RAYUWAR***FAUZIYYA-9
9RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (9) Cigaba 9. Tun
daga ranar nahad'u da azababban ciwon kai
"Migrine Headache" idan ya tasomin sai nafi
kwana biyu akwance ina juyi ga 'kirjina yai ta
bugawa da sauri, dole tasa mukaje asibiti likita
yace na rage damuwa nadena sanya abinda zai
dameni cikin zuciya idan ba haka ba zan
haifarwa kaina matsala babba. Haka suka rabani
da Nasir ta 'karfin tsiya don Fadila ma awaya
takira taci masa mutunci kuma tafad'a mishi
Mama tace niba sa'arsa bace sbd hk karya 'kara
zuwa wajena, har wayata Mama ta'kwace da
nufin wai itama tana 'kara sani adamuwa, ALLAH
yasa nayi masa txt na fatan alkhairi da nuna
alhinin rabuwarmu tare da bashi hakuri adukkan
abinda yafaru, bayannan saida nayi samari masu
kud'in da Mama takeso amma d'abi'unsu basa
birgeni 'karshema Fadila ta 'kwacesu da
muguwar yaudararta (ba lkc da kunji tuggun
Fadila akan samarina) don nayi asarar samari
sbd tarbiyar FADILA da yaudararta wanda har ya
haddasa mukazamo abokan gaba. Fa'iza likkafa
ta bud'e ko yaushe da irinmotar da ake fakata
aciki tayi kud'i wayoyi ba'a magana kowacce
sabuwar yayi tana ri'keta duk tsadarta, amma
Mama ko ajikinta, har takai Mama tafara
business da su saita siyo kaya masu tsada ko ta
kar6o daga wajen aiki ta kawowa Fa'iza da
Fadila wai su siya su bata kud'inta bafa kud'i
kad'anba masu yawa wllh, komai na zamani
yana jikin yarannan, idan wataran nace Mama
nima abani bashin sai kiji tace a'a wllh bazan
baki ba haka kawai kibarni da biya in taga dama
ta siyomin 'karamin nasu tabani. Kamar wasa
wata 2 ya rage Fa'iza tagama karatunta taje
bikin 'kawarta suka had'ata da wani saurayi ta
waya mai bala'in kud'i alokacinma baya 'kasar,
babu irin malamai dabasubiba ita da mama
wajen jawo hankalinsa akan ya aureta ba'a
maganar kashe kud'i, a6oye aka gama komai sbd
samarinta don wllh duk wanda yaji zai iya
d'aukar mummunar mataki akanta, adaddafe
tagama exam, mijin bayanan akasa rana akayi
komai bata sanshiba baisanta ba azahiri saidai
sun tura hotunan juna ta waya, dakyar yazo
saura kwana 3aure don da cewa yayi kawai
ad'aura zaizo, saida 'yan uwan Abba suka dage
akan cewa basu yarda ba sai sunganshi sannan
yazo, yagama yiwa Fa'iza komai don duk wani
kud'i data nema baya wasa wajen turo mata,
ankashe kud'i iya kashewa abikin, nayi mamakin
inda Mama tasamu Miliyoyin kud'in bikin Fa'iza,
biki tun ranar laraba aka fara ba ranar da aka
yini agida waje suka kama hotel mijin yakama
musu 2 Mama takama 3 masu tsada da tsari, tun
daga gadajen da akayi mata har zuwa kitchen
zakayi mamakin alatunsu, amma gidan haya
zasu fara zama sbd gini yake maginan gidan da
kayan gidan daga Dubai yad'aukosu, saurayine
shekarunsa 44 ammafa mummunane...
Mungode,sosai
ReplyDeletemasha Allah yayi kyau sosai
ReplyDeleteXatachi ubanta nangaba
ReplyDelete