shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-14

rayuwar-fauziya.jpg

14RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (14) Cigaba 14.
Mama Nuraddeen yana hanya yace ankammala
sabon gida yana dawowa zamu... Rufamin baki
shashasha har wnnn ne yasaki zumud'in dazaki
yo tattaki kina murna kin manta lalurar da take
damunki? To wllh kinji na rantse ko, bazaki koma
gidan wnnn Dan iskanba sakarya kina zaune da
mutum yana ha'intarki, Mama ce take maganar
cikin zafi batare da tabari Fa'iza ta juye farin
cikin data kwaso ba, haba Mama sbd wane
dalilin za'a rabani da mijina? Meyayi miki wnnn
wace irin maganace? Oho kema an gulmata miki
sharrin da aka 'kaga don rabani da shi ko? To na
rantse da girman ALLAH banga mahalukin daya
isa ya rabani da shi ba, Fauziyya ke butulu ce
baki da amana wnnn ce sakayyar sirrin danace ki
adanamin har ki fassarashi da wata manufar?
Tana magana cikin tsiwa da rashin kunya, ran
Mama yakai ma'kura wajen 6aci, cikin zafin rai
ta fizgo Fa'iza ta wurga ta kan kujera, da gudu
na ri'ke Mama ina bata hkr don nasan komai zai
iya faruwa, rabu dani naci kutumar ubanta har ni
zata zauna tanayiwa hayaniya, na datse igiyar
aurenku har abada duk abinda kika ga dama kiyi
'yar iska mara mutunci, Fa'iza ta fashe da kuka
tana cewa "Mama wllh ba halinsa bane sharrine
don girman ALLAH kiyafemin kijanye 'kudurinki,
Mama ina tare da juna biyunsa be kamata wnnn
maganar ta dinga yawo abakin kiba, juna
biyunsa d'in banza wllh 6arar da shi zanyi bazan
ta6a had'a iri da wnnn tsinannanba, haka suka
dinga hayaniya tafad'a tafad'a nidai narasa
abinyi, furucin Mama da Masifar da take yasa
dole Fa'iza tagaza maida martani tazauna
tanata rera kuka me matu'kar ban tausayi ga duk
mai sauraronta, hakan yasa naga tafara wani
abu kamar wadda zata shid'e da sauri nakamata
nace Mama don ALLAH a ajiye maganarnan
yanzu sbd jikinta bari na maidata d'aki kawai,
tayi tsaki cikin zafin rai tawuce tabarmu afalon,
nakamata mukayi d'aki Nace Fa'iza kiyi hkr
manufata kisamu 'yanchi da jindad'in rayuwa ba
kishiga cikin damuwa ba, don ALLAH ki sassauta
zuciyarki.... Fauziyya na yadda dake amma
kinsan Mama bata da hkr ko kad'an bekamata
taji maganarnanba, babu wanda yakamashi da
laifin da kuke tuhumarsa da shi, wllh yadda
Mama ta rantse nima bazan kaffaraba akan na
rabu da Nuraddeen gwara na rabu da ita! Ta
sake shararo hawayen, na kalleta cikin rauni
nace Fa'iza idan hankali ya tafi hankaline yake
nemoshi, kana chanja miji amma baka chanja
iyaye bekamata kiyi wnnn furucin ba, FAUZIYYA
ta ambaci sunana da 'karfi, kimin shiru kome
yafaru aike kika jawo, Mama ba irin iyayen da
ake lallashi bane batasan darajar 'ya'yantaba
wane irin zalunci ne batai miki ba? Nidai bazata
tauyen hakki inaji ina gani ba, cikin mamaki nake
kallon Fa'iza sbd furucin bakinta sun daki
zuciyata da yawa, lallai Fa'iza ta riqa! indai
NAMIJI ne dai dai da itane, me mutuncima ya
aka 'kare dashi ballantana shed'anin mutum irin
Nuraddeen, haka tagama tunbotsenta nataso
nabarta tanata faman zubar hawaye ad'aki, ban
raba d'ayan biyu ba saita fad'awa Nuraddeen
awaya. 'karfe 9:35 na dare Nuraddeen ya sauka
gidan Mama wnnn ya tabbatarmin Nuraddeen
yasan komai, amma yaddayashigo cikin fara'a da
nishad'i nafara kokwanto dakyar in Fa'iza ta
sanar masa, naje nasanar da Mama Nuraddeen
yazo, ta kalleni cikin takaici tace karki bari
yazauna yabaki takardar Fa'iza ya juya, nace
Mama kar ayi haka kije kugaisa sai kuyi maganar
afahimtar juna, dakyar ta aminta ta fito cikin
tsananin 6acin rai, gsky najuma banganta cikin
irin wnnn 6acin ran ba.Hmmm MUTUM!.........
(Kuyi hakuri kwana biyu kunjini shiru sakamakon
rashin lafiya danayi amman yanzu komai lafia lau
in Allah ya yadda)
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive