shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-22-23-24$ 25

rayuwar-fauziya.jpg

[16:19, 10/26/2015] Bana: 22RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (22) Cigaba 22.
Cikin sauri nafad'a band'aki na d'auraye fuskata
nasanya rigata, kaina yayi nauyi sosai hakan
yasa nafara jin hajijiya, nadad'e ina neman
mukulli daga bisani naganshi, tanata bugawa
nakasa ce mata komai zuciyata tana ta sa'ka da
warwarar abinda zata sanar da Fa'iza, haka na
bud'e 'kofar kaina a'kasa jikina sai rawa yake
baqin cikin abinda yafaru da km jikina yanamin
nuni da kamar akwai wata alama dazata bawa
Fa'iza damar ganin abinda ya kusa faruwa
shiyasa nakasa had'a ido da ita, FAUZIYYA! Ta
kira sunana azabure alamar tausayawa, gaba na
yafad'i Hawaye mai zafi yasake kwararowa a
idona, ta kalleni cikin tausayawa tace "jikin ne?"
cikin mamaki nakai dubana gareta kafin na d'aga
kaina alamun eh, "wllh d'azu nuraddeen yake
cewa kin kira wayata tsakar dare kina ta kuka
wai cikinki yana ciwo, yace daya dawoma afalon
'kasa yasamu abincinmu ga dukkan alamu tun
kafin ki kwanta baki da lfy, ta kamo hannuna
muka koma bakin gado yace ya m'iko miki
magani ko? Yanaina kinsha nace eh, muryata
tana rawa wanda dole yasa na fashe da kuka
don baqin ciki da takaici, Dan iska wato har
yasan mezai kitsa mata, "kidubi yadda fuskarki
ta kumbura Fauziyya don ALLAH kidena kukan
haka mana, ko har yanzu jikinne kawai mutafi
asibiti? Fa'iza cikin nawa yayi sau'ki kaina ne ya
takuramin da ciwo, wataqila rashin baccine
amma inaganin idan nad'anyi bacci zai daina,
ALLAH sarki sannu Fauziyya dama kinayin wnnn
ciwon cikin haka? Nace a'a inaganin kawai
chanjin yanayine, tace wayyo ALLAH yabaki lfy,
daga zaman jinya? Na kalleta lkc guda namaida
kaina 'kasa don bana 'kaunar muhad'a ido, nace
Fa'iza inaganin kawai zan koma gida tunda nazo
ciwon cikinnan yake damuna, amaimakon yai
sauki sai ya'karu dabadan da sauran kwanana
ba mutuwa zanyi... Haba Fauziyya don ALLAH
karki kawo maganar tafiya yanzu ban warke ba
wllh kema kinsani, in ALLAH ya yarda kinsamu
lfy don ALLAH karki tafi wllh Nuraddeen bazaiji
dad'in hakan ba, tanata rarrashina har tana
tambayar ya akai nadawo nan d'akin nace
tsoroneda tsabagen ciwo, haka ta tashi tace
"bari ta kawomin maganin ciwon kan, nace to,
ALLAH sarki tana jan 'kafafuwan har yanzu da
sauran ciwon, azuciyata nace wllh saidai kusan
yadda zakuyi yau saina tafi gidanmu ko ta wane
hali. Ina tsugune inda tabarni najiyo muryar
tsinannan akaina, yace "sannu Fauziyya" gabana
yai muguwar fad'uwa amma hakan besa nad'ago
na kalleshiba, duk tunanina shi kad'aine, sai naji
muryar Fa'iza tana cewa "Fauziyya Nuraddeen
yana magana ko jikinne? Na d'ago nasha kunu
nace da sau'ki yana wani tsinannan murmushi,
na kauda kai, ga maganin inji Fa'iza yace ta ci
abinci ne? Tace bari nad'auko mata bata ci ba,
cikin sauri nari'keta nace kibarshi na'koshi, yace
je ki d'auko rabu da ita anta6a ciwo bacin abinci
da daddarema bata ci ba fa inaga, Fa'iza ta
wuce da sauri abinta, Fauziyya karki gangancin
tafiya gida adai-dai wnnn lkcn, yana maganar
'kasa-'kasa tsanarsa ta 'kara shiga raina, na
kalleshi awulaqance nace kai har ka isa kahanani
yin abinda nayi niyya? Wllh saina tafi duk
matakindakaga dama kad'auka maha'inci kawai,
muna maganar Fa'iza tashigo ya cigaba kamar
me rarrashina akan karna tafi, itama Fa'izan tasa
baki haka nadage har ranta yafara 6aci
musamman da taga nafara yiwa Nuraddeen
rashin kunya don nakasa jure yi masa tattausan
kalami, tace Nuraddeen mu rabu da ita taje
nasan bazan mutu ba, wata rana bare yafi d'an
uwa rufama asiri, wllh da ina da 'yar aikina da
na huta.
23RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (23) Cigaba 23.
Haka suka gama rarrashinsu akan nazauna
amma na 'ki, tayi iya yinta akan ko wani laifin
tayimin nace a'a kawai gida zan tafi, 'karshe ta
hakura tabarni wanda na tabbatar rantane ya
6aci, babu irin txt da Nuraddeen be turominba na
barazana da ban haquri amma na sharesu.
Nagama komai nahad'a kayana nai tafiyata ko
sallama ban musu ba tunda nasan suna sama
tare da Nuraddeen km indai nai musu sallama zai
iya cewa zai kaini, saida nashiga mota snnn
natura mata txt akan cewa "tayi hkr natafi dalili
me 'karfi yasani yin hakan, karta zurfafa akan
neman ba'asi ko roqon nakomo gidanta, nayi
mata fatan samun lfy" gaba d'aya abinda yafaru
ina ganinshi tamkar mafarki, zuciyata ta hargitse
ta dagule da tunanin irin wnnn hargitsatstsiyar
rayuwa mara tsarki, nutsuwa, da rashin tausayi,
muna zuwa 'kofar gida gabana ya yanke yafad'i
ganin motar Mama a 'kofar gida, ya ALLAH
kafitar da ni daga tarkon Mama, don nasan bani
da hujjar dazan fad'awa Mama, bazan fad'i gsky
ba donnasan in bata 6are da niba to kuwa zan
jawo wa kaina wani tashin hankalin, tunda
ALLAH be bashi nasaraba kawai nayi shiru da
maganar shi yafi. Ina zura kai cikin gida tare da
kokarin sallama na hango Mama azaune kan
kujera tasha kunu tanata jijjiga 'kafa, da sauri nai
'kasa da kaina ina addu'ar ALLAH ya kareni, nayi
sallama natsuguna da nufin gaisheta, ta dakatar
da ni cikin tsawa, tace tashi karki daddara ki
gaisheni mara mutunci, wadda har abada bazaki
chanja mugun halinki ba yar ba'kin ciki, (inajin
haka nasan lallai su Fa'iza sun bugowa Mama
waya km ALLAH ne yasan me suka fad'a mata,)
na tsuguna sosai nace Mama don girman ALLAH
kiyi hkr... Munafuka meson jawa mutane abin
kunya harke kin isa ki wulaqanta ni? Wllh baki
isa ba kinaganin yarinyar cikin halin rashin lfy
kika tsallaketa kika taho, idan baki dubi darajar
'yar uwarki ba, kya duba darajar Nuraddeen
amma har kika zauna kinayi masa rashin kunya
sbd yanemi alfarmar kizauna da 'yar uwarki, ni
na nemi alfarmarkizauna da 'yar uwarki, ni na
nemi alfarmar kije kizauna amma kika
wulaqantani sbd ke kin riqa ko? To bake
kad'aice 'ya ba cikakkiyar 'yar uwarta ta tafi ta
maye gurbinki, nasan banida matsala da Fadila
duk tsiya bazata gudu ta barta ba, Kaina yana
'kasa kawai hawaye yake fita daga idona nasan
sharri kala-kala anshiryamin, zuciyata tanata
sa'ka 'karyar da zata zamo kariya gareni, amma
jin maganar Fadila ta tafi yasa nad'ago ina
kallonta cikin mamaki, azuciyata nace lallai
Mama bata da al'kibila tun kafin nazo taji ba'asi
harta tura Fadila! Innalillahi... Mama sbd wane
dalili zaki tura Fadila bayan bakisan dalilin
tahowata ba, ai baki da wani dalili daya wuce
raini da wulaqanci, inajin hk na'kir'kiro tawa
'karyar don nasan ba abinda zai yiwa Mama
tasiri azuciya idan tasa kanta ko kuma tahau
dokin zuciya, nace "Mama ba haka bane wllh ina
cikin matsala ALJANUNE a d'akunan 'kasa suke
tsoratani da siffar maza har suna 'kokarin
kusantata, ga Farouk naji yana maganar asakko
da bikin... Wata muguwar'kara na saki tare da
cillar da jakar da take hannuna lkcn da gigitaccen
marin Mama ya sauka afuskata wanda ya
dakatar dani amaganar da nake, uwar aljanu ba
aljanu ba, wato Farouk ne ya hanaki aikata
umarni na ko? To wllh wllh saidai ki nemi hanya
matuqar baza kibi umarnina ba, Farouk d'in
banza wayeshi? Tuntuni yake cin dunduniyarmu
amma sbd ke mahaukaciyace baki hankalta ba!
Daga yau ni Khadija na haramta Aurenki da shi
naga tsinannan dazai halastashi tsakanin ke da
Tijjanin (yayan Abba), zunbur na mi'ke lkc guda
nakai dubana ga Mama zuciyata ta tsaya cak km
ta 'ke'kashe, nace "Mama me kike nufi? Abinda
kikaji shi nake nufi ko zaki dakeni ne? Mama
yadda kike da hakki akaina hk nima nake da shi
akanki, kllm kokarina nasauke miki naki amma
naki 'kokarin ki tauyemin nawa, kowacce uwa
tana alfahari da 'ya'yanta kamar yadda 'ya'ya
suke alfahari da iyayensu amma banda ke Mama,
Mama kin tsaneni bakya 'kaunata ko kad'an
aranki, wllh zuciyata tafara bani tabbaci akan
niba 'yarki bace, kikaini wajen Mahaifiyata na
[16:19, 10/26/2015] Bana: 24RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (24) Cigaba 24.
Kawai naji hawaye ya cigaba da zubowa daga
idona, na kalli Mama cikin takaici nace "tunda
Mahaifina ya rasu narasa farin cikina da jindadin
rayuwata, a duniya banta6a ganin mutumin da
yasoni kamar mahaifina ba, haka kuma banta6a
ganin wanda ya tsaneni kamar wadda take
ikirarin Mahaifiyata da 'yan uwana ba, ki
'kaunaci girman ALLAH mama ki sanar da ni
Mahaifiyata naje gareta... Fauziyya idan bakimin
shiruba natashi zan iya yi miki lahani
mahaukaciya dabba, ni kike tambaya nafad'a
miki mahaifiyarki? Me yasa uban naki da yake
Masoyinki be chanjo miki mahaifiyaba kafin ya
rasu? Fauziyya kin zama cikakkiyar 'yar kanki
me ya rageki a duniya? A kan Farouk kike jifana
da wad'annan zafafan kalaman ko? Mama babu
Farouk a maganata gsky nake fad'a, kin fifita
kuskure ko ince halaka akan gsky ko daidaito,
don me kullum bani da 'yanchi bana zamowa me
gsky awajen ki? Don me kika fifita dukkan
'ya'yanki da daraja mai yawa akaina, Mama ta
wane dalili zancekina sona... Wani irin mari naji
ta bayana, idan ba kuskure ba ko kuma gamo
nayi ba saukar marin na'karaji afuskata karo na
biyu, cikin tsananin gigita zafi da azaba na juya
don ganin me wnnn aikin, babu wanda nagani sai
FAHAD 'kanina me bin Fa'iza, na kalleshi cikin
tsananin mamaki nace "Fahad ni ka mara? An
mareki 'yar baqin ciki me baqin jini da ba'kar
zuciya, har ke wace da zaki dinga fad'a Mama
tana fad'a... Innalillahi Fahad mari akan fuskata
ni? Tafd'ijan... Kamin dai-dai Fahad Mama ta
fad'a tana jijjiga 'kafa alamar jinjina. Da gudu
nashige d'aki ina kuka tare da surutai marasa
kan gado, ina tambayar kuskurena ga
mahaliccina, me nayi da za'a hukuntani da irin
wnnn rayuwar? Me yasa nazamo daga cikin
rayayyu har nayi tsahon kwanan da kllm nake
fuskantar ba'kin ciki kala-kala... Na sake
rushewa da kuka, wanda lkcn naji kira ya shigo
wayata inaji har yakatse don idan nad'agama
bazan iya maganar arzi'ki ba. Tabbas zuciyata
tadad'e tana rayamin akan nabar gidan nan,
na'ki bata goyonbaya to ba makawa yau zan bar
gidannan km da yaddar ALLAH na tafi har abada,
ko N5 bani da ita hakan yasa nayi tunanin fara
zuwa gidan Aunty Sadiya, ma'kwafciyarmu
abokiyar kirki data zamo tamkar 'yar uwa tagari
agareni, me bani shawara da tausasa zuciyata
akan wasu matsalolina data sani, hakan yasa
bana shakku wajen zuwa wajenta idan ina zubar
da hawaye, nasan tana shareminsu duk yawansu,
cikin azama na d'auraye fuskata naja hijabi na
fice, karki dawomin gida saida MAHAIFIYARKI
dan ubanki... "Mamace take maganar da cikin
zafi," ko kallonta banyi ba nai ficewata....
25RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (25) Cigaba 25.
Aunty Sadiya Mama bata sona bata 'kaunata
bansan me ta d'auki duniya da abin cikin taba, ta
fifita son zuciya akan komai amatsayina na 'ya
mace yakamata ta hango kota zargi gudun
faruwar wani abu nayi, amma Mama ta rufe
idonta tabi son zuciyarta ta danne duk wani
tunani me kyau, ni kaina hawayene yake fita
daga idona azuciyata ina mai addu'ar ALLAH ya
gaggauta kawo mata mafita da kwanciyar
hankali, ta kalleni tana share hawayen fuskarta
datayi suntum don wahala da kuka, Ummie don
ALLAH d'akko min ruwa med'an sanyi nasha,
nace to natashi ina goge hawayen da ya zuba
kan kumatuna, Aunty Sadiya tace Ummie fara
had'o mata tea sbd yunwa itama tana maganar
cikin muryar kuka, nace to, na had'o komai da
abinci na kawo mata. Aunty Sadiya ta kalleta
cikin tsananin tausayawa, tace "Fauziyya kiyi hkr
ki 'kara hkr ki kuma 'karawa babu damuwar
datake dawwamammiya duk dad'inta duk
wahalarta, duk rintsi duk wahala ALLAH yana
tare da ke karki bi zafin zuciya kice kin rabu da
Mama,gangancine Mahaifiyarkice duk irin halin da
take nuna miki.... Aunty Sadiya narantse da
girman ALLAH bazan koma gidan Mama ba,
gwara mutanen duniya sun wulakantani akan
tsananin tsana da 'kiyayyar Mahaifiyata, ko
Mahaifiyar da take faranta ran 'ya'yanta na
tabbata bata samun biyayyar da nake yiwa
Mama, amma bata gani meyasa bazata godemin
kota yabamin ko kuma ta aminta dani amatsayin
'ya kamar sauran ba?... Kuka yaci 'karfinta tayi
shiru tare da ajiye kofin hannunta tana goge
hawaye, Fauziyya karki saurin yanke hukunci
cikin fushi na yarda Mama bata miki adalci
amma zamanki kusa da ita zaki fi samun lada
akan nisantarta, duk 'kiyayyar da take miki
bazata kasheki ba idan ma zata kasheki ai ita ta
haifeki kiyi hkr, tsakanin hkr da akasinsa tazarar
kad'ance, kizauna anan idan kin huce gobe ko
jibi sai ki koma ko kuma kije gidan Abba Tijjani
ki kwana 2 kidawo... Hmmm Aunty Sadiya kenan
nata6a zuwa gidansa karo na farko da yasan
matsalata da Mama yana da zafi shima amma
bakiga cin mutuncin datayi masa ba, har da
cewa ba shi ba zuri'arta har abada, ni bana
neman sulhu gwara na tafi duniyar inda bansan
kowa ba, wataqila nafi jindad'i, wllh ganin Fa'iza
yasa nake yarda da Mama amatsayin
mahaifiyata amma badon wnnn ba da na aminta
da matsayin 'yar ri'ko ahannun muguwar....
Wayarta tai 'kara alamun shigowar sa'ko lkc
guda km kira ya shigo, amsa kawai ta bayar a'a
bana can ina gaban layinmu gidan Aunty Sadiya
ta ajiye wayar, ta bita da kallo tare da ajiyar
zuciya, tace "Farouk ne ALLAH yasa lfy naji
Muryarsa ta tabbatarmin kamar akwai wani
abu...
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive