shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-8

rayuwar-fauziya.jpg

8RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (8) Cigaba 8.
Bansan wane hali nakasanceba kawai natsinci
muryar liman yana kiran sallar asuba, natashi na
kalli katifar Fa'iza batanan da alama d'akin
Mama ta kwana, naje nad'auro alwala na idar da
sallah naja addu'o'i masu tsaho ina mai addu'ar
ALLAH yabani ikon jure wannan ba'kin ciki, ya
kuma fitomin da miji nagari nayi Aure kona samu
'yanchin kaina. Haka aka kammala komai na
karatun Fa'iza da taimakon samari da Mama har
ta fara nidai idone nawa. Bata dad'e da Farawa
ba Fadila ta gama secondry, muka dawo ni da ita
muke zaman gida, bana shiga harkarta sosai sbd
tafi Fa'iza rashin mutunci da rashin kunya, idan
Fa'iza tayimin da sau'ki sa'a tace Fadila fa!
Akwai tazarar shekaru tsakaninmu. Cikar kyau da
siffa na budurwa sun bayyana 'karara ga Fadila
ashekarunta da basu wuce 17 ba mukuma muna
24, amma sbd girman jiki saikace takai 22, tana
gara samari son ranta don kowa yasan
kyakkyawace, babu ruwana da ita ko agaban
Mama abinda taga dama takeyi sbd hk ban isa
na tsawatar mata ba idanhaka take za'kulo
maganganu tana ya6a masa har yafara jin
badad'i, idan najita nakanyi mata magana nace
au meye haka Fadila! Auren naku nakud'ine
karkisa yatsorata fa, cikin wasa bana za'kewa
don nasan da goyon bayan Mama, gashi 6urum
tanajin yazo zata rigani fita ko tana wajen
saurayinta indai ta hangoshi sai tazo, ganin
hakan yasa nace masa yarage zuwa kawai
mudinga waya zaifi sau'ki. Takanas Mama
takirani tana yabamin akan Nasir yadena zuwa
gwara da na rabu dashi sbd ba ajina bane,
kamarki ace wnnn zaki aura! Be kamace kiba
'yata, Nace ai Mama muna tare yace ma zai turo
iyayensa... To wllh baki isaba mahaukaciya inda
ke kad'ai zakisha wahalar da sau'ki amma ni
bazan sai da akuya ta dawo tana cimin danga
ba, Mamace take Maganar cikin zafi, Wllh Mama
yana da abinda zai ri'keni yana sona ina sonsa
Mama kidaure naji dad'inki awnnn lkcn... Kuka
ya su6ucemin don nasan wannan 'karamin aikin
Mama ne hana aurennan, Fauziyya kiyi hkr bazan
aura miki Nasir ba wllh, bansan lkcn dana ri'ke
hannunta ina kuka baDon ALLAH kitaimakamin
Mama..., tunda ta dage kawai kiqyaleta Mama
ina ruwan wani, Fadila ce tayi maganar. Ai nasan
shanyeta yayi shiyasa meye abinso awannan
idan ba asiri ba? To wllh yayi abanza idan asiri
ya ciki to ni bazai cini ba, sakarmin hannu
sakarya kawai.... Innalillahi wa'inna Ilaihirraji'un
MAMA karki zamo me tauyemin hakki aduk lkcn
da nazo miki dashi, karkisa zuciyata tazamo me
karaya da samun farin ciki aduniya, Mama idan
nazamo me laifi kifad'amin laifina... Kuka nake
iya 'karfina.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive