shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 16 October 2015

DAN******ALHAJI-38

dan-alhaji.jpg

DAN ALHAJI 38Muhd-Abba~Gana
komai yayi daidai dan tunda abin ya faru ko kare a cikin unguwar ba wanda yaje masa jaje hakan yan uwansa wannan abin ba karamin tayarwa da alhaji muaZzam hankali yayi ba duk sai yaji ya tsanni halayensa yasan shi ya jawa kansa halinsa na wulakanta talakawa ga irinta nan tun daga yanzu hatta yan uwansa sun tsane shi lokaci daya ya gane kuskuransa ga kuma dana sani da yake tayi akan malam nasiru ga shi cikin lokaci kankani ya bar masa duniya gashi ya rataya akan dansa kai! duniya abin tsoro ce daga wannan lokacin yasan lallai ya yarda kaki naka duniya taso shi kaso shi duniya taki shi gashi dai ta faru akan Alhaji muaZzamu ya gani tun kafin aje ko ina duk kowa ya natsu ana sauraron fitowar mai shari'ah waje ya cika makil can tsayin wasu yan mintuna sai ga shi mai shari'a ya fito kowa ya tashi ana fadin kotu ya zauna sannan kowa ya zauna waje yayi tsit ba wanda ya sake ko tari sai can ga wani mai sayar da doya ya doso get din kotun ganin mai gadin baya wajen ya zagaya ya hango mutane da yake babbar kotu ce wajen kotun biyar ce.
www.abbagana.pun.bz

ya fito yana a sayi doya wani mai tsaron kotu number 2 yace ka bar wajen nan ba wajen talla bane mai shari'a ya shigo banza yayi masa yaci gaba da fadin a sayi doya mai shari'a ya daka tsawa yace waye mai mana tallan doya anan wai? yan sanda sukayi kansa da yake mai taurin kai ne sai ya zagaya yaci gaba da tallansa mai shari'a yace aje a shigo da mai doyar nan b bata lokaci suka cika aikin su kafin su shigo dashi ya tsaya zai yimusu taurin kai ya sha kulki kotu mao shari'a yace kai na ce maka nan wajen talla ne kuma ba anje an yi maka magana ba? saboda kai dan taurin kai ne kaki maza ku ajeshi sata daya ya durkusa yace dan Allah yallabai kayi hakuri yace an kara maka sati biyu ya sake cewa wallahi talla na fito ban barwa iyalina na komai ba yace sati uku shigo ku tafi dashi ya tsaya ya sake cewa dan Allah ayi hakuri alkali yasake cewa idan baka shige ka tafi ba in ka sake magana sati hudu
ya sake cewa in kun kulleni yayana da matata zasu shiga damuwa alkali ya sake cewa kar ka kara magana sai ko cewa yayi tunda ka dauke ni ta karkarewa yai ya ringa cewa asai doya! asai doya! asai doya! ba wanda abun bai bawa dariya ba amma ba hali mai shari a ya mike yana cewa ya shiga cember aka yi gaba da mai doya a na ganin mai shari a ya tashi mutane suka shiga dariya har da tsuntsire wa shi kansa alkalin da ya shiga camber fadawa yayi kan kujera yana dariyar mai doya yace lallai wannan dan iskan kauyene bayan komai ya lafa an bar kowa yayi dariyarsa ya gyatsr mai shari a ya sake dawowa yaje yasa akayi tsit aka kira wata shari a sannan sai tasu safuwan lauyan malam nasiru mai suna mustafa dauda sai mai kare safuwan shine ya mike mai suna bala ali aka shigo da safuwan alhaji muazzam rudewa yayi ganin muguwar ramar da dansa yayi bashi ba har sauran mutane da suka san shi sun san yana cikin damuwa mai tsanani mai sharia yace ina safuwan? yace gani yace kotu tana tuhumar ka akan silar mutuwar mallam nasiru da batan yarsa wacce kayiwa fyade kayi mata ciki"

Muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive