KAUNA CE SILA***2**51-52-53-54 & 55
[12/8, 8:13 AM] Ábbä~GåñāKAUNA CE SILA 51
MUHD-ABBA~GANA
Ai kuwa ina fitowa ban tsaya a wajen mu ba sai gurin su asma'u bayan mun gaisa na shiga bata labarin abubuwan da suka faru na kuma fada mata ni nace kar ya kara kulani sai kuwa ta rike kai sai kuma ta shiga tafa hannu haba mamaa me yasa kikayi haka kin san fa yana sonki kin san halin shi wani irin miskilin mutum ne kuma kowa ya san yanda yake wa yan mata wulakanci wallahi da baya kaunarki da tuni kema kin gane gashi kin san kaf mawakan nan namu mata bbu wadda yake mutuntawa irin ki kuma kema kin yi kuskure meye na cewa ya baki lambar wata bayan kin san zakiji haushi ai ni tunda nasan kana sona bbu ruwa na da wata na katse ta nace asma'u kin gama? tace na gama ai gaskiya nake fada miki na fara magana asma'u abin da yasa na nemi lambar ta saboda ya dameni da zancenta kuma ina so na tabbatar dan yana min wasa da hankali abu na biyu kuma ban so naci gaba da yaudarar kaina ne dan me zan ta batawa kaina lokaci da bata dare bayan kuma ga wata can ya ajiye zai aura ni bance dama ni budurwarsa bace amma me yasa yake nuna kulawar sa a kaina irin yadda saurayi ne ya kamata a ce yana wa budurwarsa sai tace ban gane ba nan kuwa na ciro wayata a cikin jaka na ce mata kinga na nuna mata gurin sako ba tare dana buda ba nace mata ai kin san lambar shi a haka zaki iya ganin su ba tare da kin bude ba ai kuwa tana ganin ta razana tace yanzu mamaa da ma wannan wayar shi ce nayi murmushi nace ni dai ki ga abin da nace miki tace lallai dole ki gigice irin wannan sakonnin haka ai zasu kai dubu nayi dariya nace mata dan Allah asma'u wanda yake min wannan ya ba zan so shi ba? ya ba zan dauka yana sona ba? ya ba zan dauka nafi kowa matsayi a gurinshi ba"
www.abbagana.pun.bz
[12/9, 7:50 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 52
MUHD-ABBA~GANA
TACE gaskiya kam nace ki dauka ma zagina yake a sakon nan ai kudin shine ko bare ma ba haka bane wataran dauka na yake kamar aminiyarsa to fi sabillilahi meye amfanin ci gaba da batawa kaina lokaci tace kin yi gaskiya amma ni bazan baki shawarar ki rabu da shi ba dan idan nice sai na dage na same shi tunda bbu laifi a ciki dan kayi yakin neman abin sonka nace ban gane ba me zanyi da ya wuce wanda nake yi tace addu'a in kina yiki kara dagewa na kalleta nace ban ga amfanin yin addu'ar samun shi ba bayan nasan ba sona yake yi ba zuciyarshi tana gurin wata can sai tace waye ya fada miki haka bayan duk alamomi sun nuna yana sonki kina bani mamaki kamar baki san halin shi ba nayi shiru kawai nace mata ba zan gane ba amma na gode da shawararki tashi ki rakani yau ba zan iya wuni anan ba dan ko ganin fuskarshi bana sonyi tace lallai abin naki babbane muka fito muna fitowa shi kuma yana gyara tsayuwar motarsa na hada rai na kawar da kai muka wuce gurin mu na karasa na nemi wani a kasan mu nace masa wayata zan siyar yace meyasa ga wayar ki mai kyau ga karko nace wata zan canja ai kana da blackberry ko yace eh wacce kike so nace voltouch yace kenan ciko zakiyi nace masa E ya nuna min wata fara mai kyau nace ya bari na gama zan kawo maka yace to ina hawa sama na fara goge sakonni shi ko karantawa bana yi sai da na goge dari takwas da wani abu nayi ajiyar zuciya nace gara na goge dan barin ku ma anan tashin hankaline,
www.abbagana.pun.bz
[12/9, 8:03 AM] ?Ábbä~Gåñā?: KAUNA CE SILA
53
MUHD-ABBA~GANA
NI kuma bana son abin da zai tuno min da shi lokaci da zan tafi gida na bashi wayar tawa nace masa ka ajiye wani sati in Allah ya yarda zan baka cikon yace Allah ya nuna mana nace amin na wuce ina zuwa gida na cire sim na jefa a can kasan akwatina na karshe na ajiye shi anan haka naci gaba da bawa kaina hakuri ina kuma addu'ar Allah ya bani dangana na kuma goge lambar amaryar tashi kamar yanda ya umarta ban kuma tunanin nemansa ba bare nace ina sakarai da sakonsa bayan kamar kwana biyu da misalin takwas da mintina na dare ina zaune sai naga wata lamba tana kirana bayan na daga sai aka cemin ina gajiya maryam ce nace oh ya garin tace lafiya ban ce komai ba sai tace ga ahmad dama ce miki zanyi gashi ku gaisa sai nace to na danyi shiru sai naji maganarsa kamar yana waya sai tace bara dan Allah ya gama waya yakeyi nace mata ki barshi kawai yace na daina kula shi idan ya tafi mayi magana tace mai yasake kuwa bata karasa ba na kashe wayata sai da na fuskanci kamar ya tafi dan sai dana bari goma ta dan gota kadan tana dauka tace min Dan Allah me yasa kika ki yarda kuyi magana dashi sai nace mata bbu komai ka bana so sai tace kin san meye nace mata a,a tace min kin sam ni fa kin taba yiwa sister ta wakar aure kawai ba zan tuna miki bane nace to meye dalili tace nima kawai nace mata to shikenan sai kuma tace min ina so mu hada kai dake mu kula da ahmad tunda nasan kina sonsa,
.
