shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-26 27 28 29

rayuwar-fauziya.jpg

[16:19, 10/26/2015] Bana: 26RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (26) Cigaba 26.
Aunty Sadiya ta kalleta tace "ameen kisauri
kigama cin abincin kafin ya'karaso" tace "karki
damu Aunty Sadiya ruwan shayin ya isheni" ta
mi'ke ta tafi band'aki ta d'auro Alwala. Koda
ya'kara kira bata idar ba na amsa da cewa
Sallah ta ke, ta idar tad'an shafa hoda duk da
babu abinda hodar ta 6oye na daga tsananin
tashin hankali da damuwar da fuskarta take ciki,
na wahalar kuka da tashin hankalin jiya na
Nuraddeen da wanda mama ta d'ora yau, haka ta
tafi tana ya'ken kau da damuwa daga fuskarta.
Har na bud'e motar nayi sallama kansa yana
du'ke kan sitiyari, wannn ya tabbatarmin ba
lafiya ba, oh ni Fauziyya daga wnnn sai wancan
na fad'a azuciyata tare da bugar jikin kujerar
motar alamun ya tashi, fuskarsa ba yabo ba
fallasa ammafa akwai alamun damuwa, ko
'kiftawa baiyiba idonsa 'kyar cikin nawa kamar
me neman wani abu, gabana yafad'i hoton
abinda ya faru jiyane ya bayyana azuciyata cikin
sauri nad'auke idona don karya hango mugun
abin da bana fatan tunashi ballantana
nabayyanashi ga kowa. FAUZIYYA! Zauna mana,
yafad'a yana kallon agogon hannunsa, kawai
ganina nayi azaune batare da na nemi izini daga
zuciyata ba, wasu tambayoyi nakeson yimiki
agurguje inaso ki amsaminsu bisa gsky da
amana, na kalleshi kamar me son tambaya amma
sai nakasa, nace "ALLAH yasa na sani, yace
"Ameen, kindawo gida ne? Na dubeshi cikin
rashin fahimta, sannan nadake nace "eh", Sbd
me ko Fa'izan ta samu sauki? Na'kara bashi
amsa da "taji sauki shiyasa nadawo" yai wani
galabaitaccen murmushi kafin yace "yau kika
dawo kenan?" cikin 'kosawa na d'aga kai alamar
eh, kin tabbata gsky kika fad'amin? Na amsa,
sannan yagyara zama yace "meyakai Fadila
gidan Fa'iza yau? Da gudu najuyo na kalleshi
alamun razana snnn nai 'kasa da kaina, batare
da nace komai ba zuciyata tanata zulumin
abinda zata fad'a, yace Fauziyya ina sauraronki,
nai fuska nace "nima bansani ba", kinyi ta
'karshe karki kuma yimin 'karya duk da nasan ba
halinki bane, najuyo na kalleshi tare da jindad'in
saurin d'auke maganar dayayi, yayi gyaran
murya idonsa akan gilashin gaban motarsa
kamar me nazarin wani abu, yace "Jiya ina
kikabar wayarki inata kira tsahon lkc kafin
ad'aga kuma waya d'agamin waya? Ya salam!
Gabana yayi mummunar fad'uwa lkc guda kuma
na kalleshi muryata tana 'kokarin chanjawa nace
"wane irin tambaya kakemin haka Farouk?
Malama ki amsamin tambayar danai miki kafin ki
tuhumeni ya d'aure fuska, na maida kaina ina
kallon cinyata nace "nabar wayar asama wajen
Fa'iza saida safe take fad'amin ka kira tana
bacci Nuraddeen ya amsa" haka akai? ya juyo
yana kallona, na d'aga kai cikin shagwa6a amma
abad'ini atashin hankali nake, be tankaminba, yai
ajiyar zuciya, ni km ina ta tunanin d'akko wata
hirar da zata maye gurbin wad'annan
sar'kakakkun tambayoyin, ina kika kwana Jiya?
Km ke da wa? Sannan meya samu fuskarki da
yashafi idanuwanki suka chanja launi har suka
kumbura baki da lafiya? Innalillahi....Da badan
gigitar da Nuraddeen yasani ciki jiya ba, da nace
ban ta6a gigita irin ta wnnn lkc ba...
[16:19, 10/26/2015] Bana: 27RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (27) Cigaba 27.
Na juyo na kalleshi tare da gyara baki nace
"Farouk bangane abinda kake nufiba" Fauziyya
banason rainin hankali ki amsamin tambayar
danai miki ya fad'a cikin 'kunar rai" lailai akwai
abinda Farouk yataka tunda yafaramin wnnn
zafi-zafin har yake kokarin gigitani, zuciyata tana
taraddadi akan fad'a masa gsky shin yasan
abinda ya faru ko kuwa so yake yakamani
ahannu, "Ina tabbatar miki da idan maganarnan
ta fito saina wulaqantaki wulaqanci mai muni,
tsakanina da ke zata kasance karki bari kowa
yafuskanci wani abu ballantana adamu da sanin
halin da kike ciki, ban 6ata miki rayuwaba karki
6atamin suna...," kawai na tsinci maganganun
Nuraddeen suna yawo a'kwa'kwalwata,haka na
tsinci kaina cikin 'kokarin 6oye gskyr da Farouk
yake nema, na kalleshi muryata asanyaye nace
"Farouk wani abune ya faru? Ko kuma akace
maka nayi? Shiru nad'an lkc ya gifta tsakaninmu,
kafin yajuyo da kallonsa gareni yace " baki da
amsar bani ko?" 'Gidan Fa'iza na kwana
ad'akinta na qasa ni kad'ai kmkainane yake ciwo
shiyasa, Dakyar na'karasa muryata tafara rawa,
yayi ajiyar zuciya daga bisani yace "kin kyauta
Fauziyya yazaro wayarsa a aljihu yana dannawa,
lkc guda naji yace zaki iya tuna wannan? "
FAUZIYYA wnnn shine 'karshen gudun naki? Ga
wayarkinan anata kira kinbarta afalo, wani marar
mutunci dana tabbatar da koshi waye shi ya
kiraki, km nasan shi yake da hannu abada
gudunmawa wajen rabani da matata.....
Nu..rad..deen ka rufamin asiri don martabar
ALLAH da Annabinsa karka ketamin haddi...
Ruwan kaina gaba d'aya ya'kare tabbas
recording akai na wancen baqin azzalumin, to
waye yad'anamin wnnn mugun tarkon? Gaba
d'aya nakasa d'aga fuska na kalleshi ballantana
na iya kare kaina, Fauziyya ban tunanin duk
tsanani ko wahala zaisa kizamo maci amana ko
salwantacciya awajen Nuraddeen ba, kirasa da
wa zaki tarayyar cin amana sai Nuraddeen, kin
cuci kanki km ALLAH bazai barku ba... Farouk
karka yankemin hukunci akan abinda baka da
hujja wllh! Wllh!! ba abinda ya afku tsakanina
dashi, wllh 'karyayake bemin komai ba Farouk ka
yarda da ni don ALLAH karka 'kyamaceni batare
da daliliba... Kuka yaci 'karfina nayi shiru batare
dana so hakan ba, kukan Munafurci bazai miki
komai ba, mayaudariya ninasan ba abanza kika
dage da tambayata akansa ba, zuciyata kwata-
kwata bata aminta da abinda taji ba ballantana
ta dasa zargi sai ayanzun nan, idan ba abinda
yake tsakaninku mezaisa ki 6oyemin gsky? Duk
aminci da amanar da nabaki Fauziyya, meye baki
sani ahalin Nuraddeen ba, meye abin birgewa
gareku da abinda kuka aikata wllh ban yafe miki
ba Fauziy... Farouk ya isheka na katseshi cikin
tsawa me tafiya da kuka, meya ragemin aduniya?
Wllh na 'kuna bana tsoron wuta katafi don
ALLAH katafi karka yafemin, dama zargina kake
Alhmdllh wllh gwara da hakan tafaru, Farouk
tsakanina da kai bazaka iya shaidata akan
abinda zan aikata ba, kishi da zafin rai zasusa
kamanta amana da amincin dana baka?... Na
adana rayuwata tsahon lkc sbd na tsira da
mutuncina, nasamu damammaki masu alfarma
don salwanta rayuwata amma na'kyamacesu, na
zauna a'kunci da wahala, yau zaka kirani da
mayaudariya salwantacciya Farouk kai da kanka
da bakinka? Farouk baka 'kaunata wllh baka
'kaunata, ko video aka kawo maka ina aikatawa
na d'auka kai me 'karyatawane ashe kana sahun
gaba wajen gaskatawa, na rabu da Mahaifiyyata
alkcn da ta kemin kallon naza6eka akanta, ban
misaba nasa 'kafa na amsa abinda take zargi
wanda na tabbatar azuciyata ba haka nake
nufiba, amma zakazo da zantuka ajuye don ka
'kuduri niyar cimin mutunci, 'karshen magana
kace kafasa Aurena Farouk nima na fasa na
ha'kura, wllh na ha'kura da kai, cikin azama na
kai hannu zan tura 'kofar motar yajawo hijabina
tare da datse 'kofar yadda bazata bud'u ta
wajena ba, ya sassauta murya yace "FAUZIYYA!
Ban yanke hukunciba saida nazo wajenki don jin
gskyr lamari, kika amsamin da bakinki wanda na
tabbatar da cewa ba gsky kika fad'aminba, me
yasa kika 6oyemin gskyr?
28RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (28) Cigaba 28.
Sbd gudun tashin hankali, na juyo na bashi amsa
idona cike da hawaye, Fauzyna banda Mahaifana
aduniya bani da wanda yafiki, banda burin na
kyautatawa kowa sama da ke, bana buqatar farin
cikin kowa sai naki, kece kike d'ebemin kewa
kena mallakawa sirrin zuciyata, ke nake so nake
'kauna nake mafarkin zamowa uwar 'ya'yana,
Fauzy idan ban nuna kishi akankiba akanwa zan
nuna? Ki fahimceni nayi iya kokarin danne
zuciyata akan qin d'ora miki laifi amma kika
bud'emin hanya, ko ma'kiyina naji yana
mu'amala da Nury sainaji badad'i ballantana ke,
kuma nasamu hujjoji masu 'karfi akan hakan,
alkcn dana d'au waya don yi miki babban
albishir me d'auke da tsananin farin ciki, amma
sai ya juye ya koma baqin ciki sbd irin rashin
mutuncin da Nuraddeen yamin da baqaqen
maganganunsa, da suka fara sukar zuciyata kai
tsaye batare dana shirya musu ba yakashe
wayar, hakan yasa nasake kiran wayar anan
yakemin albishir da tarkonsa ya kamo kurciyata,
zaiga 'karshen isa da wulaqancin danake
masa,baqin cikin maganganunsa yasa nakashe
wayar, amma nakasa sukuni ina takaicin ya akai
wayarki taje wajensa, kuma me yake nufi da
tarkonsa yakama kurciyata, na shafe kusan
awanni 2 azaune narasa sukuni ballantana
fahimtar abinda yake shirin faruwa, haka nasake
kiran wayar ina addu'ar ALLAH yasa ke zaki
d'auka, abin takaici da baqin ciki ya d'aga yana
alfahari da cewa sai ya baqantamin rai da ba'a
ta6a yimin irinsa ba km da amincewarki, awnnn
lkcn gabana ya fad'i zuciyata ta fara ayyana
kala-kalan surkullen tashin hankali lkc guda na
kashe wayar, nasake kira tare da danna recording
nad'au alwashin yazamo min hujja don wllh duk
abinda ya sameki saina d'aureshi da duk abinda
yake taqama da shi, yasan muna magana amma
sbd tantirine yabar wayar akunne ina sauraron
abinda kuke lkc guda km ya kashe a inda zan
kasance cikin tsananin tashin hankali da rud'ani,
don bansan abinda ya biyo bayaba, na yarda da
ke Fauzy amma nasan rashin mutuncin
Nuraddeen yafi 'karfin tunaninki, na zubar da
hawaye daahankalina bansan lkcn dana zubar da
irinsa ba, nayi salloli adaren batare da nasan
yawansu ba, nad'aga hannu nayi addu'o'i wanda
har takai ina rasa abin fad'a sbd tsananin gigita,
Fauzy meye laifina donna nuna kishi ko na nuna
baqin cikina akanki, don kinqi bayyanamin gskyr
da nake matuqar buqata, meye laifina don na
amincewa zuciyata ta zargeki da duk laifin da
taso tunda kin nuna ni sakaraine batare da kin
sanar dani komai ba, Fauziyya ko bansan abinda
yafaru ba yadace ki sanar da ni tunda akwai
ingantattun aminci da yarda atsakaninmu, nasan
babu yadda za'ayi ki ku6uta daga hannunsa sai
wani iko na ALLAH, nasan zaiso baqantamin ta
wnnn hanyar ballantana km yazo dai-dai da hali,
Fauziyya dole na zargeki da kowanne abun zargi
tunda kin 6oyemin abinda zai cireni daga zargin,
bayan kinsan yace nakira wayarki kuma ya nuna
miki alamun ya d'aga wayar. Kaina adur'kushe
tun ina kuka har na koma shashsheka, kaina
a'kasa nace "Nuraddeen wllh wllh ba abinda ya
aikata a kaina ka yarda dani... Fauziyya
banasonkidinga rantsuwa a abinda kike da
tabbacin ba gsky bane, nakira wayarki da safe
sau da yawa baki d'aga ba ina cikin wnnn tashin
hankalin, nakira Fadila tace tana gidan Fa'iza ke
km kin koma gida baki da lfy yau, tunda ta fad'i
haka zuciyata tagama aminta da Nury ya cika
burinsa, zuciyata bata samu sukuni ba saida tazo
gareki, ganin yanayinki tun daga cikin idonki
zuwa wasu 6angare na jikinki suka tabbatar kina
cikin tashin hankali musamman fuskarki, sannan
kalamin bakinki suka chanja zuwa furta badaidai
ba karo na farko da kika ta6a yimin 'karya alkcn
danake tsananin buqatar gaskiyarki, FAUZIYYA
bazan gujeki don Nuraddeen ya wulaqanta kiba
na yarda dake km zan zauna dake akowanne
hali, burina na'kwatar miki hakki na kuma nuna
masa iya matsayinsa, amma nasan Nury bazai
ta6a barinki ba FAUZYNA!
[16:19, 10/26/2015] Bana: 30RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (30). Fauzy karki
damu da yaddar ALLAH itama zata amince da
samun farin cikinki, kidena fidda rai da samun
farin ciki ko jindad'i ke dabance ALLAH
yanasonki kuma Mama ma zatasoki da yaddar
ALLAH, "Farouk ka amincewa maganata wllh
zuwa wajen Mama babu abinda zai haddasamin
sai tashin hankali da baqin ciki tare da bankwana
da kai, "Fauzyna kidena zubar da hawaye komai
ya wuce, na amince muje wajen Abban, don
ALLAH kidena tashin hankalinki kllm ina burin
naganki cikin farin ciki, haka muka dinga hira
cikin tarairaya da fahimtar juna. Farin ciki bazai
misaltuba cikin raina, haka nasanar da Aunty
Sadiya duk yadda mukai tayi murna sosai
tadinga bani hkr akan nadaure na koma wajen
Mama, kawai na amince mata da to amma badan
zan aikata ba, da yamma li'kis nai sallama da
Aunty Sadiya na tafi gidan Abba Tijjani cikin
tsananin farin ciki. Na sanar da Abba komai da
ya faru amma ban fad'a masa dalilin barina
gidan Fa'iza ba, kawai nafad'a masa nagaji km
Farouk yanaso yazo mutsaida maganar Aureyayi
farin ciki sosai da maganar Farouk amma yayi
takaici da baqin cikin halin ko inkula da Mama
take nunawa akaina, wanda har takai yau ta wayi
gari tana mai alfahari da salwantarki batare da
tasan inda zaki ba, Fauziyya tabbas bata kyauta
ba amma da kinyi hkr wata rana sai lbr, wllh
itace Mahaifiyarki baki da wata bayan ita, ina da
ikon Aurar da ke kota amince ko bata amince ba
amatsayina na wan Mahaifinki, amma bazanyi
hakan ba dole anemi amincewarta da sa
albarkarta, zanje wajenta bazanyi 'kasa
agwiwaba kuma insha ALLAHU zamu samu
nasara, ke tawace dolene nanema miki farin ciki
amma idan ta Haj. Khadija da sauran yaranne
idan nace nacire hannuna akansu ba wanda ya
isa yace sai na mayar, ki cigaba da addu'a
Fauziyya ALLAH yana tare da ke kuma shizai
dafa miki.......
[16:19, 10/26/2015] Bana: 29RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (29) Cigaba 29.
Farouk wllh!!! Ba'karya nake ba Nuraddeen bemi
komaiba, ALLAH ya kiyayeni daga tuggunsa
yakuma tseratar da ni alkcn da zuciyata
takaraya, ta sadaukar da samun farin ciki da
kwanciyar hankali, ta aminta da hakan amatsayin
d'aya daga cikin jarrabawoyin da ALLAH yatsara
mata, FAROUK ka yarda da ni ALLAH shine
shaidata. "Fauziyya taya zan yarda cewa kintsira
daga hannun Nuraddeen bayan na tabbatar da
cewa ko baku ke6anta daga ke sai shiba idan
yaso aikatawa saiya aikata, ballantana kun
ke6anta a inda yake da damar yin duk abinda
yaso bisa son ransa, Fauziyya ALLAH yana gani
zuciyata bazata aminta da furucin cewa
Nuraddeen bai cika burinsa ba, Fauziyya ta
yaya? Meyasa kikeson yimin wasa da hankali?
Farouk zan iya dafa alqur'ani akan abinda nake
magana, kaika tabbatarmin kana gane mace idan
bata sallah ta abubuwa da dama kadubeni
dakyau kagane hakan, wannan shine dalilin
dayasa Nuraddeen ya qyaleni bisa amincewar
Ubangijina, na kwashe labarin duk yadda mukai
na fad'a masahar yadda mukai da mama cikin
kuka na 'karasa, hakika afad'in duniya bani da
abin tunawa na baqin ciki da tashin hankali
kamar abinda yafaru tsakanina da Nuraddeen da
tsananin tsanar da Mama tayi min, Farouk kaine
farin cikina don ALLAH ka amince da ni, kaine
masoyina na haqiqa wllh bazan ci amanarka ba
Farouk karka gujeni alkcn danake tsananin
buqatar.... Yasa hannu ya rufe bakina zan iya
cewa karona farko da Farouk ya ta6a ta6a wani
sashe na jikina kenan, shima hawayene yake fita
daga idonsa, tsahon lkc idanuwanmu cikin na
junanmu wanda bama hango komai sai tausayi
da soyayyar junanmu, Fauzyna ke abar so ce ga
dukkan wanda ALLAH ya azurta da sonki, wllh na
yarda dake na amince miki, akllm ina tausayin
rayuwarki bansan me kika aikata da Mama yasa
bakya birgeta ba, karki damu ni kaina na amince
daki nisanceta nad'an wani lkc amma ba duka
ba, sbd inaso kisamu nutsuwa da kwanciyar
hankali awnnn lkcn, Fauziyya akwai abinda nake
saran samu a Dubai, idan har komai ya kamallu
can zamu tare, da naso najenagama komai kafin
aure idan nadawo sai muyi aure, amma nafasa
Fauzyna dake zan tafi idan kin amince sati biyu
masu zuwa ad'aura mana aure , muje wajen
Abba Tijjani nasan bazai kasa yi mana abinda
yakamata ba, banda matsala da 'yan uwana da
iyayena Amincewarki kawai nake buqata, Fauzy
da yaddar ALLAH saina maye gurbin iyayenki
musamman mahaifinki, saina faranta miki fiye da
baqin cikin da kikasha arayuwarki, bansan wane
irin farin ciki zan iya nunawa Farouk ba, Farouk
kai masoyine abin soyuwa gareni, na amince da
buqatarka zan zauna dakai duk rintsi duk wahala
har abada bazan gujewa umarninka ba matuqar
be kaucewa dokar mahaliccina ba, kaine Farin
cikina aduniya bani da tamkarka ALLAH ya
amince maka da 'kudurinka na alkhairi, Nagode
Fauzyna amma ina roqonki akan muje wajen
Mama munemi afuwa tare da neman albarka,
Farouk karka yaudari kanka ka yaudari
kalamanka ka rusa farin cikin daka dasa
azuciyata, wllh Mama bazata amince da samun
farin cikina ba, muje ga Abba Tijjani albarkarsa ta
ishemu zama cikin aminci
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive