Wani Labari mai ban tausayi
Wallahi da ina karanta wannan labarin saura kiris
hawaye su zubo mini wasu iyalaine talakawa a
wani kauye cikin pakistan sunada 'Da namiji
Kwaya daya rak sun bashi ilimi na addini dana
zamani ya zama shahararren ENGINEER yananan
sai yasami wata attjira ya aura yananan a kauyen
nasu tare da iyayensa sai nan take matarsa ta
matsa masa tace ta gaji da zaman kauye, sai
suka tattara nasu ya nasu suka koma birni ba da
jimawa ba sai yaga wani talla ana neman
Engineers a JEDDAH A SAUDI ARABIA kenan
yaron kuwa yana da sa'a sosai sai yasamu aikin
nan take ya koma can da aiki shekaru da dama
yana turowa iyayensa kudi.
Gaba gaba dai kwata-kwata ya daina turo kudi
kuma duk shekarar Allah sai yayi Hajj Ana haka
sai ya fara mafarki a cikin baccinsa wani bawan
Allah nace masa HajjINKA BA KARBABBIYA BACE.
sai abin ya dame shi yaje ya tambayi wani
Malami wanda aka yadda dashi mai fassarar
mafarki malamin yace masa yaje yaga iyayensa
nan take ya hau jirgi sai pakistan da isarsa yaje
kauyen nasu duk abubuwa sun canja masa, ba
kamar yadda ya saniba.
sai yaga wani yaro yayi masa kwatancin iyayensa
sai yaro yace lalle akwai wata tsohuwa a gidan
makanniyya wadda mijinta ya rasu bada jimawa
ba (wato mahaifiyarsa harta makance akan zubar
da hawaye kuma babu mai kula da ita).
kusan Allah mai karbar addu'ar iyayemmu ne
( waifa lokacin da yake mafarkin addua'a
mahaifiyar ce Allah ya amsa mata kamar yadda
zaku ji nan gaba).
yana shiga ya ganta a kwance tanata faman
kadaici saboda shi kadai ke gare su balle ace
tanada wasu jikoki kuma gashi babansa ya rasu
sai yaji tana magana can ciki ciki saiya kawo
kunnensa kusa da bakinta domin yaji abinda take
fade.
kusan abinda yaji tana fada duk tsawom
shekarun daya kwashe kamar baisan da suba a
duniya, kusan iyayemmu ba kadan suke
sommuba, abinda yaji tana fada shine ya Allah ka
dawo mini da 'dana gida domin idan na rasu ya
dinga yi mini addu'a ni kuma nayi masa fata na
karshe.
inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
kunji fa ita duk bata tunanin guje masu da yayi
amma sai faman nemar masa gafara takeyi.
Ya Allah ka datar damu mu kyautatawa iyayenmu
allah kasa mu rabu dasu lafiya.
Amin allah kasamufi karfinzuciyanmu
ReplyDeleteAllah sarku
ReplyDeleteAmeeen thumma Ameeen
ReplyDelete