shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 28 December 2015

NA DAINA SO!! 1-2 & 3

na-daina-so.jpg [1/11, 8:28 AM] Âbbã Gäña NA DAINA SO!!! MUHD-ABBA~GANA 09039016969 A kokarin na gamsuwa da kwalliyar data yi mairamu ta dubi mudubi a karo na barkatai rabon ta yi kwalliya irin wannan har ta manta kwalliyar yau ta musamman ce domin kuwa a yau take sa ran haduwa da mijinta mutumin da aka shafe tsawon shekaru shida ba tare da taji duniyarsa ba miramu doguwa ce baka siririya ma'abociyar do guwar kyakkyawar fuska mai albarka ce da siririn dogon hanci matsakaicin baki,madaidaitan idanu da a da yaushe ke yunkurin tonawa kyawunta asiri.da wahala mutum ya iya fadin shekarunta na haihuwa kyan dirin jikinta zai iya sa mutum yayi tsammamin budurwace duk kuwa da cewar kusan shekarunta takwas da yin aure.fiye da awanni uku ta shafe yau tana kintsawa har kitso na musamman taje aka yi mata baya ga rangada mata kunshi da aka yi a hannaye da kafafuwa sau uku tana sauya tufafin ta gamsu da wata shudiyar atamfa riga da zani ta yanke wannan shawarar ne bayan da tayi la'akari da cewa a sanin da ta yiwa mijinta kafin ya tafi birni yana matukar sha'awar ya ganta cikin shudeyen tufafi tana fatan har yanzu yana nan da wannan ra'ayin nasa. MUHD-ABBA~GANA www.abbagana.pun.bz [11/11, 8:40 AM] Âbbã Gäñà: NA DAINA SO 2 MUHD-ABBA~GANA KUSAN rabin wata kwalba na tirare ta karar a jikinta sannan ta tukaka ko'ina da ina na cikin gidan da tiraren wuta ko'ina sai kamshi ne ke tashi gwanin ban sha'awa,dama tun da sassafe ta gama share gidan bayan data wanke bandaki,abinci na musamman ta girka masa sannan ta dama masa fura kasancewar shi mutum ne ma'abocin son shan fura, SHIN WANNE IRIN MURMUSHI YA DACE NA YI MASA? ta tambayi kanta yayin da take kallon sirrin mudubin da ke cikin faffadan dakin "abin da ke kara armashi son ki a zuciyata baya ga iya girki shine kin kware wajen iyayin murmushin satar zuciya ganin murmushinki kan mantar da ni cewa akwai wani abu mai suna bakin ciki a duniya....." akwai shafi guda na murmushinki a cikin kundin dake zuciyata tunawa tayi da ire-iren dadadan kalaman daya sha fada mata game da murmushinta kafin ta kawar da kanta ga barin kallon madubi sai da tayi murmushi gadon dake kuryar dakin ta kalla yaushe rabon ta gyara gado haka? ga mamakinta sai taji wata kunya na neman lillibe ta sai data dubi agogon dake manne a bango kafin ta fice daga dakin. MUHD-ABBA~GANA www.abbagana.pun.bz [11/12, 8:34 AM] Âbbã Gäñà NA DAINA SO 3 Muhd-Abba~Gana GARA ki yarda a je liman ya raba auren nan ko kya samu ki auri wani amma wannan mijin naki ya jima da mantawa dake inji kanwar mahaifiyarta kina sa ran zai dawo kauyen nan bayan yaje yaji dadin birni? inji wani kawun ta wanne irin sihiri yayi miki haka? wata tsohuwa ta taba tambayarta ba mamaki ma yaga wata wacce tafi ki kyau a can inji wata kawarta wacce irin tafiya ce wannan? ko aike bai taba yi ba cewar wani malami wai shin kina da tabbas din cewa yana raye? wani ya taba tambayata, miramu tayi ajiyar zuciya bayan da ta tuna da ire-iren maganganun da aka sha fada mata don ganin ta sauya ra'ayi a kan mijinta ta tuna da irin tsangwamar data sha fuskanta daga dangi saboda kin amincewa data yi a raba aurenta da mutumin da ya tafi birni ya barta ta tuna da irin rarrashin da tsofaffi da dama suka sha yi mata akan ta hakura ta fuskanci wata sabuwar rayuwar ta tuna da ire-iren shawarwarin da kawaye da dama suka sha bata a lokuta daban-daban duk dai a kokarinsu na ganin ta manta da mijin da suke ganin ya rabu da ita kuma ba zai dawo ba har abada duk watsi tayi dasu tana ji a jikinta cewa ko ba dade ko ba jima mijinta zai dawo gida don haka ba zata ci amanarsa ba ko da zai kara shekaru goma nan gaba. www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive