AL'AMARIN~ZUCI 21----------------25
[10:21PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
21 Jawota yayi, ya rungumeta yana dan bubbuga bayanta,alamar rarrashi,har saida ya tabbatar ta sauko sannan ya sake tambayar ta,nan take cemishi daddy yace inzo ka kaini wurin shan ice cream.
Har yanzu shan ice cream na nan baki daina ba ko? ya dan lakuci hancinta yana murmushi ita ma haka, sannan yace "jeki shiryo ki zo mu tafi.
Suna hanyar su ta dawowa ne take tambayar sa"yaya ni meyasa ba'a bari ina driving da kaina? kibari idan kika gama secondry school sai ki fara driving da kanki kinji,to yayana ai nakusa, domin cikin wannan watan zamu kammala.
To Allah ya kaimu,Amin,
yaya yaushe zaka koma ne? sai bayan wata daya' amma kamar yayi yawa,a yadda kasa ba zuwa, eh haka ne ina son in huta da yawa ne...right! ni kuma sai in ganka da yawa kenan shiyasa nake kara jin sonki a cikin zuciyata mimi har nake tunanin bazan iya rayuwa bake ba...nima haka yayana i love you so much more
Written by Bilkeesu giro
[10:21PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
22 Mimi!!tashi baccin ya isa haka kinsan yau ranar family meeting ne,ina so mu karasa aikin mu cikin lokaci,to mommy.
Dayake duk za'ayi family meeting kowa da kalar abincin da zai kai, bayan angama meeting kowa shi zai dibi abincin son ransa, suna masu ci cikin zumunci da yarda da kuma aminci.
Kowa ya hallara a babban falo, Alhaji Hassan shi ne ya bude taro da addu'a,Alhaji ne, ya tashi yana cewa "dama yau rana ce wacce muke tattaunawa akan abubuwa da dama ciki harda warware matsalolin mu da suka shafi wannan family, sai dai yau Alhamdlillahi babu matsala ko daya inshaAllah fa ce alheri da na zo muku dashi.
Alherin shi ne za'a sa ranar daurin auren Mimi da faruk,wadan da dama kowa yasan suna son juna sosai da sosai.
Duk da haka nasan zaku yi mamaki sosai saboda ba wanda ya kawo auren su kusa,nima a daren jiya nayi wannan tunani ya kamata a yi auren nan kafin faruk ya tafi tunda Mimi ce yake jira kuma ta kare karatun ta, na secondry, in yaso idan mijin ta ya amince ta ci gaba da karatu, sai taci gaba.
Gaba ki daya falon yayi tsit kowa na saka abu a cikin zuciyar sa kuma da alama abin yayi matukar yi musu dadi,akasin faruk wanda tun lokacin da aka fara zancen zufa ke karyo masa har yanzu.
Ko meye dalili oho,muje zuwa........
Written by Bilkeesu giro
[10:21PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCI lNa Bilky giro
23Ina fatan wannan hukunci da na yanke yayi?gaba dai falon ya dauka sai cewa suke"yayi gsky hakan yayi daidai Allah ya tabbatar da alheri.Amin
Ko akwai mai magana a cikin masoyan?cewar Alhj hassan.Eh Abba, faruk ne ya furta hakan tare da mikewa tsaye,fadi maganar ka muna jinka.
Don Allah famly kuyi hakuri da abinda zai fito bakina musamman ma Alhj da Mimi nasan zaku fi kowa jin haushi da kuma mamaki akan abin da zan fada.
Alhj inaso ayi hkr a janye aure na da Mimi....saboda me! alhaj hassan ne cikin kakkausar murya yake magana, faruk kana da hankali kuwa?meye dalilinka.....Abba wlh bana son Mimi.....INNaLILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN falon ne ya dauka da hakan sai da kowa ya mike saboda tsananin mamaki akasin mimi wacce ko mikewa ta kasayi tana nan zaune kamar gunki,idanunta na kan faruk ko kiftawa basayi
saboda tsananin mamaki.
Written by Bilkeesu giro
[10:22PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCI iNa Bilky giro
24Tas!!Tas!!Tas!!kake ji Abba ya wanke faruk da mari uku masu kyau cikin tsananin bacin rai...ka ga kyale shi haka, faruk fada muna dalilinka na cewa baka son Mimi,alhj nima haka na sami kaina da bana son Mimi a cikin 'yan kwanakinan nayi duk yadda zanyi in maida son yaki amma wlh ina son Mimi abaya shiyasa banaso ayi auren nan nasan wahala kawai zatayi.....Hauka! to bari kaji in gaya maka aure ba makawa sai anyi in yaso ka kasheta, dan rainin hankili..a'a alhj hassan cewar abban Mimi, baza ayi haka ba tunda baya so shikenan....wlh ba makawa auren nan sai anyishi kuma cikin satin nan inshaAllah.
Kuma ka bace ka bamu wuri,koda abba ya juyo ya ga Mimi zaune shar hawaye na zuba a idonta,kuma har yanzu idanun ta na kan faruk ...Mimi !mimi! Abba ne ke jijjiga ta,ko motsi taki, fa ce hannuta da ta nuna faruk dashi, amma sai ta kasa furta komai ganin sukayi ta zube kasa sumammiya innalillahi wa inna ilaihi raji'un kowa yayi kanta sai yayyafa mata ruwa ake, da kyar suka samu ta farfado aka wuce da ita cikin gida.
Faruk sai kuka yake sosai akan rashin fahimtar sa da ba'ayi ba.Hafiz yaja shi zuwa dakinsa.
Hafiz wlh na kasa gane wannan al'amari da zuciya ta tazo min dashi...... sai kuma wani irin kuka ya kwace masa.
Written by Bilkeesu giro
[10:22PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky gir
25Hafiz nasan yanzu Mimi zata yi tunanin na cuceta....to kai meyasa baka bar abin a ranka ba watakil ko son zai dawo bayan anyi aure, hafiz bana tunanin haka,kuma bana so kyautawa ta da Mimi ya dawo rashin kyautatawa, domin idan na aureta a cikin rashin sonnan bansan mai zai faru ba,ban taba tunani cewa soyayya ta da Mimi zata dawo hakaba,faruk addu'a ya kamata kayi domin wannan al'amari na zuciyar ka yana da ban tsoro da al'ajabi.
Mommy, yaya ya cuceni, yayi min ilar da har in mutu bazan mantaba,me nayi maka da zaka min haka.. ashe da gaske ne cewar zainab namiji ba dan goyo bane,mommy yaya yasa na tsani maza a duniya, Allah ya...kul!! kar ki kuskura ki kara tunanin furta wanna mummunar Kalmar....wayyo Allah mommy na yazan da raina.... wani irin kuka ya kwace mata mai tsanani.
Kiyi hakuri Mimi dama haka rayuwa take soyayya na zama ki,haka kuma ki kan koma so kiyi hkr kinji, ki rungumi kaddara,tajawota jikinta ta rungume, tana mai kara rarrashin ta.
Faruk baka kyauta wa family din nan ba,faruk me ya hada ka da mimi da har zakayi wannan furucin da ba Mimi kadai taji zafinsa ba.
Umma wlh mimi bata min komai ba kawai haka naji a zuciyata bana sonta.....da kin kyale dan iskan yaron nan marar mutunci, wanda hankalinsa kadai ake gani amma baya dashi...a'a Alhj kada zafin zuciya ya debeka kayi wa yaron nan baki.
Written by Bilkeesu giro
Dan allah acigaba
ReplyDelete