shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 10 October 2015

DAN******ALHAJI-27

dan-alhaji.jpg

DAN ALHAJI 27







Muhd-Abba~Gana


tana fita ganin sulaiman yasa ya taji wani faduwar gaba ta karasa inda yake suka gaisa duk ta matsu taji halinda safuwan yake ciki yace baki tambayeni mutumin kiba? tace shine abinda nake so ji yace to mutumin an binciko file dinsa ta dafa kirjinta tace bashi da lafiya mai ya same shi? wallahi zazzabi ne mai zafi ya kamashi ko abinci baya ci a gaskiya zazzabi bai kama shi da wasa ba shine naga ya dace na zo na sanar da ke dan kar kiji shiru tace hakan yayi kyau na gode shi kuma Allah ya bashi lafiya yana gida ne ko .......? yace a'a suna da likitansu a gida shi yake buba shi gashi bansan gidan su ba inji ta sulainman yace gidansu ba boyayye bane ko kuma kar na baki wahala kawai ki gaya min ranar da zaki sai na zo mu tafi tsaya na baki lambata idan kina da bukatar hakan sai ki neme ni tace ba damuwa in haka ta taso na neme ka sukayi sallama ta shige gida ta sanar da ummin ta safuwan bashi da lafiya sosai shine abokinsa yazo ya gaya mata habiba tace aiya shi yasa kwana biyu baya zuwa Allah ya bashi lafiya tace ummi dan Allah ki barni naje na duba shi tace kin san dai bazan mu tunkari abbanki da wannan maganar ba ta sake sasaauta murya ummi har naje na dawo ba tare da ya sani ba tare da halima abdullahi ta raka ni hakan yayi kyau sai ki shirya ku tafi nan da nan ta shirya cikin wani leshi madan karen kyau gashi ta tsara kwalliya mai daukar hankali tayi kyau sosai abinka da kyakywa ta sake tsokano shi ita da kanta da ta duba madubi sai data firgita gashi kayn fitet ne ta dauko mayafi ta yafa tana fitowa umminta tace baza ki tafi a haka ba ita kanta kyaun rufaida ya firgita ta duk dacewa kamar su daya sai dai ta fita haske.





Muhd-Abba~Gana



www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive