shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 18 December 2015

KAUNA CE SILA***2***56

kauna-ce-sila.jpg

KAUNA CE SILA
56






MUHD-ABBA~GANA





TO ni me zan ce maka sweet heart kake sona ce kome ina tura masa na tayar da sallar shafa'i da wutiri ina cikin yi kuwa sakon shi ya shigo ban duba ba har sai da na gama nayi shirin kwanciya nayi addu'oi na sai na fara karantawa: SUNANA AHMAD BA WANI SWEET HEART TUNDA AIKIN SAN HAKA AKA SAKA MIN bayan na karanta sai nace masa idan kuma ba zan ce ahmad din ba fa sai yace min sai na fadi abin da nake fada dana ce masa naji to dai a wannan dare munyi wa juna sakonni da yawa kamar bamu yi tsawon lokaci ba ma magana ba matsala ta shine son da nake yiwa yaya yayi min illa ba karama ba tunda kome yayi min in har zai kula ni to zam saka jiki da shimuyi yanda muka saba duk da abin yana raina amma yana min sako zan masa idan ma tambaya ta wani abu yayi to kuwa zan bashi amsa daidai da abin da ya tambaya na karbi sabuwar watar da nace a saida min BB ta zamani Allah ya sani makasudin yin wayar shine dan na dinga hira da kawaye na wa,ayanda mukayi garko tare da sauran su dai duk yawancinsu suna yi wasunsu kuma sunyi aure gaskiya a lokacin dasu kawai nake chatting tunda dama yaya ne ya sabar min hira ta waya to yanxu kuma ina sona dan ja baya tunda auren shi zaib yi saboda haka dole ne na koyawa kaina zama ba tare da shi ba kuma juriyar hakuri da rashinsa ranar wata juma,a ina zaune a gurin su yaya muna zaune ana ta hira sai ya shigo yayi sallama aka amsa bai zauna ba ya fita can ya dawo lokacin ina ta danna wayata ya shigo ya dauki abinda zai dauka ya fita ban kuma jin duniyar shi ba har na tafi gida ina alwalar magariba kawai ina shigowa naga yayi min text ina karantawa sai naga yana tambayata meye ya hadani da waya BB sai na ce masa ina chatting ne amma da kawaye na na makaranta nace masa ko babu kyau na daina sai yace a ,a ki daina nima dana taba yi na daina saboda bana so yin hira da sababbin mutane amma zan dawo dayi nima nace masa to nagode mukayi sallama.






www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive