shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-17 18 $ 19

rayuwar-fauziya.jpg

[15:56, 10/26/2015] Bana: 17RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (17) Cigaba 17. A
kwance nake ina tsara txt d'in ban hakuri da km
albishir ga Farouk, saiga nashinan yashigo na
katsar da nawa na karanta nashi kamar hk: "
Madam! Kiyi hkr akan abinda yafaru kuskurene,
danasan Nuraddeen mijin 'yar uwarkine dabanyi
sakaci da harshena ba wajen sarrafa zantuka
marasa kyau akansa, kiyi hkr da yaddar ALLAH
bazan sake kamanta haka agareki ba, sannan
inaso kinemamin izini ga Mama don gabatar da
kaina amatsayin siriki, fatan amincin ubangiji da
kulawarsa abaccinki na wnnn dare" na tabbatar
Fadila ce tafad'a masa komai, amma naji dad'in
yadda yafahimceni km yakeson gabatar da
maganarsa alkcn danake matuqar son hakan,
namaida masa da amsa cikin jindadi da nuna
fahimta. Alhmdllh wata 3 Farouk yace asa duk da
Mama tace ad'an tsaya tukunna bataso yahad'e
mata da haihuwar Fa'iza amma Abba Tijjani yace
baza'a d'aga ba. Acikin satin aka gama komai
za'a maida Fa'iza gidanta babu irin fad'an da
ba'ayi mataba akan kula da miji da kwalliya
tsaftasbd duk ta ajiyesu wai ita me ciki km mara
lfy, jikin be gama sau'ki ba Hajara me aikinta km
tana gida Iyayenta sunce aure zasuyi mata,
hakan yasa Mama tace mukoma tare kafin
asamo mata me aiki sbd girki da gyaran gida,
wllh har cikin zuciyata banso hakan ba don
banga dacewar hakanba, nayi-nayi da Mama
akan abari ta samu sau'ki gaba 1 kafinnan sai
asama mata 'yar aiki amma Mama ta dage wai
ga abinda mijinta yace km Fadila ba abinda zata
tsinana mata shiyasa, abin har yakaita ga 6acin
rai dole tasa na amince muka tafi tare SABON
GIDA.
18RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (18) Cigaba 18.
Bansanar da Farouk ba saida muka koma munyi
waya nake shaida mishi ina gidan Fa'iza sbd
jikinta bai wareba km bata da me aiki, yaji
takaicin hakan amma bashi da yadda zaiyi,
Fauziyya saidai mudinga waya zuwa lkcn da zaki
dawo don bazanzo mutakurawa mara lfy ba keda
kike zaman jinya, sannan ki ri'ke amana kizamo
mai gsky da taka-tsan-tsan da rayuwarki
yagama nasihunsa dftn samun lfyr Fa'iza mukayi
sallama. Nice girki gyaran d'aki da gida gaba
d'aya tare da tarairayar mara lfy kasancewar mai
gidanta inyafita tun safe sai dare nima nafison
hakan don nafi sakewa. Kwana na 4 agidan
Farouk yacemin zaizo muje nagaida Auntynsa
anan 'kasan su Fa'iza sbd ta dage sai ya kaini
amma yace muhad'u awani store nan kusa don
bazai 'karaso gidan ba nace to, nagama komai
kan lkc Fa'iza tace akwai wani 'lace' d'inta riga
da zani sawarta d'aya sabone nasashi nace to,
5:00pm cif na shirya tsaf nayi kwalliyata na
feshe jikina da kayan 'kamshin Fa'iza, nayi kyau
sosaikamar don ni akai kayan zanin ya shefu
kamar siket, ita kanta Fa'izan ta yabamin sosai
da kyan da nayi, nabata magunguna da abinci da
duk abinda zata buqata na wuce cikin sauri sbd
nad'an 6ata lkc km inaso nadawo da wuri sbd
abincin dare, mukaje muka gaisa da matar mai
mutunci da fara'a tahad'omin goma ta arziki,
Farouk ma yahad'o kayan dubiya masu yawa
yace nakawowa Fa'iza yana dubata sauri yake,
yanatamin nasihu akan rayuwa da rikon amana
aduk halin dana tsinci kaina, ya ajiyeni ya wuce
abinsa. Koda nadawo magriba tayi kasancewar
bana sallah kai tsaye kitchen na wuce nad'ora
abinci sannan nad'ebi kaya nai sama wajen
Fa'iza, tayi murna sosai da kayan, nayimata
sannu ina tsokanarta akan nabarta ita kad'ai
ALLAH yasa bata damu ba, tana dariya tace ba
abinda nayi wllh na sumbaci goshinta nace
yawwa my patient, naso cire kayan sbd nafi
sakewa nayi girki amma Fa'iza tace nabari kawai
in nagama girkin nacire nayi wanka gaba d'aya
nace to. Abin tsautsayi da 'kaddara ina falon
'kasa azaune ina kallosbd inason abincin yagama
gaba d'aya nakai musu sama na ajiye na huta,
inzan kwanta nake sakkowa 'kasa ko in
Nuraddeen yadawo don ad'akunan falon 'kasa
nake kwana amma in nagama komai sama nake
komawa tun safe zuwa lkcn bacci, kamar wasa
naji ana buga 'kofa banji 'karar motaba km idan
Nuraddeen ne kai tsaye zai bud'e nasan tunda
mutum yazonan kofar falo me gadi ne yabud'e
masa gate, sai nayi tunani ko ma'kwaftane
sukazo duba Fa'iza, 'karar su ac da inji duk be
bari najiyo muryar da take buga 'kofa ba koba
'karama wannan kofar baka jiyo komai awaje in
aka rufe, mayafina yana sama babu abinda zan
rufe jikina akusa bugun da ake yasa kai tsaye
naje nabud'e 'kofar don nasan mawuyacine
namiji yazo gidannan awnnn lkcn, kai tsaye naja
'kofar ina yun'kurin tambayar waye? Alkc guda
numfashina yatsaya cak ganin wanda yake tsaye
km ya dabaibayeni tun daga sama har 'kasa da
wani irin mayataccen kallo lkc guda yai ajiyar
zuciya, tare da cafko hannuna ya had'a jikinsa da
nawa yana kiran My wife I luv u! Da wani irin
sautin murya....
[15:56, 10/26/2015] 19RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (19) Cigaba 19.
Ilahirin zuciyata da dukkan ga66aina rawa suke,
rikon da yayimin shiya hanani 'kwatar kaina da
yun'kurin 'karfina, muryata tana rawa nace
"Nuraddeen meye haka? Fauziyyace fa don
ALLAH kasakeni....! Amadadin ya sakeni sai ya
kawo bakinsa ya rufe nawa dashi numfashina
yatsaya cak alkcn danaji zirarowar hannunsa
cikin rigata wanda yabashi damar zugeta da
'karfin tsiya, ya tattarani ya ri'ke innalillahi
wa'inna ilaihirraji'un zuciyata take ta faman
fad'i, cikin gigita da tsananin 'karfi na fizge kaina
alkcn danaji yana yun'kurin d'aukata wanda
nasan makomar zancen, da gudu nayi baya cikin
tashin hankali da galabaita narasa ina zanyi rigar
jikina ta zare tafad'i 'kasa wanda yasake
bayyana surar jikina 'karara, ihu na 'kwalla alkcn
danaga ya tunkaroni yana sarrafa wata muguwar
dariya daga bakinsa, shikanshi ya tsorata da
ihun amma dake shed'anine be gudu ba, ni kuwa
da gudu nakai 'kafafuna d'akin dayake kusa
dana kwana na, kasancewar shine afarko kafin
wanda nake kwana nadatse 'kofar lkc guda na
silale jikin 'kofar ina mai zubar da hawaye, nakai
tsahon lkc ina jikin 'kofar ina kuka daga bisani
nami'ke jikina yana rawa na kunce zanin jikina
najashi saman 'kirjina, na fad'a kan gado ina rero
kuka cikin takaici da bakin cikin wnnn abu,
mamaki da ba'kin ciki su suka samu gurbi
azuciyata suka rikitar da duk wani tunani nawa,
dana sani d'akina nashiga kodan nasamu suturar
suturce jikina amma bani da ikon komawa
d'akina awnnn halin gwara na kwana anan, na
zauna kan gadon ina zubar hawaye tare da
addu'o'i kala-kala akan ALLAH yatseratar dani
daga sharrin Nuraddeen har wajen 1:00am idona
biyu nakashe fitilar d'akin nazare mukullan
d'akin nashiga bargo ina sake rero wani sabon
kukan. Bansan menayiba baccine yasaceni ko
kuwa tsabagen tashin hankali da rud'une,
Nuraddeen natsinta atsaye akaina yad'ora
'kafarsa d'aya agefen gadon daga gabana,
Hasbunallahu wani'imal wakil cikin sauri na
maida kaina cikin bargo ina addu'ar ALLAH yasa
mafarki nake... FAUZIYYA wnnn shine'karshen
gudun naki? Ga wayarkinan anata kira kinbarta
afalo, wani marar mutunci dana tabbatar da
koshi waye shiya kiraki, km nasan shi yake da
hannu abada gudunmawa wajen rabani da
matata, ya fizge bargon da 'karfinsa alkc guda
ya kunna fitilar d'akin, duk wanda yaganni
yatabbatar d'ayan 2 ya faru kona mutu ko km
jinin jikina ya'kare, amma ba d'ayan biyu
tsabagen tsagwaron tsoro da firgicine,
Nu..rad..deen ka rufamin asiri don martabar
ALLAH da Annabinsa karka ketamin haddi.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive