shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 22 October 2015

RAYUWAR***FAUZZIYA-1

rayuwar-fauziya.jpg

1RAYUWAR (FAUZIYYA) part (1)
"Ya faru dagaske"
WANNAN WACE IRIN RAYUWA CE?. Kasancewar
yau ranar hutuce wato asabar yasa nayi aniyar
yin hutun karshen mako agidan babbar yarmu,
nashirya tsaf cikin d'oki da zumud'in ganinta,
ban 6ata lkc ba nafito nayi sallama da mutanen
gida, tare da yi musu busharar sai ranar litinin da
safe zandawo, kasancewar sun sani tuni kawai
nayi musu yasa suka amsa da ALLAH yakaimu
tare da addu'ar fatan alkhairi, suna masu
jaddada gaisuwarsu gareta da iyalanta. Sallama
d'aya nayi tafito cikin murna da d'okin ganina ita
da yaranta, takama hannuna muka shiga ciki,
bayan gaisuwa da tambayar lafiyar kowa
amutanen gida, muka hau hirar duniya, ban wuce
'kwakkwaran awa 2 da zuwa ba, mukaji ana
buga gate da sauri naje zan bud'e tare da
takaicin waye zai shiga hakkin hirarmu. Waye?
Na tsaya ina tambaya afusace, amma aciki ake
amsawa, na tambaya kusan karo na 3 kwata-
kwata nakasa gane me maganar, amma sautin
muryar mace ne hakan yasa na'karasa na bud'e
kai tsaye, gabanayafad'i alkcn danayi ido 4 dame
'kwankwasa 'kofar ganin yadda yanayinta ya
chanja, mace mai fara'a da son jama'a duk da
matsalolin da suke damunta basa ta6a chanja
halayyarta ta kirki, amma yadda naganta abin
yabani mamaki idonta yayi ja yana ta zubar
hawaye, yanayinta duk abin tausayi... Ummie
Aunty Sadiya tana nan? Ta fad'a tana
shashshekar kuka, nace eh tananan, sannu da
zuwa Aunty Fauziyya jikina asanyaye nafad'a, ta
wuce ciki batare data amsaminba, ni kuma na
datse 'kofar tare da taikaicin har yaushe Aunty
Fauziyya zata samu farin ciki med'orewa
arayuwarta? Wllh banta6a ganin mutumin da
yake cikin rud'un rayuwa irin Aunty Fauziyya ba,
(nazauna a wajen yarmu tsahon lkc shiyasa
nasaba da ma'kwafta da 'kawayenta). Ina shiga
naji Aunty Sadiya tana tambayar Aunty Fauziyya
meya faru kuma? Wani abu suka sake yi miki?
Takasa magana kuka kawai take me matu'kar
ban tausayi, wanda har saida yasa hawaye
yazuba daga idona sbd nima nasan wasu daga
matsalolinta. "Aunty Sadiya nagaji! Wllh nagaji!!!
Na dad'e ina jiranmutuwata ta'ki zuwa, natsani
rayuwar duniyarnan, rabona da farin ciki
namanta, bani da mai farantamin rai, narasa
jindad'in rayuwa, wai wnnn WACE IRIN RAYUWA
CE? Aunty sadiya aduniya inaganin babu wanda
yatsaneni kamar 'yan uwana da mahaifiyata,
bansan daliliba, wllh naje ma'kurar da bazan
koma gidansu ba har' abada! Gwara nashiga
duniya, har ALLAH yad'au rayuwata......
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive