shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 10 October 2015

DAN******ALHAJI-22 & 23

dan-alhaji.jpg

[10/3, 5:34 PM] Abba~Gana: DAN ALHAJI 22

muhd-Abba~Gana


maganar ta doki zuciyarsa sosai yace shikenan sankin ganni gobe tace Allah ya kaimu bai masa ba ya kashe wayar hannun yasa ya dafa kumatunsa yana tunanin maganar data gaya masa jikinsa yayi sanyi yace laalle wanan yarinyar wato dole ta guji bacin ran ubanta amma ni akanta na sakawa nawa iyayen bacin ran a kanta na dauke kafana daga gidanmu sai alhaji ya tau tsawon kwana bakwai bai sani a idonsa ba idan abin ya dameshi sai dai ya kirawoni a waya shima dakyar nake amsa maganar sa duk saboda ita zuciyata ta ringa zuga shi kawai ya dauki shawarar abokanansa idan kuma ya tuna da son da yake mata sai yaga hakan bai dace ba gwara ya bari ta zama mallakin sa yayi niyar ya share ta kar ya kuma zuwa gurin ta hakan ta faskara,daukar mota sa yayi ya ratsa ta majalisa anan ma sun yaudare shi ya ki,ya zare jikinsa yace to zan tafi wajen ginbiya yana bala'in basu mamaki da shagala irin ta DAN ALHAJI yanzu yarinya karama ta dauke masa hankalinsa yafi tsohon minti goma bai sami yaron da zai aikaba yana daga idonsa suka hada ido da ita ta fito daga kusa da gidansu da kamal a hanninta yana kuka kayanda tsa sunyi mata kyau shirt da riga nena material ta yafa dan kwali a kanta ganin safuwan taji gaba daya gabanta ya fadi ba karamin dadi tajiba bata bari yagane ba fuskarta ba yabo ba fallasa ya mika hannu ya karbi kamal ya sake barkewa da kuka yamika shi tasa hannu zata karbe shi dan kwalinta ya sullube sakar baki yayi yana kallon gashinta har baya bashi da maraba dana india gashi rigar tayi bala'in fito da suran jiikinta haba ganin hakan yasa shi ya direrece ta lura da hakan tayi sauri ta shige gida har ta dawo sam bai san tana tsaye ba ya shiga duniyar tunani.


muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz
[10/4, 10:22 AM] Abba~Gana DAN ALHAJI 23

Muhd-Abba~Ganasai da ta dan daki murfin motar sannan yayi firgit tace tunananin mai kakeyi haka? yayi murmushi yace tunanin naya wuce naki na ga kin zama mallakina tace kar ka sami damuwa insha Allahu kamar yaune haka sukayi ta hiransu cikin faranta zuciya a hanyarsa ta zuwa gida ba abinda yake illa tunanin surar da Allah ya bata a gaskiya gani yake idan ya sameta yafi kowa sa'a ya buge siteri yace ai ni indai na sami wanan yarinyar ba kuma wata yarinyar da zata bani sa'awa a rayuwata wani tunani ya fado masa sai daya ji bugun zuciya wani tsoro ya bayyana a fuskarsa tunawa yayi anya mallam nasiru zai bashi yarsa idan yayi bincike ya gano halinsa dana mahaifinsa na kin talakawa idan ko ta bincike ne a gaskiya bazan sameta ba a halin irin na mahaifinta mai ra'ayin rikau saboda duk wanda ya kwana ya tashi cikin unguwarsu ba wanda bai san tabargazar da sukayi da shi da abokinsa ga kuma halin da yake ciki shi da alhaji har yanzu yana kan bakarsa ta bai yarda ya aureta ba ko jiya sai daya dada jadda masa akn ya samo ko yar wacece indai ya amsa sunansa na mai kudi yanuna masa indai bai aureta ba zai iya shiga wani halin tatshin hankali yana gama wannan tunanin duk saiya ji ransa ya baci ji yake kamar zuciyarsa zata fashe ta warwatse gaba daya a daddafe ya ringa tukin har yazo gida d kyar yana shiga cikin gidansa firiji ya zarce ya bude ya dauko kwalban barasarsa bai tsaya tsiyayawa ba kwalbar ya daga ya tittila a cikinsa sai da ya tabbatar da ba komai a cikin kwalbar sanan ya jefar ya samu waje ya zauna idonsa ya kada yayi jajawur saboda tsabar bacin rai.

muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive