shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-13

rayuwar-fauziya.jpg

13RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (13) Cigaba 13.
Naja tsahon lkc ina neman ta hanyar da zan
6ullowa al'amarin, na yanke shawarar kawai
nasamu Fa'iza nashaida mata munanan d'abi'un
mijinta guda 2 LUWADI da ZINA kozata rabu da
shi kai tsaye, amma yarinyarnan 'kememe ta'ki
yarda wai sharrin mutanene. Wllh wnnn ciwon
saida aka yiwa FA'IZA aiki mama tace adawo da
ita gida idan ta warke sai ta koma sbd jikin
bakyan gani km likitan yabada shawarar arabata
da mijinta nad'an wani lkc ta samu lfy, dakyar
da tashin hankali ya yarda da hakan wata'kila
yafara tsarguwa musamman da yaga andage sai
takoma gida, kai tsaye yashirya yakoma Khairo
wai zai siyo wasu kaya da za'a 'karasa sawa
asabon gidansu ya sallami komai da za'a
bu'kata na kud'i ya wuce, kwananta biyar agida
sau'ki yana d'an samuwa, ni kuwa azuciyata ina
neman hanyar da zan samu fuska wajen Mama
muyi maganar Nuraddeen don wllh nad'au
alwashin har gaban su Abba Tijjani matuqar
Mama bata bada goyon baya Fa'iza tarabu da
Nuraddeen ba. Sati guda kenan dadawowar
Fa'iza gida wajen 8:30pm nagama bata
magungunanta na tabbatar baccine zai tafi da ita
har zuwa safe kasancewar akwai na bacci masu
'karfi a cikinsu sai inyi magana da Mama
atsanake. Karfe 9 naje nasamu Mama a nutse
nayi sa'a ita kad'aice a d'aki tana duba wasu
takardu, ALLAH yataimakeni tabani had'in kai
muka zauna nayi mata bayani dalla-dalla ta
fahimta, hakika ran Mama idan dubune ya6aci ta
yarda d'ari bisa d'ari musamman da taga
shaidar lalurar jikin Fa'iza, tace wllh bai isaba ita
Fa'izar mahaukaciyar inace take zaune da shi
ahaka? Ba gyara halinsa zaiyiba gwara araba
auren kawai yafi sauki Dan iska ashe kud'in
nasama na haram ne mugu, nayi mamakin
Mama km naji dad'in fahimtata da tayi na
'kokarin ceto 'yar uwata, karo na farko da Mama
ta ta6a farantamin asanin hankalina km karo na
Farko data ta6a sanyamin albarka ahankalina
kenan, sai dai ba anan gizo yake sa'karba anya
kuwa Fa'iza zata yarda da wnnn 'kuduri namu?
Amma da yake Mama tad'au abin bada wasaba
nasan kota'ki kota so Mama bazata janyeba.
Bayan mun idar da sallar asuba Mama takirani
tace zata fita aiki yau da wuri sbd zasuyi ba'ki a
asibiti karnayi maganarnan da Fa'iza saita dawo
zamu zauna nace to, wajen 'karfe 2 Nuraddeen
ya kira wayata yace nabawa Fa'iza kasancewar
an ajiye tata wayar sbd yawan kira, lkcn ne yayi
dai-dai da dawowar Mama nabata wayar naje
wajen Mama don yi mata sannu da zuwa, abin
mamaki muka tsinci Fa'iza afalon da muke ni da
Mama cikin fara'a da zumud'i, karo na farko data
taka da 'kafarta acikin gidannan amma kana
ganinta kasan mugun 'karfin hali tayi, Fa'iza
lafiyarki kuwa? Ko wani abune ba gwara ki
magana azoba, ballantana yanzu Fauziyya ta
baro wajenki, Mamace take maganar cikin fad'a
irin wanda ake yiwa mara lfy idan yayi kuskure
ga lafiyarsa.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive