shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 22 October 2015

SIYAMA***8-9-10-11 & 12

siyama.jpg

8siyama

Tana zaune akan gadonta sakeena ta kirata suka sha hira anan take bata lbrn irin zaman da sukeyi da ya naseem sakeena tayi dariya sannan tace haba siyama sekace ba mace ba aike zaki jawo hankalinsa tace sakeena kinfi kowa sanin halin ya naseem tayaya zan jawo hankalinsa tace barikiji daga yau ke zaki fara yimasa girki ko bazai ciba kiyi masa sannan kar kisake kisaka manyan kaya kisa kayanda zasu bayyana surarki a waje sannan kidinga janshi da hira koda bazai kulakiba tace gaskiya sakeena bazan iyaba ya naseem wani irin mutum ne ba irin mutanen da mace take jawo hankalishi bane tace kintaba ganin namijin da bazai juyu ba to ki sani wlh kina zaune wata zata zo ta mallake gidan ba abunda siyama ta tsana irin kishiya tace nagode sis zan gwada tace to ina sauraronki ta kashe wayar ta tashi ta debo wasu shedanun English wears tana tunanin tayadda zata gara ya naseem sannan tayi dariyar mugunta tace ya naseem kashirya domin zaka garu sosai..............


www.abbagana.pun.bz

9siyama

Jinsa tayi ya shiga dakinsa ya kulle kofa da alama abokin nasa yatafi . da safe ta tashi da wuri tayi masa hadadden breakfast ta jera akan dinning sannan ta zauna tana jiransa yana fitowa yaga irin shigar dake jikinsa gabadaya kirjinta a waje yake sannan rigar bata kai gwiwa ba yaga tanata masa murmushi tace yaya ga abincin kazo muci tun dazu nake ta jiranka ya kalleta yace nace kiyi girki dani bazan ci abincinki ba don haka kar ki kara girki dani ya fita ya barta wani bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya ta dauki waya takira sakeena tace sakeena wlh bazan iyaba tace meyafaru tafada mata abunda yafaru tsakaninta da ya naseem sakeena tace hakuri zakiyi siyama ina tabbatar miki ya naseem saiyadawo tafin hannunki siyama tace nagode ta kashe wayar. Abangaren ya naseem kuwa tunda ya fita ba abunda yake tunowa sai surar jikin siyama zuciyarsa tace kodai kafara sonta da karfi yace never bazan taba son siyama ba haka ranar ya wuni yana tunaninta itakuwa dataga lokacin dawowarsa yayi tayi wanka tasa kayan dasuka fi na dazu tayimasa haddadiya jallof din shikafa ta ajiye drinks kala-kala tanajin ya kwankwaso kofa taje ta bude masa tana budewa kuwa ta rungume shi wani abu yaji tundaga kafarsa har cikin kansa sai ya tsinci kansa da kasa tureta daga jikinsa sai da ta dade ajikinsa sannan tace yaya sannu da zuwa kasa magana kawai yayi sbd irin kyan dayaga takara .................


www.abbagana.pun.bz


10 siyama

Gabadaya jikinsa yayi sanyi cikin murya mai sanyi yake magana yace siyama tace na'am yaya yace jeki ki cire kayan dayake jikinki tace yaya mesuka yace kawai ki cire tace to tana shiga daki ta cire kayan ta sako wanda suka fiso haduwa tayi murmushi tace ya naseem manya kadan kafara gani kenan tafito ta tarar dashi a zaune tace ya naseem na chanja ya kalleta yayi shiru tace muje kaci abinci yace banace miki kada ki kara girki daniba taje ta zauna kusa dashi yadda sunajin numfashin juna tace haba yayana nasan kana jin yunwa ka tashi muje kaci abinci kaji yayana takarasa maganar cikin shagwaba sai ya tsinci kanshi da bin abunda tafada suka je suka zauna tayi serving dinsu suka fara ci suna ci yana kallonta takasan ido saida yacinye plate guda tabbas abinci yayi masa dadi yatashi ya nufi dakinsa yana zuwa ya kwanta ya huta amma ina idanunsa siyama suke hango masa zuciyarsa sunan siyama take kira anan ya gane cewa tabbas ya kamu da son siyama son ma bana wasa ba gashi kuma bayaso ta rainashi adaren ranar kasa bacci yayi ba abunda yake tunani sai siyama yatashi yayi sallah ya roki ALLAH yasa siyama ma tana sonshi................


www.abbagana.pun.bz

: 11siyama

Adaren ranar kasa bacci yayi barawon bacci ne dai yadaukeshi da safe yauma kamar kullum ta tashi da wuri tayi wanka tashirya tayimasa girki yana fitowa yau taga sai murmushi yake yimata itama tana tayimasa tace masa ya naseem inatajiranka yau baka fito da wuri ba yace wlh siyama jiya bansamu bacci bane tace meyafaru yace siyama dan ALLAH kiyi hakuri da irin tsanar dana nuna miki wlh yanxu ina mutukar kaunarki tace ya naseem kenan saidai kayi domin siyama bata sonka kuma bazata soka ba har abada ta tashi ta nufi dakin ta barshi da bakin ciki aransa haka yafita aiki ranar kwata-kwata ba walwala afuskarsa itakuwa tana komawa daki ta dau waya takira sakeena tace saky kinsan meyafaru tace a'a sai tabata lbrn yadda sukayi da ya naseem sakeena tace bana fada miki ba to yanxu ke mekika cemasa tace nafada masa abunda yake raina bana sonsa sakeena tace zama kifara sonsa ne haka suka gama tadinsu suka yi sallama ta kashe waya yau da yadawo tayi masa girki ta ajiye masa amma sai tagudu daki ta kwanta shikuma yana dawowa yaga yau bata tareshiba amma tayi masa girki baya so yatakura mata shiyasa ya kyaleta yazauna yaci abincinsa saida sukayi kwana uku suna wasan buya da ita ana ukun ne yana kwance adaki yana tunanin shifa yafara cutuwa da irin wannan zaman don haka dole yaufa yaje ya karbi hakkinsa..................

www.abbagana.pun.bz

12siyama

Tashi yayi yatafi dakinta yana zuwa ya tura kanshi ciki yana shiga saida gabanta yafadi tace ya naseem Lfy yace zo muje dakina batare da shakkar komai ba ta bishi suna zuwa yayi alwala sannan yace itama tashiga tayi alwala tafito yajasu sukayi sallah to anan zance ya canja salo yafara kissing dinta itakuwa anan tafara mishi kuka gashi shikuma baya son kukanta don haka sai ya kyaleta yace siyama bata kulashiba itadai kukanta take ya durkusa yace wlh siyama ina sonki pls kema ki soni shiru tayi masa yace shikenan to ki yarda mudinga kwana daki daya dake sannan kuma ki sake sosai dani tace toh yace yawwa haka suka kwanta ya rungumota ahaka har bacci yadauketa shikuma haka ya kwana yana tunaninta yayi alkawarin idan ALLAH ya yarda bazai mata dole ba harsai ta amince zai cigaba da hakuri itakuwa siyama baccinta takeyi hankalinta kwance washegari da safe sungama breakfast kenan saiga sakeena nan da mijinta da gudu ta tashi taje ta rungumeta suka gaisa da mijin saky sannan suka shige daki nan kuwa suka fara hira anan siyama ta kwashe abunda ke faruwa tafadawa sakeena nan saky tace haba siyama ki tausayawa yaya harfa ya dan rame tace hmm bayanxu ba tace barikiji do the right thing at d right time wlh idan baki sani ba kisani akwai yan matan da suke bin ya naseem amma baya kulasu amma idan kika hanashi abunda ALLAH ya hallata masa dole watarana ya kulasu..................
www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive