shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-35(KARSHE)

rayuwar-fauziya.jpg

35RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (35) KARSHEE.
Tunda muka d'auko hanya nke addu'ar samun
nasara akan Mama haka ma Faruk bnda rarashi
da karamin karfin gwiwa ba abinda yke, munyi
kyau sosai shigarmu iri d'aya idan ka ganmu
azahiri zaka iya cewa nishadi muke amma a
badini fargaba ta rinjayi nishadin. Muna shiga
harabar gidan mukaci karo da Amir yana ball da
gudu yazo ya taremu muka karasa ciki, afalo
muka riski Fa'iza da turkeken cikinta da Fadila
tana kwance kan doguwar kujera tana danna
waya, mukayi sallama Fa'iza ta juyo takare
mana kallo tayi tsaki taja jiki tabar falon, Fadila
ce ta amsa sama-sama suka gaisa da Faruk
tana lumshe ido kamar me jin bacci, yace ina
Mama? tace "tana shiryawane zata kai Fa'iza
asibiti, jiya mijinta ya tafi america yasamu wani
aiki acan shima in ya dawo da ita zai tafi, tana
maganar cikin shagwaba, Faruk yai murmushi
yace na masa murna sosai ita km ALLAH yabata
lfy, tace ameen ta tashi tana rangaji ta fice.
Zuciyata ta cika da tsananin fargaba jikina yai
sanyi don nasan babunasara tunda munafukanta
suna kusa. Kutashi ku fitarmin daga gida tun
kafin nadau mataki akanku, Muryar Mama ce
take maganar cikin hayaniya, da gudu muka
tsuguna ni da Farouk muna rige-rigen gaisheta
amma ko ta kanmu batabiba tacigaba da
masifarta, na sallamaki ga wnnn dan iskan da ya
shanyeki kika za6eshi akaina, indai namijine zaki
gane kuskurenki, kin za6i bin Umarnin Tijjani
akan nawa haka nima naza6i rabuwa da ke
har'abada, mu zuba duniyace kuma zakiga
karshenki, Fauziyya na tsaneki ALLAH yatsine wa
rayuwarki nayi nadamar haihuwarki, ina alfahari
da Fa'iza nasan itace 'ya amma ke butuluce
mahaukaciya dabba... Da gudu na'karasa na rufe
bakinta ina kuka, Mama don ALLAH kiyi hakuri
kiyafemin kidena aibatani da munanan kalamai,
Mama lkc yayi da zaki soni ki nunamin 'kauna
kamar yadda kowacce uwa take ga 'ya'yanta...
Fizge hannuna ta yi cikin tsananin tsana ta daga
hannunta ta daddalla min mari a kumatuna biyu,
sakeni danasoki gwara naso dabbar da aka
la'anta gwara na sassautawa ma'kiyyina
bana'kaunarki wllh, silalewa nayi natsuguna na
kama 'kafarta ina kuka nace "Mama ko zaki
kasheni bazan gaji da rokon afuwarki ba, na
tabbata zan kasance mai samun rahama ga
mahaliccina... Mama kiyi hakuri munsan munyi
kuskure don ALLAH kiyafemana, Faruk ne yake
maganar cikin girmamawa da tausayawa, ta
kalleshi awulakance tace "rufamin baki mara
mutunci munafiki har ka isa kasani nayi abinda
banyi niyya ba?" matsiyaci baka da kud'in da
zaka nunamin isa da gadara, ina da surukin daya
fika daraja da mutunci da komai, karka sake
samin baki ina gargad'inka daka fitarmin daga
gida, "Mama don ALLAH kidena 6ata ranki da
lkcinki kizo mutafi, Fa'iza ce ta leko tayi
maganar lokaci guda kuma ta juya. Nidai ina
ri'ke da kafarta ina ta gunjin kuka tasa kafarta ta
shurar da ni har sai da na buga kaina, inaji Faruk
yana Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Mama me
yai zafi haka? Idan baku fitarmin agida ba sai
kaga abinda yafi haka zafi, atake ya ja hannuna
ya wurgani cikin mota ina kuka ina tirjewa,najuyo
muryar Fadila tana cewa "gsky Mama baki
kyauta ba, ba hujja ba dalili," ransa a6ace yaja
motar muka tafi kaina har yafara zubar da jini
ban'karasa jin maganar Fadila ba ballantana
amsar da Mama ta bata muka fita, wnnn itace
rabuwar da mukayi da Mama da 'yan uwana,
Faruk yana tabani hkr lallami da alqawurikan
rikon amana da kulawa, hankalin Abba ya tashi
matu'ka da jin labarin yadda mukai da Mama,
shima yamin nasihu da fad'a akan namanta da
komai ALLAH bazai kamani da laifin komai ba,
km alkairi zai musanyamin da shi. Ranar
bankwana da 'kasata 'yan uwana da dangina,
mukayi sallama da kowa muka wuce cikin kewa
da begen dangi ni kuwa zuciyata kamar ta fashe
don ba'kin ciki da takaici, babu jinin Mama wajen
rakiya ballantana Mama, sai gidan Abba da
Iyayen Farouk da 'yan uwansa. Cikakkiyar wata
biyu da tafiyar Fauziyya ba'ayiba, aka aiko da
cewa ankama Nuraddeen a america dumu-dumu
da laifin sata da kuma cutar da yaro 'karami da
halayyarsa ta Luwadi, banda miliyoyin kudi
da akasa masa na tara harda shekaru masu
yawa, ga matarsa batafi sati uku da haihuwa ba
ta haifi 'yarta mace, da an6oye maganar amma
ahankali ta bayyana har a net. A yanzu kuma
'kishin-'kishinake akan Fadila tana shaye-shaye
kuma tana harkar 'yan mad'igo (neman mata),
sannan tana d'iban yara 'yan mata tana kaiwa
alhazawa, yanzu hk suna rikici akan takai wata
yarinya kuma ciki ya fito iyayenta sunce kotu
zasu kai bazasu yarda ba. Idan kajewa Mama
jaje banda zubar hawaye babu abinda take, ashe
gadon Fauziyyama dasu ta hada tayi bikin
Fa'iza, idan kagansu da halin da suke ciki saika
tausaya musu, Fauziyya kuwa tanacan karatuma
zata fara, 'karshen alawa 'kasa kowa yace
"kadan Mama tagani daga sakayyar ALLAH, da
rabon ita zatazo tana neman Fauziyya donta yafe
mata.......... KARSHE..(labarinnan gaskiyane
amma akwai inda aka kara aka kuma rage, wnnn
darasine ga al'umma, meza kuce? NAGODE muku
da kulawarku, sai yau ALLAH ya nufeni da
kammalawa agurguje)
Share:

10 comments:

 1. TNX duk wanda yakaranta dole yadauki darasin rayuwa

  ReplyDelete
 2. kai gaskiya abun yayi7 April 2016 at 12:00

  kai gaskiya abun yayi dadi

  ReplyDelete
 3. Hmmmm,mugode.akwai darasi babba a labarin

  ReplyDelete
 4. Tnx allah yakara basira

  ReplyDelete
 5. Daman haka abinyake daga wahala sai dadi

  ReplyDelete
 6. Mun gode gaskia akwai darasi aciki sai wanda ya karanta

  ReplyDelete
 7. Kai Allah Ya Karamana Tausayi Da Imani

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive