shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-7

rayuwar-fauziya.jpg

7RAYUWAR (FAUZIYYA) Part(7)
Dukkan wahalhalu da wulakanci da cin mutunci
nafuskancesu iri-iri don sunfi 'karfin na fad'esu.
Wata irin rayuwa Fa'iza ta d'orawa kanta ta
'karya da harka da manyan samari masu kud'i,
hakan yasa Fadila tafara kwaikwayonta har tana
'kokarin nuna mata ita ta fita, kai har takai
tsakaninsu suna kaffa kaffa da wayoyin juna, sbd
sunfara 'kwacewa juna samari, musamman
Fadila Idonta yabud'e sosai da wayewar zamani
kwarkwasa iya taku son kud'i da tsananin
yaudara duk ta iyasu. Nidai ido ne nawa wata
rana muna zaune afalo tare da Almajirin gidanmu
yanata kod'a Fa'iza Matar Manya kamar yadda
yasaba idan yanason kud'i sbd yazama kamar
d'angida, cikin 'kasaita take magana tana bashi
amsa mai d'auke da saqon dazai iso gareni, " ai
wllh ni matar manyace mutumin daya amsa
sunan me kud'i aduniya shizan aura, ai baka
saniba jiya nayi gamo da wani mugun mai kud'in
da ake ji dashi a'kasar nan, haba Aunty wayeshi
haka? Almajirin ya tambaya yana ri'ke baki,
"Hmmm zan fad'amaka ba yanzu ba sbd
kasanmahassada kunensu yana tare da mu" ta ja
'kafa tana girgiza jiki ta fice, azuciyata nace
yarinya ALLAH yataimaka duniya ce. Mama
tadaina tsawatar musu kwata kwata sbd suna
sammata kud'in samarin, dubunnai suke shigowa
dashi duk sanda suka fita hira, tun sunayi
a'kofar gida acikin mota har takai saidai
ad'aukesu ayi gaba, abin yana matuqar 6atamin
rai don mutuncin Abba suke zubarwa km wasu
basa tantance Fauziyya da Fa'iza sai ayi tunanin
nice. Misalin 8pm na idar da sallah ina addu'o'i
Fa'iza ta leko tace Fauziyya inkingama Mama
tana kiranki tana d'akinta nace to, nabita muka
tafi nayi sallama natsuguna nace Mama gani
zuciyata tanata tunanin wane laifi tayi, Fauziyya
mama ta kira sunana cikin nutsuwa, na amsa
kaina a'kasa kamar wadda tai laifi kasancewar
nasan kirana baya wuce na laifi, Saurayin Fa'iza
yace yanaso ta koma makaranta sbd haka
yabada rabin kud'in kuma zai nema mata poly...
Zuciyata ta harba da 'karfi wllh da nasan wnnn
ne kiran bazanzo ba, don wulakanci saurayine zai
biya mata kud'inmakaranta? Nayi saurin 'kakalo
murmushin ya'ke nace Mama ALLAH yasanya
alkhairi na kalli Fa'iza da ta hakimce akan gado
nace Fa'iza ina tayaki Murna, idan nanuna rashin
jindad'ina na shiga uku amma tabbas naji
takaicin hakan... Karki damu Fauziyya kema
ALLAH yakawo miki naki, Mamace tafad'a da
alamun rarrashi, don takaici nafito nabasu waje.
Ina shiga d'aki nafashe da kukan dana rasa
matsayinsa.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive