shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday, 22 October 2015

RAYUWAR***FAUZZIYA-3

rayuwar-fauziya.jpg

3RAYUWAR (FAUZIYYA) part (3)
Cigaba 3. Haka nazamo ina tafiya makaranta ni
kad'ai, rashin mutuncin yau daban na gobe
daban awajen fa'iza, Mama ma haka wataran
take hararata tana tsaki idan nace na tafi,
Abbana kawai muke kyakkyawar sallama da shi
sai fahad. Komai yanamin dad'i karatu ya
kankama ina daga cikin d'alibai masu 'kwazo da
haza'ka. Abba yana matu'kar yabamin da
jindad'in yadda nake kokari sosai amakaranta,
nazamo abokiyar shawararshi da tausasa
zuciyarshi. Akwai wani lkc da yakirani daga ni
sai shi yabani wasu takardu 3 na kadarorinsa
kawai yace na adanasu agurina karna sake
nafad'awa kowa zaimin bayaninsu nan gaba,
nace to na ansa na ajiye. Ba'afi kwakkwaran sati
3 ba lkcn saura wata 2 mushiga shekara ta 3 a
JAMI'A, nayi sallama da ABBA lfy yamin addu'a
dftn alkhairi har yake shaidamin yau hutawa zaiyi
agida bazai fita ba kansa yana masa ciwo, nace
to ALLAH ya sawwake sai nadawo. Bazan wuce
cikakkun awa 4 amakaranta ba, naga mssd clls
d'in ABBA da FAHAD kasancewar muna Aji wayar
tana silent banjikiranba, da sauri nakira Abban
har sau 2 amma be d'aga ba gabana ya yanke
yafad'i, hakan yasa naji badad'i, nakira FAHAD
ta'ki shiga, kawai sai nakira mama ringing 1-2 ta
d'aga, muryarta danaji ita tasani atashin hankali
batare da nasan metake cewa ba na katsar da
wayar, tabbas nasan gida ba lfy cikin azama
nahad'a komai na tafi gida. Innalillahi wa'inna
Ilaihirraji'un tun afarkon layinmu nafuskanci wani
yanayi daban mutane sunata cincirindon shiga
gidanmu, to meyake faruwa? Haka na dinga
tambayar kaina kutsawa nake ina kokarin shiga
gida batare da na tantance furucin da mutane
sukeyiminba, mugun ji mugun kalami mugun
zato da mugun gani nayi alkc guda, gawar ABBA
atsakiyar gida naci karo da ita na gigita 'kwarai
da gaske tun kafin na tantance gskyr lamari, da
gudu naji Fa'iza ta rungumoni tana fad'in WAYYO
FAUZIYYA MUNSHIGA UKU ABBA YA RASU! Na
kalleta na kalli gawar alkc guda na 'kwalla 'kara
na sulale 'kasa sumammiya.... MAFARIN KOMAI




www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

  1. Natausayamata tunkafin inkarasa gaba

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive