
Baya halatta mai al'ada tayi sallar farilla ko nafila,
idan kuma tayi baza'a karba ba sannan kuma tayi
laifi, sannan bayan ta kammala al'adar bazata rama
sallolinba.
2. SAKI:
Baya halatta matar da take al'ada a saketa, wannan
ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka
koda yanason ya saketa to yabari saita kammala
al'ada kafin yasadu da ita sai ya saketa.
Amma idan ya saketa tana jinin Hailar to sakin yayi
amma za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin
bai kai uku ba.
3. Dawafi:
Baya halatta mai al'ada tayi dawafin Ka'abah,
amma zatayi sauran dukkan abinda maniyyaci
yakeyi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana
muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.
4. ZAMA A MASALLACI:
Mace mai Haila bazata zauna a cikin masallaciba,
domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro
dadai sauransu.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Allah saka da alkairi
ReplyDelete