www.abbagana.pun.bz
[12/9, 8:20 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA
54
MUHD-ABBA~GANA
A take naji wani takaici nace mata shi ne ya fada miki ni ke sonshi shi baya sona? sai tace a,a to ai da baya kulaki ya za ayi ki samu lamba ta kawai dai bana so naga mace tana son namiji sosai kuma bata sameshi ba sai nace mata ke ba kya sonshi kenan sai tace a,a ina sonshi amma ba zan bar miki shi ba sai dai ya hada mu nayi saurin tattarar numfashina nace to ni bana sonshi idan ma kina ganin da ina sonshi to yanzu a a sai tace ina da wayanda na sani haka suka yi tayi ni gaskiya ma saboda bacin ran da maryam ta jefa ni bana gane me take cewa sai da tace min kina tare kuwa da ni nace mata E ina jinki sai tace ahmad har fada mukayi yace wai bana kishinsa nace masa ba haka bane abin da dai na sani ahmad yana sona nace mata haka ne Allah ya tabbatar da alkairi tace amin na gode muna gamawa naji wani kuka yazo min tare da haushin shi mai tsanani wato ni ina nan ina kishinshi shi kuma yana can yana son wata in Allah ya yarda ko da zan kwanta ciwone tona hakura dashi in Allah ya yarda saboda takaicin da nake ciki washegari dana fita kawai sai na karbi kudin wayata yace min wadda kika ce kina so fa nace zanzo na siya kamar nan da sati biyu yayi dariya yace Allah ya nuna mana na fita na barshi a nan ranar haka na wuni kamar mara lafiya ina kuma taci gaba da jin haushin shi da muka hadu da asma,u na bata labari ita ma tace min kai kema dan Allah ki daina kiranta nace mata wallahi ita ta kirani da har na goge lambarta amma bbu abinda zai kara hada mu da ita bara na kirata a wayannan kwanaki na bawa kaina hakuri nayi juriya na kuma fuskanci rayuwa duk da bana jin dadin yanayin da muke ciki amma idan ka ganni ba zakace ina cikin damuwa ba,
www.abbagana.pun.bz
[12/10, 7:24 AM] ?Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA?
55
?MUHD-ABBA~GANA?
MUNA yawan haduwa ina yawan zuwa gurin su amma ko da na ganshi ko gaisuwa bata hadamu idan na ganshi sai dai na dauke kai mun kusa kai wata a haka dan munyi kamar kwana ashirin da bakwai wata rana da yamma nayi shirin tafiya gida asma,u ta tashi dan rakani muna fitowa sai muka hango shi zaune a inda suke zama amma yau shi kadaine a zaune sai asma,u ta ce min dan Allah ke kuwa kizo ki gaishe shi ko dazu sai da ya tambaye nikr haba ke kuwa nace mata ba zan jeba gaskiya tace dan Allah fana ce miki nace to muje muna zwa sai asma,u tace masa "farin doki sannu da hutawa sai ya kalle ta yace yawwa nima na san ana ce masa farin doki to amma ban taba kiran shi da haka ba ni kuwa jin ta fadi haka kuma dama dole tayi min nazo na gaida shi sai nima nace farin doki ina wuni sai ya kallleni a razane bai amsa ba naga yana girgiza kai kenan mamakin jin hakan yake daga bakina ganin bashi da niyyar amsawa sai naja hannun asma,u muka tafi muna tafiya muna dariyar abin da yayi ni kuwa ko kadan banji haushin kin amsawar saba duk kuma abin da nayi masa ina gida ina shirin shiga wanka zan kwanta sai naji an yi min text ban kawo komai ba tun da wayata ce ta amfanina da kowa yake kirana ina budewa sai naga lambar yaya nace kai to ya akayi yasan bana amfani da layin dana ware masa sai nace bari dai naga me yace min wai nan na fara karantawa kamar haka: BA SUNANA FARIN DOKI BA KARKI KARA KIRANA DA HAKA KI KIRANANI DA SUNAN DA BABANA YA RADA MIN ,dariya sosai nayi bayan da na gama karantawa na ajiye waya ta na wuce wanka ina tunanin me ya kamata na fada masa ne dana dawo sai na fara rubuta masa.
www.abbagana.pun.bz
nice story, but we are not hear the first story
ReplyDelete