shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 16 October 2015

DAN******ALHAJI-33

dan-alhaji.jpg

DAN ALHAJI 33








Muhd-Abba~Gana




cikin zafin nama yayi kan malam nasiru ya ce kan har ka isa ka zo har gidana kaci min mutunci hajiya bilki data shigo taga Allah yayi kan mallam nasiru ta shiga tsakanin su da sauri shi ko nasiru ko zagesu Alhaji yaci gaba da fada sai naga wanda ya tsaya maka a garin nan ko wayene wallahi baka isa ka jada niba kawai talauchi yana damunka zaka zo kayiwa mutane hauka ga kanan babban mahaukaci kana ganin yata ko ta rasa wanda zata aura zata auri dan kane? zan bari ta saurareshi ne kaine baka isa da danka ba amma nina isa da yata banza shashasha banZa, ya ringafizgewa yana ki bar nina nuna masa matsayina ta juya tace da mallam nasiru dan Allhah fita kayi tafiyarka kayi hakuri ya fita yana cwa da kin bar shi ya dau raina tunda bani da galihu ta zaunar da shi tace kaga abinda nake gaya maka ka barshi ya auri wacce yake so kaga yanzu ya jawowa mutane abim kunya yace au ke kin yarda shi yayi mata? kunya kuma su suka ji tunda ba a jikin sa cikin yake ba duk abinda namiji yayi adone kuma sai na dau mataki a kansa zai sa yazo har gida yaci mutunci na sai na sa an daure shi ya raina kansa hajiya bilki tace haba yallabai a cuce shi a hana shi kuka kasan fa duk abinda ya fada gaskiya ne kawai dan bashi da kudi a danne masa hakki, a fussace yace ke tunda kina da kudi basai ki tsaya masa ba wannan ai maganar banza ce kina ganin abinda mutum nan yayi min ya nuna kudi a kaaa an yaya gasu gutsi gutsi baza su taba moruwaba tace ai bai rama ba na riga na cuceshu ya harzuka yace walllahi ran ki zai baci saboda tashi ki ban waje ya sake daka mata tsawa ta mike ta fice ya zauna yana ta kunfar baki yana hada gumi yana ganin tunda yake bawanda ya taba ci masa mutunci irin wannan zaune suke a majalisa suna ta shewa duniya tayi musu dadi mallam nasiru ya hango dan marakin zuciyarsa ta kuma yi masa zafi tafiya yake kamar zai fadi har ya karaso kusa da inda suke ya tsaya jikin wata bishiya da aka sare cikin daga murya yace kai safuwan wainwayo yayi da sauri kiran da yaji kamar daga sama ganin malam nasiru yayi a tsaye yana ganinsa ya taso cikin faduwar gaba haka kawai yaji bugun zuciyarsa yana karuwa.
yana karasowa inda yake ya sunkuya zai gaishe shi yace dakata daga wajen ubanka nake naje dan mu sami masahaal akan abinda kayiwa rufaida har ciki ya samu shine ya nuna min bashi da mutunci kafin ya sake wata magana safuwan yace ya za'ayi kaje wajen sa o shi yayi mata cikin?? malam nasiru yace rashin kunya zakayi min har kana da bakin fadamin wannan maganar yace an fada maka kai kake niyyar zagin ubana to wallahi kar ka yarda ka zagar min uba yace idan na zage shi me zakayi? yace rama masa zanyi uba bai fi U.......kafin ya karasa mallam nasiru ya kai masa mari fau!! yan majalisan ganin haka suka taso da sauri shi ko safuwan ganin haka yana juyowa shima ya kai masa wani wawan mari anan da nan mallam nasiru yayi sauri ya kauce kaucewar da zaiyi yaci tuntube ya fada kan wata reshen bishiya yana fadowa kansa ya fashe kafin wani lokaci mutane sun taru kowa na fadin albarkacin bakinsa



lmuhd-Abba~Gana










www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive