Qissar wani mahaukaci mai suna BAHLU wanda yarayu a zamanin sarki HARUNA Ar-RASHEED
Qissar wani mahaukaci mai suna BAHLU wanda
yarayu a zamanin sarki HARUNA Ar-RASHEED
(Abu Ja'afar Bnul Mansoor Al-Khaleefatul
Abbasiy).
Wata rana Bahlul yana zaune abisa kabari, saiga
Sarki Harun Rasheed, zai wuce a bisa doki tare
da masu bashi tsaro, sai sarki Harun ya kalli
Bahlul yace masa:
"Yaa kai Bahlul yaa kai wannan mahaukaci wai
yaushe zakayi hankali ???
Sai Bahlul ya sauka daga kan kabarin, yahau can
kan wata doguwar bishiya, sannan yadaga
muryarsa sosai yana cewa:
"Yaa kai Harun yaa kai wannan mahaukaci
yaushe zakayi hankali ???
Tirqashi in banda mahaukacin da anriga an san
cewar mahaukaci ne, wanene a zamanin ya isa
yadubi Sarki Abu Ja'afar yace masa
mahaukaci ???
Sai sarki Haruna ya zaburi dokinsa yakara
kusantar bishiyar da Bahlul yake akai, yadaga
kansa mai dauke da ado na sarauta, ya kalli
Bahlul a sama a zaune yace masa:
"Yanzu nine mahaukaci lo kuma kai da kake
zaunawa a kan kabari ???
"TIRQASHI"
Sai Bahlul yace:
"ina ai ni inada hankali"
Sai Haruna Ar-rasheed yace masa:
"Tayaya kuwa haka zata kasance ???"
Sai Bahlul yanuna yatsansa zuwa ga gine- ginen
benayen fadar Harun Ar-rasheed.
Yasake bashi amsa da cewa:
"saboda ni nasan wadancan masu karewa ne"
Ya cigaba da cewa:
"Wannan kabarin kuwa shine tabbas, shi yasa na
rayashi, kuma nadawo natare a wajensa, kai
kuwa sai ka ruguza naka kabarin kagina benaye a
duniya, shi yasa baka son zuwa inda naka yake,
kariga ka rusa shi!!!"
Bahlul ya karasa maganarsa da cewa:
"To kafadi mini wanene mahaukacin tsakanin ni
da kai?".
Harun yayi kuka har saida gemunsa yajike da
lema, sa'ar nan yace:
"Wallahi kafadi gaskiya".
Sai yace:
"kara mini wani wa'azin yaa Bahlul".
Sai yace masa:
"Littafin Allah Al-Qur'ani ya isheka wa'azi".
Harun yana jin ya fadi haka sai yace:
"To kana da wata bukata in biya maka ita ?"
Sai Bahlul yace:
"kwaraima kuwa, buqatata guda uku ce"
Bahlul: 1. Kakara mini shekaruna na duniya.
Sarki Harun: Wallahi bazan iyaba.
Bahlul: 2. Ka kareni daga mamayar mala'ikan
mutuwa.
Sarki Harun: Wallahi bazan iyaba.
Bahlul: 3. ka sakani a aljannah ka nisanta ni
daga wuta.
Haruna: Wallahi bazan iyaba.
Sai Bahlul yace masa:
"To wallahi kasani kai kanka abin mulkane, kai
bamai mulki bane, don haka kasani bani da wata
bukata a wajenka.
Tofa kunji mahaukaci mai hikima.
Wanne da darasi kuka dauka acikin wannan Qissa
gameda shugabanninmu na yanzu ???
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.